TAMBAYA TA 1:
Mene ne manufar yin aure da fa`idarsa?
AMSA:
Yana daga babbar manufar yin aure biyayya ga umarnin Allah da Manzonsa r. Dalili kuwa shi ne faxin Ubangiji I cewa:
…فَانْكِحُوا مَا طَابَ لَكُمْ مِنَ النِّسَاء… النِّسَاء:3
Ma’ana:
…Ku auri abin da ya daxaxa gare ku na daga mata…
Da kuma hadisin da ya tabbata daga Anas Ibn Malik t cewa Manzon Allah r ya ce:
…فَمَنْ رَغِبَ عَنْ سُنَّتِي فَلَيْسَ مِنِّي.
Ma’ana:
…Wanda ya qyamaci sunnata ba ya tare da ni.
Haka kuma yana daga cikin fa`idar yin aure:
Samun nutsuwa da kwanciyar hankali da soyayya da qauna da jin qai da rahama da zamantakewa ta gari tsakanin ma`aurata. Dalili kuwa shi ne faxin Ubangiji I cewa:
وَمِنْ آيَاتِهِ أَنْ خَلَقَ لَكُمْ مِنْ أَنْفُسِكُمْ أَزْوَاجًا لِتَسْكُنُوا إِلَيْهَا وَجَعَلَ بَيْنَكُمْ مَوَدَّةً وَرَحْمَة… الروم: 21
Ma’ana:
Yana daga cikin ayoyinsa, halitta muku mata daga jinsinku domin ku samu nutsuwa a tare da su, Ya kuma sanya soyayya da jin qai a tsakaninku…
Samun zuriya ta gari, wanda ta haka ne ake gane asalin mutane da dangantakarsu, savanin hanyar fasadi da zina. Ta irin wannan zuriya ta gari kaxai ne za a iya samun `ya`ya masu biyayya ga iyaye da yi masu kyawawan addu’o’i.
Aure yana taimaka wa musulmi wurin kawar da idonsa daga kallon haram da kiyaye kansa daga faxawa cikin alfasha.
Samar da al`umma ta gari wadda Manzon Allah r zai yi alfahari da yawansu a ranar alqiyama, a kan al’ummomin sauran Annabawa.
Xaukar nauyi da tausayawa da `ya`ya na gari suke yi wa iyayensu yayin da suke da buqata.
Leave a Reply