Muyi amfani da social media wurin yaɗa akhairi mu guji yaɗa sharri da jita jita

Danna nan domin shiga karatu Online

Ibnul Jawzy yace:

wanda yakeson kada ayyukansa na alkhairi su yanke bayan mutuwarsa, toh ya yaɗa ilimi.

Attathkira 55

Alhamdulillah, a wannan zamani Allah ya sauƙaƙa mana hanyoyin yaɗa ilimi, musamman kafofi na sada zumunta, ya kamata Musulmi yayi amfani da wannan dama domin ya bar wata sadaqa jariyah wacce zata rinƙa samunsa acikin ƙabarinsa, ba dole sai ka zama malami kafin ka yaɗa ilimi ba, ko hadisi ingantacce ko kuma ayah ka yaɗa wani ya gani ya amfana kana da lada, haka nan ko wani wa’azi na malami ka yaɗa wani ya amfana kana da lada, kuma baka san ina wannan lada zata tsaya ba, domin a lokacin da ka yaɗa wani ilmi wani ya amfana da shi, shima ya je ya yaɗa ko yayi aiki dashi wani ya gani ya ɗauka toh haƙiƙa kaima kana da lada,

Abu Huraira Allah ya ƙara masa yarda ya rawaito daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yana cewa

من دعا إلى هدى كان له من الأجر مثل أجور من تبعه لا ينقص ذلك من أجورهم شيئاً، ومن دعا إلى ضلالة كان عليه من الإثم مثل آثام من تبعه لا ينقص ذلك من آثامهم شيئاً

Duk wanda yayi kira zuwa ga shiriya, yana da lada kwatankwacin wa’inda suka bishi cikin wannan shiriya, kuma ba za’a rage musu komai daga cikin ladansu ba, wanda kuma yayi kira zuwa ga ɓata, yana da zunubi kwatankwacin zunubin wa’inda suka bishi kan wannan ɓata ba za’a rage musu komai daga cikin zunubnsu ba

Muslim 2674

Don haka ya dace Musulmi ya kula sosai kan abubuwan da yake yaɗawa a social media, domin laifin ko ladan ba ga wanda ka tura masa kaɗai yake tsaya wa ba, zaka iya tura wani abu mara kyau na tsaɓon Allah laifin yaci gaba da binka har ranan tashin Al Qiyaama, haka nan zaka iya tura wani abu na Alkhairi, ladan yaci gaba da binka har ranan tashin Qiyaama, sai a kula. ya zamto abinda za mu faɗi ko zamu tura baya ƙunshe da tsaɓon Allah.

Inya zamto abinda zamu faɗi babu Alkhairi aciki toh shiru shi yafi mana alkhairi.

Abu Huraira ya rawaito daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yana cewa:

من كان يؤمن بالله واليوم الآخر فليقل خيراً أو ليصمت

Wanda yayi imani da Allah da ranar ƙarshe toh ya faɗi alkhairi ko yayi shiru


Ya kamata Musulmi ya guji yaɗa duk wasu abubuwa da basu da amfani, haka nan kuma ya guji yaɗa abubuwa da zasu jawo masa fushin Allah.

Allah yasa mudace.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates