Allah maɗaukakin sarki shine yake bada lafiya, sannan shine yake sauƙar da cuta, Amma duk wata cuta da Allah ya sauƙar to yana sauƙar mata da magani. Wanda Allah ya bashi ilimin sanin maganin ya sani wanda Allah bai bashi ba kuma ba zai sani ba.
Wasu daga cikin mutane idan rashin lafiya ta same su sukan kasa haƙuri suje wurin wanda yake da ilimin likitanci ya duba su ya basu magani wacce ta dace da yanayin jikinsu da kuma rashin lafiyarsu, sai suyi gaggawa wurin zuwa wurin wanda bashi da cikakken ilimi kan harkar likitanci ko kuma mai maganin gargajiya wanda daga bisani wani a ta dalilin haka akan rasa rai.
Baya halatta Musulmi ya aikata haka. Domin baya halatta mutum ya jefa kansa zuwa ga Halaka kamar yadda Allah yayi umarni yace
Kada ku jefa kanku zuwa ga Halala
Baqara: 195
Hakanan wasu sukan yawaita shan magunguna na gargajiya ba tare da ƙa’ida ba, ko na Bature shima ba tare da ƙaida ba. Wanda dukkan wa’innan magunguna suna da illoli irin tasu. Bincike ya nuna yawaitar kamuwa da cutar ƙoda da mutane suke fama dashi yana da alaƙa da shaye shayen magunguna na gargajiya da na bature ba tare da ƙa’ida ba.
Kaman irin magunguna kashe gajiya kaman su profen da makamantansu. Wasu sun mayar da irin wa’innan magunguna kamar abinci kullum sai sun sha wanda wannan ba ƙaramin illa yake yi wa jikin ɗan Adam ba.
Haka nan kuma wasu zaka samesu kowani lokaci acikin shan maganin gargajiya suke, ko dun neman ƙarin ƙarfin maza, ko ƙarin ƙarfin jiki da sauransu. Shima wannan yana da illa sosai.
Abinda ya ja min hankali nayi wannan rubutu shine jiya wani mai siyar da maganin gargajiya ne wanda muke da alaƙa dashi muka haɗu sai ya ɗauko wani magani ya bani yace gashi naje na gwada. Maganin ba na gargajiya bane ana siyar dashi a chemist. Na karɓa na tafi dashi na koma gida nayi bincike kan maganin sai naga ai magani ne da wa’inda suke da lalurar “Erectile Dysfunction” suke amfani dashi. Ma’ana masu lalular tashiwar gaba, wanda gabansu baya tashi. Sune ake basu wannan magani, kuma ba’a basu sai tare da kulawar likita, sannan ba’a shan shi laida biyu a rana. Sannan yana da wasu illoli wanda su wanda suka ƙirƙiri maganin sukayi bayani har sukayi nuni da cewa likitar da zai bada wannan maganin sai ya lura da yanayin wanda za’a bashi ya tabbatar haɗarin da ke tattare da bashi wannan maganin bai kai haɗarin da rashin bashi zai janyo ba.
To amma abin mamaki shine shi wannan mutumi yana siyar wa mutane wannnan magani ne ba tare da bayani ba. Kuma wasu daga cikin masu siyan maganin basu kusantar iyalansu sai sun sha wannan maganin wanda anyi maganin ne don masu lalura, amma wanda bashi da wannan lalurar zai rinƙa sha duk lokacin da zai kusanci iyalin shi. Wanda wannan magani ƙarshen ta zai jawo masa illar da bazai rabu dashi ba har ƙarshen rayuwar sa.
Wannan babbar kuskure ne. Musani cewa Kiyaye lafiyar mu wajibi ne na Shari’a a kanmu.
Mu kiyayi shan magunguna babu ƙa’ida domin hatsarinsa yana da girma sosai.
Allah ya tsare mu ya kuma ƙara mana lafiya.
Leave a Reply