Yaya ake Sallar idi a gida

Danna nan domin shiga karatu Online

Idan Musulmai suka kasa ƙaddamar da Sallar idi a Masallatan idi ko kuma Masallatai da ake salloli kamar irin hali da muke ciki na Annobar Covid19, ta yadda a wasu wuraren mutane bazasu iya fita zuwa yin Sallar idi ba toh Musulmi yana da zaɓi biyu idan zaiyi Sallah a gidansa.

  1. Ko dai ya Sallace ta a gida kamar yadda ake sallar idi. Raka’a biyu Raka’ar farko zaiyi kabbara guda 7 banda Kabbarar harama ko shida. Zai karanta suratul A’ala ko Suratu Qaf idan ya sami dama. sannan a raka’a ta biyu zai yi kabbara biyar banda Kabbarar tasowa, sai ya karanta suratul ghashiya ko Qamar idan ya sami dama.
  2. Ko dai ya sallace Idi raka’a huɗu, ya sallame bayan raka’a biyu, ya ƙara kawo raka’a biyu yayi sallama. Ko kuma ya sallace ta raka’a huɗu ba tare da sallama ba kamar sallar Azahar. Amma bazaiyi wa’innan ƙabbarori da muka ambata a baya ba, zai sallace ta ne kamar yadda yake sauran salloli babu canji.

Sannan ana iya yi tare da jama’a ko mutum shi kaɗai. Idan ya ga dama kuma ba sai ma yayi ba, sabida Sallar idi ba farilla bace a magana mafi inganci.

An rawaito daga Anas dan Malik cewa ya sallaci idi tare da iyalansa raka’a biyu kamar Sallar idi a lokacin da yake zaune a wajen garin da ake yin sallar idi.

Haka nan an rawaito daga Ibn Mas’ud yace wanda Sallar idi ta kuɓce masa zai sallace ta raka’a huɗu ne.

Sannan an rawaito daga Aliyu Bin Abi Talib cewa yayi umarni ayi sallah da gajiyayyu a masallatai raka’oi huɗu.

Kamar yadda kuka gani cewa babu wani Nassi a bayyane daga Annabi wanda yayi bayani kan yadda za’ayi Sallar idi a gida, sai dai anyi ƙiyasi ne kan wannan Aathar da muka kawo a sama. Sabida haka zai iya yiwuwa Ijtihadin maluma ya banbanta kan wannan Mas’ala.

Allah yasa mudace, ya kuma kawo mana ƙarshen wannan Annoba ta corona.

Wani sashi na wannan rubutun na fassara shi ne zuwa Hausa daga Maqala da aka saka a shafin dorar.net domin duba cikakken bayani Danna nan

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates