Wannan ba Barkwanci bane Cin Mutuncin Addinin Musulunci ne

Danna nan domin shiga karatu Online

Allah maɗaukakin sarki yace:

Haƙiƙa za’a jarrabe ku cikin Dukiyoyinku, Da kawunanku, sannan kuma zakuji cutar wa mai yawa daga wa’inda Allah ya basu littafi gabaninku(Yahudawa da Nasara) da Mushrikai

Surat Aal Emran: 186

Cutar da Addini da maƙiya addini sukeyi abu ne wanda Allah ya bada labarin cewa zasu yi shi, amma haka bashi yake nufin muyi shiru mubarsu suci gaba da aikata hakan ba, dole mu tashi mu fuskance su muyi iya ƙoƙarinmu wurin baiwa Addinin mu kariya.

Haƙiƙa wannan ɗan wasan Barkwanci mai suna Chinedu ya kamata mahukunta su nemeshi kuma su dakatar dashi ya bar irin wannan Barkwanci da yakeyi wanda yake fita da siffa ta Musulunci amma yana yin abubuwa da suka tsaɓa wa Addinin Musulunci, Hakan Ɓatanci ne wa Addinin Musulunci kuma bai dace Musulmai su saka idanu suna kallo suna shiru ba. Ya kamata masu faɗa aji su sanya baki cikin wannan lamari.

Sau da dama zaka ganshi zai saka kaya wanda duk wanda ya ganshi da wannan kaya abinda zai zo masa zuciya shine wannan Musulmi ne kuma mai riƙo da Addini, amma kuma sai kaga irin abubuwa da yakeyi a barkwancinsa Ya tsaɓa wa koyarwar Addinin Musulunci.

Abin haushi ma shine yadda Wasu Musulman basu fahimci irin Cin zarafin addini da yake yi ba, zakaga suna kallon Barkwancinsa, suna dariya har suna yaɗa wa. Ya kamata muji tsoron Allah, idan har bazamu iya tashiwa mu kawar da Mummunar abu ba, to kada mu taimaka wurin yaɗa shi.

Ya kamata mu faɗakar da mutane kan hatsarin wannan mutumi, da Wasu ireirensa, Kuma ya kamata Mahukunta su shiga lamarin don wannan cin zarafin Addinin Musulunci ne.

Wataƙila wani yace Ai Shiga da yakeyi shiga ce ta Larabawa ba ta Musulmai bane kawai

Wanda zai faɗi wannan Son zuciya ce zata sanya shi ya faɗi haka, ko rashin sani. domin koda shiga ce ta larabawa amma ta juya ta zama shiga ta Musulmi a faɗin duniya baki ɗaya, ta yadda irin shiga da yakeyi da zarar kaga Mutum dashi aka tambaye ka wannan Shigar Wasu mabiya Addini ne? Zaka ce Musulmai. Saboda haka koda cewa shiga ce ta Larabawa a asali amma a duk faɗin Duniya Musulmai su suka fi amfani dashi, Saboda haka ya zamo shiga ce tasu baki ɗaya. Kamar ɗaura rawani ne, wannan Al’ada ce ta larabawa, amma daga baya ta zama Al’ada ta Musulmai baki ɗaya shiyasa zaka ga limamai da sarakuna dashi, wannan akwai shi da yawa cikin lamuranmu na yau da kullum, saboda haka duk wanda zai sanya rawani yanzu ana ganinsa za’a ce wannan Musulmi ne, saboda Musulmai ne aka sansu da sanya Rawani, to haka nan irin wannan shiga da wannan mutumi yakeyi. Ya kamata Musulmai masu kishi su daina bibiyarsa da yaɗa ayyukan sa domin hakan taimakawa ne wurin rusa Addinin Musulunci

Allah yasa mudce.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates