Sunnar Al fijr ko kuma Raka’oi biyu da akeyi bayan ketowar alfijr suna da falala sosai, ba wajibi bane mutum yayi sai da sunnah ce mai ƙarfi.
An rawaito daga Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi yana cewa:
Rakao’i biyu ta Al fijr tafi duniya da abinda ke cikinta alheri
Muslin ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 725
idan mutum bai samu daman sallatanta ba har akayi sallar asubahi toh zai iya yinta bayan Sallan asubahi ko kuma lokacin sallar walaha
Leave a Reply