Danna nan domin shiga karatu Online
Istigfari yana daga cikin ayyuka masu falala a addinin Musulunci wanda kuma bashi da wahalar aikatawa. A kowani irin yanayi mutum zai iya yin Istigfari inba a bayan gida yake ba.
·
Allah maɗaukakin sarki yana cewa acikin Suratul Asr. Ina rantsuwa da zamani ɗan Adam na cikin hasara Sai dai wa’inda sukayi Imani, Sukayi aiki na ƙwarai, sannan sukayi wasiyya tsaƙaninsu da bin gaskiya, da kuma Haƙuri. Wa’innan nau’ukan mutane huɗu su kaɗaine basu cikin hasara a duniya.
·
An rawaito daga ibn Sirin yana cewa إن هذا العلْمَ دينٌ فلينظُرْ أحدُكُم مِمَّن يأخُذُ دينَهُ Hakika wannan Ilimin addini ne, ɗayanku ya lura sosai daga waye zai rinƙa ɗaukan addininsa. Haƙiƙa shi addinin Musulunci ya ginu ne kan ilimi, shiyasa ba’a yinsa da jahilci, dole sai mutum ya nemi ilimin yanda ake yinsa. Amma sai dai wurin neman…
·