Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana koyar da Sahabban sa neman zaɓin Allah(Istikhara) cikin lamuransu duka kamar yadda yake koyar dasu surah daga cikin surorin Al Qur’ani kamar yadda Jabir bn Abdullahi ya bada labari. Annabi yace: idan ɗaya daga cikinku yayi niyyar aikata wani lamari toh yayi raka’a biyu sannan sai yace:
اللهم إني أستخيرك بعلمك ، وأستقدرك بقدرتك ، وأسألك من فضلك العظيم ، فإنك تقدر ولا أقدر ، وتعلم ولا أعلم ، وأنت علام الغيوب ، اللهم إن كنت تعلم أن هذا الأمر خير لي في ديني ومعاشي وعاقبة أمري ، أو قال : عاجل أمري وآجله فاقدره لي ويسره لي ثم بارك لي فيه ، وإن كنت تعلم أن هذا الأمر شر لي في ديني ومعاشي وعاقبة أمري ، أو قال : عاجل أمري وآجله فاصرفه عني ، واصرفني عنه ، واقدر لي الخير حيث كان ثم أرضني به ، قال : ويسمي حاجته }
idan mutum yayi istikhara sai yaga cewa ya sami natsuwa zuwa ga lamarin da yakeson aikata wa to wannan yana nuni da cewa shine zaɓin da Allah yayi masa.
Amma idan kuma bayan yayi istikhara sai zuciyarsa bata karkata zuwa ga wani ɓangare na abinda ya nemi zaɓi akansa ba, toh sai ya sake maimaita istikharar, idan duk da haka bai samu natsuwar zuciya kan lamari ɗaya ba toh sai ya nemi shawarar wanda ya aminta dashi. Sai ya dogara ga Allah, kuma duk abinda Allah ya ƙaddara masa toh shine Alheri.
Leave a Reply