Allah cikin hikimar sa ya boye mana sanin gaibi, kuma aka hana mu damar sanin mi zai faru gobe, hakanan ba rayin da yasan ranar ajalin sa ko garin ajalin sa. Kuma samu da rashi, ko juyawar yau da gobe duk naga Allah shi kadai ubanginjin talikai.
Mu dai ‘yan adam sai buri, da yawan tanadi, ga kwadayi da son mu samu mu tara, gamu da sha’awa a ciki da wajen zukatan mu, da sauran bukatun dan adam a rayuwa.
Hakika rashin sanin abinda zai faru gobe darassi ne, kuma nuni garemu cewa muyi taka tsan-tsan da wannan rayuwa, mu yiwa kan mu tanadin alheri duniya da lahira.
Ya kai dan uwa na, kada ka wulakata wani baka san gobe mi zai zama ba. Kada ka tozarta addini don baka san kana wani aiki mutuwa zata riske ka ba. Kada kaci haramun don baka san miye abincin ka na karshe ba. Kowa ya nisanci alfasha da miyagun aiyuka don bawanda yasa aikin sa na karahe.
Muyi don Allah mu bari don Allah cikin dukkan aiyuka da huldodin mu na rayuwa. Mu bi hanyar Allah da ta Manzon Allah (saw) insha Allahu ba zamu tabe ba.
Ina rokon Allah ya kara mana ilimi mai amfani, ya datar damu natsuwa da karuwar imani, amin.
Leave a Reply