Neman sani kafin aiki da amfani da lokaci wurin neman ilimin addini

Danna nan domin shiga karatu Online

Shin ka taba zama kayi tunani meyasa Allah ya halicce ka? Kuma shin ko kana gudanar da rayuwar ka wurin cimma wannan abinda Allah ya halicce ka don shi?
Shin a cikin awa 24 da kake dashi a rana awa nawa kabai wa Abinda aka halicce ka don shi?

Allah ya halicce mu ne don mu bauta masa, kuma ba’a bauta masa da jahici,

Kamar yadda yayi bayani

(وَمَا خَلَقۡتُ ٱلۡجِنَّ وَٱلۡإِنسَ إِلَّا لِیَعۡبُدُونِ)
“Ban halicci mutum da aljan ba sai don su bauta min”

Surat: At-tur Ayah: 56

Ya sake cewa game da neman ilimi:

(فَٱعۡلَمۡ أَنَّهُۥ لَاۤ إِلَـٰهَ إِلَّا ٱللَّهُ وَٱسۡتَغۡفِرۡ لِذَنۢبِكَ وَلِلۡمُؤۡمِنِینَ وَٱلۡمُؤۡمِنَـٰتِۗ وَٱللَّهُ یَعۡلَمُ مُتَقَلَّبَكُمۡ وَمَثۡوَىٰكُمۡ)

Ka sani cewa Babu abin bauta wa da gaskiya sai Allah, sannan ka nemi gafarar zunubanka, da kuma na Muminai Maza da mata………….

Surat: Muhammad Ayah: 19

A wannan ayah sai Allah ya fara kawo neman sani kafin aiki.


Ya zama dole akan kowani musulmi ya kebance wani lokaci acikin ranarsa wurin neman ilimin addini kamar yadda yake daukan lokaci mai yawa wurin neman duniya. Domin da ilimin addini ne mutum zai san yadda zai bauta wa Allah ya, kuma tserar da kansa daga wuta.

A wannan zamani da Hanyoyin neman ilimi suka yawaita, ga kafafen sada zumunta da kafafe na yada ilimi ako ta ina, kada ka bari a barka a baya wurin neman ilimin addinin ka.

Ya zamto a kowani rana koda hadisi daya ne ka karanta shi, ka nemi sanin ma’amarsa, ko aya daya.
Haka nan acikin karatuka na malamai da akeyi ya zamto ka sami wasu kana bibiyarsu domin kaima ka fa’idantu da abinda ke ciki.


Allah yasa mudace

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates