Tarihin Annabi Fitowa ta 1: Haihuwar Annabi

سيرة النبي
Download

Haihuwar Annabi (Sallallahu alaihi Wasallama).

Kafin Hijira: 53

Shekarar Miladiyya: 571


Maluman Tarihi sun samu tsaɓani kan takamammen rana da kuma wata da aka haifi Manzon tsira(Sallallahu alaihi Wasallama). Sai dai kuma sun samu haɗuwa kan cewa an haifi Manzon Allah ne Ranan Litini a shekarar giwaye.

Ibnul Qayyim yana cewa:

babu tsaɓani kan cewa an haifi Manzon Allah ne a cikin Garin Makkah, sannan kuma an haifeshi ne a shekarar giwaye.

-Zadul Ma’ad Fi Hadyi khairil ibaad 1/76.


An rawaito daga Ibn Abbas Allah ya ƙara Masa yarda yana cewa:

An haifi Manzon Allah ne A shekarar Giwaye.


Wani shekara ne Shekarar Giwaye?

Anyi wa wannan shekara laƙabi ne da shekarar giwaye domin a cikinta ne Sarkin habasha(Abrahata) ya tura runduna zuwa makkah domin rushe ɗakin ƙa’abah, domin ya wajabta wa mutanen makkah zuwa Cocinsa da ya gina domin yin ibada, acikin Wannan runduna da ya tura akwai babban giwa. Amma Allah bai basu daman rushe ɗakin ƙa’aba ba.


Dalilin cewa an haifi annabi (Sallallahu alaihi Wasallama) ranan litini shine: an rawaito hadisi daga abi Qatada Al-Ansari. An tambayi Manzon Allah kan azumin da yakeyi rabar litini sai yace:

Wannan rana ne da aka haifeni aciknsa, sannan kuma rana ne da aka sauƙarmin da wahayi.

-Muslim 1162.

Wannan hadisi yana nuna cewa ba ranar juma’a aka haifi Manzon Allah ba.

An haifi Manzon Allah Bayan rasuwar mahaifinsa, mahaifinsa ya rasu lokacin mahaifiyarsa tana da cikinsa. Manzon Allah yayi rayuwarsa a matsayin Maraya.


Wannan Tarihi ina tsaƙuroshi ne daga Mausu’ah ta Tarihi ta “dorar.net” domin karantawa cikin harshen larabci Danna nan.

Click Here to Support our work

Leave a Reply

%d bloggers like this: