Yan Mazan Jiya: Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya, Malami Na Allah (24)
Ci gaba…..
- Ibnu Taimiyya ya shiga kurkuku cikin ‘yanci da walwala. Maƙiyansa masu yi masa hassada kuwa suna waje a sake, amma a cikin damuwa da baƙin ciki. Domin shi Ibnu Taimiyya da man abin da yake zaton zai faru da shi ke nan, don haka babu wani abu sabo a wurinsa. Yana cewa: “Ni da man na kasance ina jiran faruwar haka, kuma akwai alheri da maslaha mai yawa a cikin hakan”. Ibnu Taimiyya ya kasance yana buƙatar ya samu inda zai sarara, ya yi nesa da hayaniyar jama’a. Shigarsa kurkuku ya sa ya samu natsuwa, sai ya mayar da hanakalinsa kan abu biyu: Na farko, bautar Allah da karatun Alƙur’ani. Na biyu, sake samun damar bitar ra’ayoyinsa da sake rubuta su a cikin natsuwa.
- A wannan lokaci ne ya samu damar rubuta tafsirin ayoyin Alƙur’ani masu yawa. Kuma alaƙarsa da mutane ba ta yanke ba, yana ci gaba da samun saƙonnin mutane da tambayoyinsu, yana kuma rubuta musa amsa. Da zarar kuma ya rubuta wani sako yanzu ne cikin gaggawa zai yaɗu cikin jama’a, a yi ta tattauna a kansa. Wata ƙila rashin ganin sa a cikinsu ya sanya sun ƙara damuwa da lamarinsa, don haka sai yake yin tasiri a zukatansu fiye da lokacin da yake cikinsu. Domin duk abin da ba a so a sani, ake ta ɓoɓɓoye shi, idan har ya fito ya bayyana, to sai ya fi yaɗo a tsakanin mutane. Saboda jama’a za su yi ta bibiyar sa, suna neman sa, don su karanta shi a tsanake, domin ya zama wani abu mai tsada da daraja, ta haka sai ka ga cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ya shiga hannun kowa.
- Da maƙiyan Ibnu Taimiyya suka lura da cewa, a she an yaka ne ta tashi. Domin kuwa gangar jikin Ibnu Taimiyya kaɗai suka iya tsarewa. Ba su iya tsare ra’ayoyinsa da aƙidarsa ba. Don haka sai suka fara sabon tunani na yadda za su ɓullo wa lamarin. Sai suka shirya wani makircin sabo a wurin masu iko, domin su dakatar da fitowar wannan haske daga kurukuku zuwa hannun malamai.
- A ƙoƙarin cimma wannan mummunan makirci ne, a ranar 9 ga watan Jumadal Akhira, na shekarar 728 aka kwashe duk littattafan da suke wajen Ibnu Taimiyya da takardun rubutu da alƙaluma da tawada. Gaba ɗaya aka hana shi karanta komai. A farkon watan Rajab na wannan shekarar kuma aka ɗauke littafansa na karatu da waɗanda ya rubuta zuwa wani babban ɗakin ajiyar littattafai. Yawan waɗannan littattafai sun kai mujalladi sittin da kuma ɗaurin kundaye goma sha huɗu.
- Ibnu Kasir ya bayyana dalilin da ya jawo aka yi Ibnu Taimiyya wannan aika-aika, inda yake cewa: “Dalili shi ne martanin da Ibnul Ikhna’i ya mayar wa Ibnu Taimiyya a kan mas’alar ziyara. Sai Ibnu Taimiyyya shi ma ya mayar masa da martani, ya kuma nunu jahilcinsa da ƙarancin iliminsa. Da Ibnul Ikhna’i ya karanta martanin Ibnu Taimiyya sai ya ji haushi, ya kai shi ƙara wajen Sarki. Sarki ya yi umarni da a kwashe duk littafan da suke tare Ibnu Taimiyya”. [Al-Bidaya, Wan-Nihaya, juz. 18. Sh. 293].
Za mu ci gaba in sha Allah….
Leave a Reply