GABATARWA:
Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai
Jinkai
Da yawa daga cikin mutane suna
tsammanin malaman Sunnah da
suka ce a kame baki daga kutsawa
a cikin rikittan da suka faru a
tsakanin iyayenmu musulmin farko
sun fadi haka ne don suna son a
boye gaskiya. Wannan kuwa
kuskure ne babba.
Tarihin magabata, musamman ma
dai almajiran Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wa Alihi
Wasallam na da banbanci da
sauran tarihin mutane baki daya.
Dalili kuwa shi ne, ba zaka iya raba
tarihinsu ba da na maigidansu
wanda shi ne Allah ya dora ma
alhakin tarbiyyar su da shiryar da
su zuwa ga gaskiya.
Dalili na biyu kuma shine
kasancewar su mutanen da Allah
ya zaba kuma ya fifita su
albarkacin zamowar su tare da
amintaccen Allah; masu ba shi
shawara, masu taimakon sa, masu
bin sa sallah, masu ba shi zakka,
masu tanyon sa jihadi, masu ba shi
aure, masu makwautaka da shi,
kuma wadanda tarihi ya tabbatar
sun fifita shi a kan kowa da kowa.
Kai, har ma sun kashe Iyayensu da
danginsu a wajen kariyar sa. Haka
ma duk abinda suka mallaka na
duniya sun sadaukar da shi domin
wannan farin masoyi da basu taba
hada kowa da shi ba.
Wannan magana ba na ji-na ji ba
ce, maganar Allah ce. Mutum har
ya kan yi mamakin irin yadda
wannan lamari zai shige ma wasu
duhu alhalin ga shi nan baro baro
a wurare cikin Alkurani da ba su
kirguwa.
Sahabbai mutane ne kamar kowa
ta fuskar cewa suna iya yin
kuskure ko laifi amma banbancinsu
da sauran mutane shi ne suna da
tsarkin zuciya da shedar Alkur’ani.
Ba ni zaton wannan magana ta
bukaci a kafa mata hujja, sai fa ga
wanda ba shi da wata masaniya
sam sam game da Alkurani. Don
haka idan sun yi kuskure to, sun
samu yafewar Allah da tabbacin su
yardaddu ne, ‘yan aljanna. (Duba
alal misali: Suratul Hashri: 8-10 da
Suratul Fathi: 18 da Suratul
Mujadala: 22 da Suratut Taubah:
100).
Wannan shine dalilin da ya sa
malaman Sunnah suka fifita kame
baki daga fadin abinda ya gudana
a tsakanin sahabbai domin bakin
rijiya ba wurin wasar makaho ne
ba. Wanda kuwa duk ya shagaltu
da neman kurakuransu da
ayubbansu zai wayi gari yana raina
su ko ya kyamace su alhalin Allah
ya umurce shi da darajanta su da
kaunar su da yi masu Addua. Ka
ga a nan shi ne ya fada ruwa.
Daga cikin abinda ke nuna mana
cewa, ba wai nufin malamai shine
a boye gaskiya ba, zamu ga ai duk
tarihin nan da suka ce mu kame
baki daga ce-ce-kuce a kansa su
suka rubuta shi, ba su boye kome
daga cikinsa ba, sawa’un mai dadi
da maras dadi, na gaskiya da na
karya. Sun hikaito mana ko wanne
a matsayin ruwaya da aka fada
kuma sun kawo wanda ya fade ta.
Dalili na uku da ya sanya malaman
Sunnah daukar wannan matsayi
shine la’akari da suka yi da yadda
tarihi ya gauraya da ra’ayoyi da
son zuciya na daidaiku da na
kungiyoyi wadanda ba su jin ciwon
fesa karya don cimma wata
manufa, ko aibanta wani ko
gwarzanta shi. Ga kuma tarihi bai
samu irin hidimar da Hadisin
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa
Alihi Wasallam ya samu ba na
cikakkiyar kulawa da tantancewa
tare da banbanta ingantacce daga
wanda ba shi ba.
Bugu da kari kuma sai marubuta iri
iri suka bayyana kowa da irin
fassarar da yake ma abinda ya
auku. A dalilin haka, sai aka yi ta yi
ma wasu riwayoyi gyaran fuska,
wasu aka sauya su, aka karkata
alhairan wasu suka koma sharri,
wasu kuma aka kara masu matsayi
suka kai inda ba su cancanta ba.
Daga nan zamu fahimta cewa,
kame bakin da aka ce ayi don
maslaharmu ne kada mu fada
karangiya, mu janyo ma kanmu
hisabi a kan abinda tun asali bai
shafe mu ba. Daman dai
madaukakin sarki bai ajiye tarihin
wasu abin hisabi ga wasu ba don
ya ce:
(( ﻭﻻ ﺗﻜﺴﺐ ﻛﻞ ﻧﻔﺲ ﺍﻻ ﻋﻠﻴﻬﺎ ﻭﻻ ﺗﺰﺭ ﻭﺍﺯﺭﺓ
ﻭﺯﺭ ﺍﺧﺮﻯ ﺛﻢ ﺍﻟﻰ ﺭﺑﻜﻢ ﻣﺮﺟﻌﻜﻢ ﻓﻴﻨﺒﺆﻛﻢ ﺑﻤﺎ
ﻛﻨﺘﻢ ﻓﻴﻪ ﺗﺨﺘﻠﻔﻮﻥ(( ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻻﻧﻌﺎﻡ: ١٦٤
Kuma ya ce:
(( ﻣﻦ ﺍﻫﺘﺪﻯ ﻓﺈﻧﻤﺎ ﻳﻬﺘﺪﻱ ﻟﻨﻔﺴﻪ، ﻭﻣﻦ ﺿﻞ ﻓﺈﻧﻤﺎ
ﻳﻀﻞ ﻋﻠﻴﻬﺎ، ﻭﻻ ﺗﺰﺭ ﻭﺍﺯﺭﺓ ﻭﺯﺭ ﺍﺧﺮﻯ، ﻭﻣﺎ ﻛﻨﺎ
ﻣﻌﺬﺑﻴﻦ ﺣﺘﻰ ﻧﺒﻌﺚ ﺭﺳﻮﻻ(( ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻹﺳﺮﺍﺀ: ١٥
Shi ne kuma buwayayyen sarki
harwayau yake cewa:
(( ﺗﻠﻚ ﺃﻣﺔ ﻗﺪ ﺧﻠﺖ ﻟﻬﺎ ﻣﺎ ﻛﺴﺒﺖ ﻭﻟﻜﻢ ﻣﺎ ﻛﺴﺒﺘﻢ
ﻭﻻ ﺗﺴﺎﻟﻮﻥ ﻋﻤﺎ ﻛﺎﻧﻮﺍ ﻳﻌﻤﻠﻮﻥ(( ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﺒﻘﺮﺓ :
١٣٤، ١٤١
Tarihin na bayan sahabbai bai
banbanta da wannan ba. Domin
koda basu da wata sheda daga
Alkurani ta zama ‘yan aljanna
amma suna cikin wadanda
fiyayyen talikai ya ce su ne
“Fiyayyun Tsara”. (SAHIH AL
BUKHARI, Hadisi na 3650 da
SAHIH MUSLIM 6632). Kuma
gabacinsu a addini ya cancantar
da su mu roka masu abinda Allah
ya ce mu rinka yin addu’a da shi ga
magabata:
(( ﻭﺍﻟﺬﻳﻦ ﺟﺎﺅﻭﺍ ﻣﻦ ﺑﻌﺪﻫﻢ ﻳﻘﻮﻟﻮﻥ ﺭﺑﻨﺎ ﺍﻏﻔﺮ ﻟﻨﺎ
ﻭﻻﺧﻮﺍﻧﻨﺎ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺳﺒﻘﻮﻧﺎ ﺑﺎﻹﻳﻤﺎﻥ، ﻭﻻ ﺗﺠﻌﻞ ﻓﻲ
ﻗﻠﻮﺑﻨﺎ ﻏﻼ ﻟﻠﺬﻳﻦ ﺍﻣﻨﻮﺍ ﺭﺑﻨﺎ ﺍﻧﻚ ﺭﺅﻭﻑ ﺭﺣﻴﻢ((
ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﺤﺸﺮ: ١٠
Wannan ita ce fahimtar malaman
Sunnah na farko wadda Shehin
malami Ibnu Abi Zaid Alqairawani
ya fada a cikin RISALA, da kuma
Ibnu Abil Izz Al Hanafi a cikin
SHARHUL AQIDATIT
TAHAWIYYAH, da Al Imam Al
Barbahari a cikin SHARHU
USULIS SUNNAH da dai sauran
su.
Ko a yau, da ace kowa zai kama
bakinsa da ya fi alheri. Mu ma da
sai mu ja bakunanmu mu lizimci
kawaici. Amma tunda yake har
wasu na kutsa kansu a cikin
wannan sha’ani, su rinka tsinto
labari kowane iri ba tare da sun
san mafitarsa ko mashigarsa ba,
sa’annan su koma da zagi da cin
zarafi, wani lokaci har da dibar
albarka ga musulmi magabata to,
ya zama wajibi duk mai abin fada
bisa ga hujja ya fito ya fada don
bada kariya ba ga magabata ba,
don su tuni suna cikin ganin
sakamakon aikinsu. A’a, don dai
kare wadanda aukawarsu cikin
wannan lamari na iya janyo masu
rubushi da gamuwa da fushin Allah
da fuskantar hisabi mai tsanani.
Abinda ya rage mu fadi a nan
shine, tarihin musulunci a cike
yake fafil da abubuwan Jin dadi da
murna da alfahari. Alhairan da ke
cikinsa sau da yawa sun ninka
sharrinsa. Tarihi ne da wata
al’umma – ba mu ba – ba zata iya
kawowa ba. Don haka, mayar da
hankali kawai ga wuraren da aka yi
kurakurai ko shaidan ya ci galaba
ba yin adalci ne ga tarihin wannan
al’umma ba. A duk tsawon shekaru
30 na halifancin Rashiduna guda
hudu yakin basasa biyu ne kacal
aka yi. Alhalin an yi jihadi da cin
birane da isar da sakon musulunci
sau dubunnai da dama. A tsawon
shekaru 100 na daular Banu
Umayya wurare kadan ne musulmi
suka daba ma kansu wuka, a yayin
da sun isar da sakon Allah zuwa
ga kusan duk duniyar da take raye
a wancan lokaci. To, ina adalci in
muka rufe alheri, muka tona sharri
shi kadai?!
Rikicin Karbala na daya daga cikin
matsalolin da suke da muni a cikin
tarihin musulunci na farko. Mafiya
yawa daga cikin rubuce rubucen
da aka yi basu bi ka’idoji na rubuta
tarihin musulunci ba. A cikin
wannan rubutu zamu kwatanta yin
adalci wajen bitar abinda aka
rubuta a kan sa. Zamu kuma yi
bayanin mummunan tasirin da ya
bari a cikin al’ummar musulmi,
sannan mu bada shawarwarin da
zasu taimaka mana don mu cira
daga wuri daya mu karasa gaba.
Leave a Reply