Tarihin Annabi Fitowa ta 2: Tsaga Ƙirjin Manzon Allah da Mala’ika Jibrilu yayi Lokacin yana yaro

Tsaga Ƙirjin Manzon Allah da Mala’ika Jibrilu yayi Lokacin yana yaro:

Kafin Hijira: 49

Shekarar Miladiyya: 575


An rawaito hadisi daga Anas Allah ya ƙara masa yarda yace:

Mala’ika Jibrilu yazo wurin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama lokacin yana wasa da yara, ya kamashi ya kwantar dashi, sai ya tsaga ƙirjinsa, sai ya ciro zuciyarsa, sai ya cire wani gudan jini daga zuciyar, sai yace wannan shine rabon da shaiɗan yake dashi a jikinka, bayan haka sai ya wanke zuciyar A cikin wani kwano na Gwal da ruwan zamzam, sannan sai ya haɗe zuciyar ya kuma maidashi mazauninsa, bayan da wa’innan yara da suke wasa tare da Manzon Allah suka ga haka sai suka garzaya zuwa ga mai rainonsa(Halimatu-ssa’adiyyah). Suka bata labarin cewa An kashe Manzon Allah, sai suka zo wurin Mazon Allah suka sameshi yanayinsa ya canza alaman cewa akwai wani abu da ya sameshi.

– Muslim 268


Wannan shine Tsaga zuciyar annabi da akayi karo na farko, karo na biyu shine lokacin da za’a turoshi a matsayin Manzo, sai kuma karo na uku lokacin da za’ayi isra’i da mi’iraji dashi.

Sannan kuma wannan tsaga ƙirji da akayi wa Manzon Allah yana daga cikin Alamomi da mu’ujizozi da suka fara bayyana masa tun yana yaro wanda ya fara nuni da cewa akwai wani abu mai girma a tattare dashi.


Wannan Tarihi ina tsaƙuroshi ne daga Mausu’ah ta Tarihi ta “dorar.net” domin karantawa cikin harshen larabci Danna nan. Domin yin gyara Danna nan

Donate to support Us. May Allah reward You with Jannah
Account Number: 3077875210
Account Name: Mukhtar Muhammad
Bank: First Bank Nigeria
You can also Click Here to Donate Online

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You may use these HTML tags and attributes: <a href="" title=""> <abbr title=""> <acronym title=""> <b> <blockquote cite=""> <cite> <code> <del datetime=""> <em> <i> <q cite=""> <s> <strike> <strong>

%d bloggers like this: