2.0. Kyautata Niyya:
2.1. Kyautata niyya watau ikhlasi, ginshiƙi ne na kowace ibada a Musulunci. Ilimi ibada ce babba, domin da shi ne ake sanin Allah da annabawansa da abin da ya ya saukar da sauran shikashikan imani. Mai neman ilimi shi ne farkon wanda za a yi tsammanin zai tsarkake niyyarsa, ya kyautata nufinsa tsakaninsa da Mahaliccinsa, ya nemi ilimi don Allah, ba don wata manufa ta ƙashin kansa ba. Idan ya yi haka, to da ma hakan ake kyautata masa zato zai yi tun farko. Amma idan ya yi akasin haka, to lalle al’amarinsa zai yi matuƙar muni, zai zamanto kamar yadda Hausawa kan ce, ‘ana zaton wuta a maƙera sai kuma kwatsam ga ta a masaƙa’.
2.2. Hadisi mai matuƙar razanarwa da ban tsoro ga ɗalibin ilimi ko ga malami, shi ne hadisin da Ka’abu ɗan Malik ya ruwaito daga Annabi (SAW) yana cewa, “Duk wanda ya nemi ilimi domin ya yi kafaɗa da kafaɗa da malamai, ko kuma don ya yi jayayya da jahilai, ko kuma don ya jawo hankulan mutane zuwa kansa, to wannan Allah zai shigar da shi wuta”. [Tirmizi, #2654, Ibn Maja, #253]. A hadisin Jabir ɗan Abdullahi, Annabi (SAW) cewa ya yi, “Kada ku nemi ilimi domin kawai ku riƙa yi wa malamai fariya da shi, ko domin ku yi jayayya da jahilai da shi, ko kuma don ku jagoranci majalisai da shi. Duk wanda ya yi haka, to wuta ta tabbata gare shi, wuta ta tabbata gare shi”. [Ibn Hibban, #77].
2.3. Babban abin da zai jawo haka, kamar yadda malamai masu sharhin hadisai suka faɗa, shi ne rashin tsarkake niyya da neman suna da fariya da kuma neman abin duniya. Waɗannan duka ɓacin niyya ce take haddasa faruwarsu. Neman ilimi don kawai samun tagomashin duniya alama ce da ke nuna mutuwar zuciya. Malik ɗan Dinar ya tambayi Alhasan al-Basri, ”Mece ce uƙubar malami?” Sai ya ce masa: “Mutuwar zuciya”. Sai ya tambaye shi, “Mene ne kuma mutuwar zuciya?” Sai amsa masa da cewa: ”Neman duniya da aikin lahira”. [Ahmad, az-Zuhd, 265].
2.4. Zahabi, babban masanin tarihin Musuluci yana cewa: “Magabata sun kasance masu neman ilimi don Allah, sai wannan ya sa suka ɗaukaka, suka kuma zamanto shugabanni abin koyi. Wasu kuma suka fara neman ilimi ba don Allah, suna tsaka da nemansa sai kawai suka farka, suka yi wa kansu hisabi, daga nan sai iliminsu ya ja su zuwa ga ikhlasi. Kamar yadda Mujahid da waninsa suke cewa: “Mun nemi ilimi ba tare da wata niyya ta a zo a gani ba, sai daga bisani Allah ya arzuta mu da kyakkyawar niyya. Wasu kuma cewa suka yi: “Mun nemi ilimi ba don Allah ba, amma ilimin ya ƙi, sai dai ya zamo don Allah”. [Zahabi, Siyarun Nubala’, juz. 7, sh. 152].
Za mu ci gaba in sha Allah…
Leave a Reply