MU 'YAN KUNGIYAR JAMA'ATU IZALATIL BID'AH WA IQAMATIS SUNNAH SAI MU YI MURNA MU YI FARIN CIKI MU GODE ALLAH(Dr Ibrahim Jalo Jalingo)

Danna nan domin shiga karatu Online

MU ‘YAN KUNGIYAR JAMA’ATU
IZALATIL BID’AH WA IQAMATIS
SUNNAH SAI MU YI MURNA MU
YI FARIN CIKI MU GODE ALLAH:
11/3/1434. H 23/1/2013 M
Lalle mu ‘Yan Kungiyar IZALA sai
mu yi murna mu yi farin ciki saboda
yadda Allah Madaukakin Sarki ya
yi wa shugabanninmu mutum
goma sha hudun nan da suka
rubuta wa Kungiyar Jama’atu
Izalatil Bidi’ah wa Iqamatis Sunnah
Constitution dinta watau:-
M. Isma’ila Idris. M. Hudu Chikaji
Zaria. M. Sidi Attahir Sokoto. M.
Alhasan Sa’id Adam Jos. M. Sa’idu
Hasan Jingir. M. Rabi’u Daura. M.
Yakubu Musa Hasan Katsina. A.
Ahmadu Gyallesu. A. Yaro Bichi. A.
Bashir Makama. A. Ali Ibrahim
Hikima. A. Bala Jaban. A.
Mamman Malunfashi. A. Isa Waziri.
Sai mu gode wa Allah Madaukakin
Sarki da Ya yi wa wadannan
mutum 14 muwafaka da taufiiqi a
lokacin da suka rubuta Constitution
din kungiyar Izala, ta yadda suka
rubuta shi bisa tsarin da ya dace,
watau suka rubuta shi a bisa tsarin
da bai saba wa Shari’ar Musulunci
ba. Ta yadda dukkan wani wanda
ke son ya maida kungiyar wata
kungiyar ‘yan bidi’ah mai take
ka’idodin Shari’ah ba zai samu
damar yin hakan ba matukar dai
zai jingina wannan aikin nasa ne
da Constitution dinta watau tsarin
mulkin tafiyar da lamuranta, bai isa
ya fada cikin wata bidi’ah ko wata
karkata ba sai in ya bar yin aiki da
wannan Constitution din nata ya
koma can yana hauragiyasa kamar
yadda sauran ‘yan bidi’ah da masu
bautar son zuciya ke yi cikin ko
wane zamani kuma a ko wane guri.
Lalle wannan abin farin ciki ne
matuka wanda zai wajabta wa ‘yan
wannan kungiya su gode wa Allah
Madaukakin Sarki a kan shi.
************************************************************************************
Idan kana son fahimtar gaskiyar
wannan magana tawa sai ka lura
da wasu abubuwa kamar haka:-
Na farko: An rubuta a bangon
Constitution din Kungiyar Izala
kamar haka:-
{ ﻻ ﻃﺎﻋﺔ ﻟﻤﻦ ﻟﻢ ﻳﻄﻊ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﺰ ﻭﺟﻞ. ﺣﺪﻳﺚ
ﺷﺮﻳﻒ.{
ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻻﻣﺎﻡ ﺍﺣﻤﺪ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺴﻨﺪ ١٣٢٤٨، ﻭﺃﺑﻮ ﻳﻌﻠﻰ
ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺴﻨﺪ ٤٠٤٦، ﻭﺍﻟﺸﺎﺷﻲ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺴﻨﺪ١٢٦٥،
ﻭﺍﻟﻀﻴﺎﺀ ﺍﻟﻤﻘﺪﺳﻲ ﻓﻲ ﺍﻷﺣﺎﺩﻳﺚ ﺍﻟﻤﺨﺘﺎﺭﺓ ٢٣٤١ .
ﻭﺣﺴﻦ ﺇﺳﻨﺎﺩﻩ.
Ma’ana: {Babu wata daa’a ga
wanda bai yi wa Allah Mai girma
da buwaya daa’a ba. Hadithi mai
daraja}.
Kun ga a nan da za a samu wani
fitsararre wanda son mulkar jama’a
ya yi tsatsa cikin zuciyarsa, ko
hassada to toye tunaninsa, har
hakan ya kai shi ga neman take
wasu ingantattun hadithan Annabi
mai tsira da amincin Allah, kuma
ya nemi tilasta wa mutane yin
masa daa’ah a kan hakan to sai a
ce da shi: Ba ka da wannan gurbin
a cikin Kungiyar Jama’atu Izalatil
Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah,
saboda ita kungiyar IZALA an gina
ta ne a kan haramta daa’a da
biyayya ga dukkan mutumin da ya
ki yin biyayya da daa’a ga Allah
Madaukakin Sarki da kuma
ManzonSa mai tsira da amincin
Allah.
*********************************************************************************
Na biyu: An rubuta a SECTION
ONE (b) kamar haka:-
((Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa
Ikamatis Sunnah’ Kungiya ce ta
addinin Musulunci wacce
Musulmai suka kafa ta, sannan
tana da Headquarter watau jigo a
Jos babban birnin Jihar Plateau. Ita
dai kungiya ce wacce ba ruwanta
da duk wata kungiya ta asiri, ko
kuma wata darika ta kowace iri,
haka kuma ba kungiya ce ta wata
siyasa ba)).
Kun gani a nan idan wani ya nuna
son zuciya ya zabi yi wa duniya
karya, ya nemi yi wa kungiyar
IZALA sharri ta hanyar nuna wa
duniya cewa ita kungiya ce
mallakar wani mutum daya tak,
domin dama kungiya ce da wani
mutum guda ya kafa, to sai a ce da
shi karya kake yi azzalumin banza
mayaudari, lalle hakika Kungiyar
Izala kungiya ce da wasu Musulmi
suka hadu suka kafa saboda yakar
bidi’a da tsaida sunnar Annabi mai
tsira da amincin Allah ta hanyar yin
wa’azi da karantar da mutane cikin
makarantu, wannan shi ne abin da
yake rubuce cikin constitution din
Kungiyar wanda mutum 14 suka yi
ittafaki a kan rubuta shi, cikinsu
kuwa har da M. Isma’ila Idris Bin
Zakariyya. Sannan kuma wanda
duk Shaidan ya batar bayan
wannan ittifaki nasu ya je ya yi
wani shaidan karya ba za mu taba
karban maganrsa ba wacce ya
gina a kan son zuciya ko hassada
ko son mulki, sannan mu bar bin
abin da suka rubuta a hade a
lokacin da hammin kowa daga
cikinsu shi ne: Tsaida Sunnar
Annabi mai tsira da amincin Allah
da kuma yakar bidi’un da Shaidan
ya cusa cikin addinin Musulunci.
**********************************************************************************
Na uku: An rubuta a SECTION SIX
PART ONE kamar haka:
((JAGORANCIN KUNGIYA: (I)
Jagorancin wannan kungiya ya
rataya ne a wuyan shugabannin da
wannan kungiya ta ga sun dace su
shugabance ta, wanda kuma za su
kasance a karkashin shugabancin
wani shugaba da ta zaba, don
kuwa Manzon Allah (S.A.W.) ya ce:
“Idan Musulmai uku sun hadu dole
ne su sanya dayansu shugaba,
don tafiyar da al’amarinsu”)).
Kun gani a nan Constitution din
Kungiyar Izala ya fito fili ya ce:
Dukkan shugabannin kungiyar
Izala za su kasance ne a karkashin
shugabancin shugaban da
Kungiyar Izala ta zaba. Saboda
haka, ke nan da za a samu wani
mutum wanda son mulki ya gigita
masa tunanin shi har ya nemi nada
kansa shugaban kowa a cikin
Kumgiyar Izala sai a taka masa
Birki sannan a ce da shi: Kungiyar
Izala ta rika ta tabbatar da cewa
dukkan wanin shugaban wani
bangare na Izala: Shugaban
majalisar Dattijai ne, ko shugaban
Majalisar Iyayen Kungiya ne, ko
shugaban Majalisar Aikace-Aikace
ne, ko shugaban Majalisar Wa’azi
ne, ko shugaban Majalisar
Sadarwa ne’ ko shugaban
Majalisar Shari’a ne, ko shugaban
Majalisar Ilmi da Ilmantarwa ne, ko
shugaban Majalisar Kudi ne, ko
shugaban Majalisar Bincike ne, ko
shugaban ‘Yan’agaji ne, koma
shugaban wani bangare ne daga
cikin bangarorin kungiyar Izala to
shugaban da Kungiyar ta zaba shi
ne shugaban shi.
**********************************************************************************
Na hudu: An rubuta a maganar
karshe cikin Constitution din
Kungiyar IZALA a (iv) CLOSING
REMARKS watau jawabin
RUFEWA kamar haka:-
{Muna kara tabbatar wa jama’ar
Musulmin Duniya cewa, wannan
kungiya tamu kungiya ce da aka
kafa ta domin ta karantar da
jama’ar Musulmi ta hanyan yi
musu wa’azi da kuma kafa
makarantu, ita ba kungiya ba ce ta
siyasa, ba kuma kungiyar asiri ba
ce, haka kuma ba ta darika ba ce
ko wace iri, ita dai kungiya ce ta
addinin Musulunci tsantsa kamar
yadda Annabinmu Muhammad
(S.A.W.) ya taho da shi. Haka
kuma ba ruwanta da tilasta ma
wani ko wassu zamowa dan ko yan
wannan kungiya kamar dai yadda
ya riga ya gabata a can sama,
wannan kungiya dai ba hukuma ba
ce, haka kuma ba ruwanta da
shishigi a harkar hukuncin kasan
nan ko wata kasa, wanda ta
kasance akwai yan wannan
kungiya a cikinta, (manufa dai ita
wannan kungiya ba ta da ikon
hana hukuma yin hukunci a kan
dan wannan kungiya a lokacin da
duk aka same shi da wani laifi a
cikin kasan nan ko wata kasan).
Kuma duk mutumin da ya yi Imani
da Alkur’ani da hadithan Annabi
Muhammad (SA.W.) da kuma
Ijma’in Malamai na kwarai, to ko a
dokan daji yake shi kadai babu
shakka dan wannan kungiya ne.
Haka kuma matukar yana sauraron
wa’azinta babu shakka yin haka
ma taimakawa ne. Ita dai wannan
kungiya ba da wani kati ko wata
shaida na nuna cewa lalle sai ka yi
rajista matukar dai ka yi Imani da
abin da aka fadi a sama to babu
shakka Kai dan wannan kungiya
ne. Kuma sannan kowa na da
hakkin ba wa kowa shawara, ko
nasiha ko mai girman wanda za a
yi wa nasihar ko ba da shawarar,
ko mai kankantar shi mai nasihar
ko shawaran matukar yin shawarar
ko nasihar an yi yadda Musulunci
ya shirya abubuwa}. Intaha.
Kun gani a nan idan har an samu
wasu wadanda Shaidan ya rikitar
da tunaninsu har suke ganin cewa
IZALA tasu ce ba ta wani ba, ko
suke ganin cewa su ne suka riga
shiga IZALA saboda haka duk wani
wanda ba su ba ba yi da wani
hakki a cikinta, to sai a ce da su
karya kuke masu bautar son
zuciya, da tafiya cikin jahilci da
rudani, Yana rubuce cikin tsarin
mulkin Izala cewa: Duk wanda ya
yi imani da Alkur’ani da Sunnar
Annabi mai tsira da amincin Allah
ko ma a Ina yake to lalle shi
wannan dan IZALA ne. Ke nan ba
lafuzan IZALA ba ne abin da yake
muhimmi a’a yin aiki da Alkur’ani
da kuma ingantattun hadithan
Annabi mai tsira da amincin Allah
shi ne muhimmi.
Allah Ya taimake mu Ya nuna
mana gaskiya gaskiya ce Ya ba
mu ikon bin ta, Ya nuna mana
karya karya ce Ya ba mu ikon kin
ta. Ameen.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

11 responses to “MU 'YAN KUNGIYAR JAMA'ATU IZALATIL BID'AH WA IQAMATIS SUNNAH SAI MU YI MURNA MU YI FARIN CIKI MU GODE ALLAH(Dr Ibrahim Jalo Jalingo)”
  1. Yusufshamza Avatar

    Subhanallah ya Allah ka rabamu da kungiya domin kowa annabi ya hane da binta amma yan 419 din addini wato Izala sun rike kungiya amma suna zagin masoya annabi

  2. abdulmalik kaduna Avatar
    abdulmalik kaduna

    Allah ya temaka wa malaman mu na sunnah kuma Allah yakare mana su dr ibrahim jalo jaling, shaik kabiru gombe tauraron zamani shaik saidu hasan jingir, shaik gero argungu, shaik yusuf sambo rigachikun shaik sutus sunna yakubu musa, shaik dr Alhasan sa’id adam, shaik dr dikko shaik dr pakistan shaik sani yahaya jingir shaik bello saminaka shaik balalau yola shaik rabiu daura shaik tekex zaria shaik sani hashir shaik habib yahaya kaura

  3. nasirudden abdulhameed Avatar
    nasirudden abdulhameed

    assalamu’alikum allah ya gafarta malam don allah inoson na dauki wannan kundi nawayarm dajama’akay allah ya karama rayuwa albarka amin

  4. umar idris Avatar
    umar idris

    haba dr jalo, aikaman ne dacewa consitution anrubutashine na jekanayika domin gonnati tayiwa kungiyar register. A kakidodin gonnati dukwata kungiya datakeso ayimata regista, to dolene sai tarubuta consitution inta tabaiwa gonnati, sa an aduba shi kamum ayardashi asan manufanta ayimata regisater. To anan abun dubawa da hankali shi wanda yakeda qur ani da hadith, ijmain malam magabata na farko a hannun shi, to dashi zaiyi amfani ko ko da consitution. Ai mai lafiyaryar hankalima yasan cewa tunda ga abinda aka saukar daga sama qur ani da sunnan ma aiki (saw), tobabu abinbi illa a ajiye wanan abin da wasu suka rubuta ayi aiki da qur ani da sunna. Nabiyu tunda kungiyar take wa azi ba wani malami wanda yataba hawa kan mambari yayi mana wa azi dashi consitution in, to anan abin tabaya shin wai babushi consitution inne ko ko dama anyishine kawai don gonnati. amsa ee, anyine don gonnati. Na uku aika ka mantane cewa da’a matukar in basabawa ALLAH DA MANZON SA BANE to ai anayiwa shugaba da’a domin dole ka kau dasonranka kabishi, to amma anan zaka iya bawakanka amsa domim inkabangare ai akwai mabiya ataredakai kuma zaka umurcesu dawani abu su aiwatarma matukar baisawa ALLAH BADA MAMZON shiba to shi meye sunanshi, kaga ida sunyi ka amintadashi kaga kayi turka da warwarakenan tundashima sunan shi da’a sukama.

  5. baka ganeba shine akwai banbanci tsakanin yiwa allah da manzonsa biyaya dakuma yiwa shuwaga banni biyayya.kagane nasir?

  6. SANUSI HALIL BALI Avatar

    Mude maganan yan izala su hade a najeriya maganace kai gaskiya shine a cewa makwadaitan malamai na izala subar kafirta musulmi da zagin waliyan mu kaman su shehu tijjani,inyass,abdulkadir.saboda haka a gayama kafiru gombe,abubakar giro subar zagin waliyai in sunki sudaina to akwai malam maiguduma to yan izala maganan hadewa babushi face wannan.

  7. SANUSI HALIL BALI Avatar

    Mude maganan yan izala su hade a najeriya maganace kai gaskiya shine a cewa makwadaitan malamai na izala subar kafirta musulmi da zagin waliyan mu kaman su shehu tijjani,inyass,abdulkadir.saboda haka a gayama kafiru gombe,abubakar giro subar zagin waliyai in sunki sudaina to akwai malam maiguduma to yan izala maganan hadewa babushi face wannan.akiyaye

  8. Abubakar Garba Zobali Potiskum Avatar
    Abubakar Garba Zobali Potiskum

    Allah ka saka wa malaman mu na sunnah.Allah ka jikan mahaifan mu. Amiin !!

  9. Ameen

  10. gaskiya ne mudai fatanmu anan shine Allah ya kara nunamana gaskiya mubita , amma tabbas bin sunnar annabi akan yadda yadace da al qur ani maigirma shine babba rabu anan duniya da kiyama amma bawai katsaya kanabin shehu ba ko wani dan Adam din dan Allah shine maulammu shine majibencin lamarinmu yan uwa mudage muyi abinda sunna takoyar da al ur ani maigirma shine babban dacewa

  11. Iliya sani fagge Avatar
    Iliya sani fagge

    Allah ka sakawa malaman mu da alkhairi kuma allah ya jiqan sheikh ja afar kuma allah ya toni asirin wa anda suka kashe sa

Leave a Reply

Categories
Latest updates