Wasiyyar Mu’awiyah ga Yarimansa
A lokacin da sayyidina Mu’awiyah
(R.A) ya lura da kusantowar ajali
sai ya yi wasici ga wanda ya nada
a matsayin magajinsa inda ya
gaya masa maganganu masu
tsadar gaske inda Allah ya sa
Yazidu ya kiyaye su.
A cikin wasicin nasa ne yake cewa,
ka sani duk abinda na yi a duniya
babu wanda ya kai hatsarin nada
ka da nayi. Amma na yi ne ina mai
kyautata maka zato. Idan ka
kyautata zamu tsira ni da kai, in
kuwa ka bi son zuciya to, lalle ne fa
zamu sha wuya. Sannan ya yi
masa wasici da kula da hakken
marasa karfi da dai al’amura da
dama da zaku iya komawa gare su
a littafinmu na Kaddara Ta Riga
Fata.
Game da wasicin da ya yi masa a
kan sayyidina Husaini mun kawo
maku shi a cikin wancan littafi daga
littafan Sunnah amma shekaru
goma bayan wallafa shi sai ga shi
na yi tuntube da wata magana
wacce ta yi daidai da waccan a
littafin nan na Shi’a mai dinbin
daraja a wurinsu. Don haka nake
so in kawo ta a nan. Ga abinda
Majlisi mai littafin ya ce:
” ﻭﻭﺻﻰ ﻣﻌﺎﻭﻳﺔ ﺍﺑﻨﻪ ﻳﺰﻳﺪ ﻓﻘﺎﻝ ﻟﻪ -: ﻭﺃﻣﺎ ﺍﻟﺤﺴﻴﻦ
ﻓﻘﺪ ﻋﺮﻓﺖ ﺣﻈﻪ ﻣﻦ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ، ﻭﻫﻮ ﻣﻦ ﻟﺤﻢ
ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺩﻣﻪ، ﻭﻗﺪ ﻋﻠﻤﺖ ﻻ ﻣﺤﺎﻟﺔ ﺃﻥ ﺃﻫﻞ
ﺍﻟﻌﺮﺍﻕ ﺳﻴﺨﺮﺟﻮﻧﻪ ﺇﻟﻴﻬﻢ ﺛﻢ ﻳﺨﺬﻟﻮﻧﻪ ﻭﻳﻀﻴﻌﻮﻧﻪ،
ﻓﺈﻥ ﻇﻔﺮﺕ ﺑﻪ ﻓﺎﻋﺮﻑ ﺣﻘﻪ ﻭﻣﻨﺰﻟﺘﻪ ﻣﻦ ﺭﺳﻮﻝ
ﺍﻟﻠﻪ، ﻭﻻ ﺗﺆﺍﺧﺬﻩ ﺑﻔﻌﻠﻪ، ﻭﻣﻊ ﺫﻟﻚ ﻓﺈﻥ ﻟﻨﺎ ﺑﻪ ﺧﻠﻄﺔ
ﻭﺭﺣﻤﺎ ﻭﺇﻳﺎﻙ ﺃﻥ ﺗﻨﺎﻟﻪ ﺑﺴﻮﺀ ﺃﻭ ﻳﺮﻯ ﻣﻨﻚ
ﻣﻜﺮﻭﻫﺎ”
Majlisi ya ce: Mu’awiyah ya yi ma
dansa Yazidu wasici yana mai
cewa: “Shi dai Husaini ka san
matsayinsa a wurin manzon Allah
(S) (yana nufin kaunar da manzon
Allah yake masa) kuma jininsa ne
da tsokarsa. Ina kyautata zaton
mutanen Iraqi za su fito da shi (da
sunan tawaye) sannan su fita
batunsa, su tozarta shi. To, idan
haka ta faru kuma ka kama shi ka
kula da hakkinsa da matsayinsa na
wajen manzon Allah (S), kada ka
kama shi da laifin da ya yi. Tare da
haka kuma muna da kyakkyawar
hulda da shi, ga kuma zumunta.
Don haka, kada ka shafe shi da
wani mugun abu ko ya ga wani
abinda ba ya so a wurin ka”. Duba
Bihar Al-Anwar na Majlisi (44/311)
To, ka gani fa. Wannan littafi na
daya daga cikin manya manyan
kundayen ilimi da tarihi wadanda
Shi’awa ke bugun gaba da su. Ga
shi ya tabbatar da wannan wasici
mai nuna cewa, babu wata gaba a
tsakanin su irin yadda su yan
shi’ah suke nunawa. Haka kuma
ba shi nufin kome sai alheri gare
su.
Maganar zumunta da Mu’awiyah
ya yi a tsakanin su kuwa yana da
kyau wanda bai sani ba ya sani
cewa, Banu Umayya dangin
manzon Allah ne Sallallahu Alaihi
Wa Alihi Wasallam. Domin shi
Umayyatu kakan nasu dan
Abdushams ne dan Abdumanaf.
Abdumanaf kuwa shi ne kakan
manzon Allah (S) na uku. Da
Hashim kakan manzon Allah (S) da
Abdushams mahaifin Umayyah
uwarsu daya ubansu daya. Don
haka ba mai raba Banu Hashim da
Banu Umayya sai jahili ko kuma
mai mugunyar manufa ga dangin
manzon Allah makusanta. Kuma
‘ya’yan manzon Allah (S) guda uku
mata (Zainab da Rukayya da
Ummu Kulthum) duk a cikin Banu
Umayya suka yi aure. Kuma shi ne
da kansa ya aurar da su. Fatima ce
kawai ta auri dan uwanta Ali daga
gidan Banu Hashim. A cikin
gwamnatin manzon Allah (S) kuma
babu wani gida da yake da kason
da ya kai na Banu Umayya a cikin
ma’aikata; gwamnoni da sauransu.
Don haka, duk wanda yake jin
yana kiyayya da gidan saboda
yana ganin laifin wasu a cikin su to,
ya canja matsayinsa. Zamu koma
kan nadin Yarima bayan mutuwar
babansa.
Ku dakace mu.
Leave a Reply