Jawabin da Malam Dahiru
Bauchi ya yi a shirin safe na BBC
hausa a yau 21/5/2015, hakika
ya fadi daidai cikin wani sashi
nasa, ya kuma kasa fadin daidai
cikin wani sashi nasa.Ya fadi daidai a inda ya kafirta
‘yan Tijjaniyyar nan da suka yi
bukin maulidin Sheik Ibrahim
Inyas a garin Kano, sannan a
wajen wannan buki nasa
wasunsu suka yi ta furta
kalaman batunci ga Annabi Mai
tsira da amincin Allah.
Amma bai fadi daidai ba a inda
ya ce babu abin da ake kira Ahlul
Hakikati cikin Darikar Tijjaniyyah,
ya kuma fadi hakan ne duk kuwa
da cewa a cikin Darikar tijjaniyyah
a kwai yarda da abin da ake kira
Wahdatul Wujudi, shi kuwa
Wahdatul Wujudi tabbas yana
daga cikin lazimin wannan akida
yarda da irin maganar cewa
Ibrahim Inyas Allah ne.
Ko shakka babu a cikin darikun
Sufaye musamman Darikar
Tijjaniyyah a kwai gurbatattun
akidu daban daban na tozarta
Alqur’ani, da tozarta Manzon
Allah mai tsira da amincin Allah,
da ma tozarta Zatin Allah shi
kanSa, hakika dukkan masu
nazarin littattafan wadannan
darikun sun san da haka.
To amma dai a takaice muna iya
cewa an dan samu ci gaba cikin
jawaban da shi Malam Dahiru
Bauchi ya yi; domin a da irin
wannan bayanin ne na bayyanar
da kafircin wasu akidu na Sufaye
idan Ahlus Sunnah masu
Da’awah suka bayyana su ga
Duniya zai a ji wasu daga cikin
masu gafala ko son zuciya suna
ta cewa: ‘Yan Izala na kafirta
Musulmi!
Muna fata Malaman Sufaye a ko
ina suke za su yi hakuri, su kara
tunani su sa tsoron Allah cikin
lamuransu su daure su yi
Musuluncin nan kamar yadda
Annabi Mai tsira da amincin
Allah tare da Sahabbansa suka yi
shi. Allah Ya taimake mu.
Ameen.
Leave a Reply