Me ya biyo bayan kashe Husaini?
Bayan da mutanen Kufa suka ga
abinda ya faru a ranar Ashura sai
suka hakikance sun ci amanar
sayyidina Husaini tun da su suka
gayyato shi amma kuma suka
tozarta shi. Sun fito da shi daga
amintaccen gari kuma sun yi biris
da zuwansa har mai aukuwa ta
auku. To, sannan ne fa suka fara
tunanin yadda zasu kankare ma
kansu wannan laifi. A nan ne wata
kungiya ta bayyana mai suna
“Jaishut Tawwabin” rundunar
masu tuba. Babbar manufar
wannan kungiya tasu ita ce yin
gangami don fada da gwamnatin
Banu Umayyah da ta zama
gwamnatin ‘yan ta’adda wadda ba
ta kiyaye alfarmar jinin gidan
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa
Alihi Wasallam ba. Manufa ta biyu
ita ce daukar fansar jinin ‘ya’yan
gidan Manzon Allah da aka kashe.
To, sai dai wannan fargar jaji da
‘yan Shi’ah suka yi ba ta yi wani
tasiri na azo a gani ba. A
maimakon haka sai ta ida dagula
lamurra, ta kara auka al’ummar
musulmi cikin rikici. Ko kuma
daman dai tuban muzuru ne,
amma wata ajenda suke da ita ta
kara dagula al’amurran musulmi da
raba kansu? Sanin gaibu sai Allah.
Duk abinda ‘ya’yan wannan
kungiya ta ‘yan tuba suka yi bai
wuce kamfe ne da furofaganda ba
ta batunci ga gwamnatin Yazid da
kokarin wanke hannun ‘yan Shi’ah
daga wannan ta’asa.
A cikin wannan kungiyar ne aka
samu wani dan ta’adda mai suna
Mukhtar bin Abi Ubaid Ath Thaqafi
wanda ya lashi takobin sai ya ga
bayan duk masu hannu ga kisan
Husaini. A cikin haka kuwa ya
halaka mutane masu dinbin yawa
wadanda ba su ji ba, ba su gani
ba, tare da cewa kuma lalle ya
kashe da dama daga cikin
mutanen waccan la’anannar
runduna ta Bin Ziyad wacce ta
kashe Husaini. Daga karshe dai
Mukhtar ya yi da’awar cewa, yana
haduwa da mala’ika Jibrilu a
kullum don tattauna matakan da
yake dauka a cikin wannan jan aiki
da ya dora ma kansa. Da haka sai
ya zama kamar yana da’awar
annabta kenan.
Daga cikin babban tasirin da
kungiyar Tawwabuna ta yi ta shigar
da mutanen Makka da Madina
cikin wannan rikici. Ina nufin
yunkurin juya gwamnati mai ci ta
Yazidu. Kodayake ba lalle ne a
dora masu dukan alhakin abinda
ya faru ba. Zai yiwu a samu wasu
karin dalilai da suka dada hasa
waccan wuta a birane masu tsarki.
Zamu yi maganar yadda mutanen
wadannan birane masu albarka
suka fada cikin wannan rikici da
mugun aikin da Yazidu ya aikata a
kan su, abinda ya kara dada ma
gwamnatinsa bakin jini da tsana a
tsakanin al’ummar musulmi kuma
Allah bai yi ma sa jinkiri a bayan
hakan ba..
Leave a Reply