Yin Barkwanci da wasan kwaikwayo mai ɗauke da isgilanci ga Addini Kafirci ne

Danna nan domin shiga karatu Online

A lokacin da ilimin addini yayi ƙaranci a cikin Al’ummah, jahilci ya yawaita zaka rinƙa ganin abubuwa masu ban mamaki matuƙa, ta yadda zaka ga mutane suna wasa da addini amma ba tare da sun sani ba, domin a haƙiƙa inda sun san cewa wannan abu da sukeyi ya tsaɓa wa Addini da da yawa daga cikinsu bazasu yi ba, duk da akwai wa’inda suna yin abinda sukeyi alhali suna sane da cewa wannan abu bashi da kyau.

Daga cikin abubuwa da suka shahara a wannan zamani namu shine: “wasan barkwanci” wanda ake kira “comedy” a Turanci. Da yawa mutane sun ɗauki wannan hanya wurin neman samun raha, su kuma masu yin wannan abu sun mai da shi a matsayin hanyan neman kuɗi.

Toh abin takaici shine ta yadda wa’innan masu yin wannan wasanni na barkwanci suka fara wuce gona da iri ta yadda wasan nasu ta fara shiga fagen wasa da addini. ta yadda zaka ga akan nuno mutum yana Sallah amma acikin sallan yana aikata abubuwa domin ya sanya mutane suyi dariya. Wanda wannan mummunan aiki ne wanda ka iya kai mutum ga kafirci. Domin izgili da addini Kafirci ne kamar yadda Allah ya bada labari acikin Alqur’ani.

وَلَئِنْ سَأَلْتَهُمْ لَيَقُولُنَّ إِنَّمَا كُنَّا نَخُوضُ وَنَلْعَبُ قُلْ أَبِاللَّهِ وَآيَاتِهِ وَرَسُولِهِ كُنتُمْ تَسْتَهْزِئُونَ ۝ لا تَعْتَذِرُوا قَدْ كَفَرْتُمْ بَعْدَ إِيمَانِكُمْ

Attaubah: 66

Allah yace: Idan ka tambaye su, zasu ce mu mun kasance ne kawai muna garauniya ne da wasa, kace musu shin da Allah ne da Ayoyinsa, da kuma Manzanninsa kuke izgili? Kada ku bada wani uzuri kun riga kun kafirta bayan imaninku.

dalilin sauƙar wannan ayah shine wasu daga cikin Musulmai a yaƙin tabuk sun faɗi munanan zance game da sahabban Annabi, suka sifanta su da cin abinci mai tsanani, da tsoro da kuma ƙarya, da Allah ya zarge su kan wannan zance da sukayi sai suke bada uzuri cewa ai su ba da gaske suka faɗi abinda suka faɗa ba, kawai sunyi haka ne suna raha, da wasa. Sai Allah ya mayar musu da martani cewa Shin da Allah da Ayoyinsa da kuma Annabinsa suke izgili? Sun kafirce.

Wannan ayah take nuna cewa duk wanda zaiyi izgilanci ga Ayoyin Allah ko hadisan Annabi, ko kuma addini ya kafirta.

amma sabida jahilci sai kaga wa’innan comedians ɗin suna Wasan comedy da Sallah ko kuma Azumi ko kuma wani aiki na addini, kamar jifan shaiɗan. Sai kaga waninsu na cewa na jefeshi a wuri kaza. Kamar ya ganshi. Kawai sabida ya bada dariya. Toh haƙiƙah mai wannan aiki ya sani wannan aiki nashi ka iya kaishi ga kafirci in bai tuba ya daina ba. Haka nan kuma masu yaɗa irin wa’innan abubuwa ya kamata suji tsoron Allah su sani cewa ba’a wasa da Addini. Kuma Allah zai tsayar dasu ya tambaye su duk abubuwan da suka aikata. Kuma duk yaɗa wa da sukayi wani ya gani shima ya yaɗa toh haka laifi zata ta binsu har zuwa ranar tashin AlQiyaama.

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yana cewa:

ويلٌ للَّذي يحدِّثُ فيَكذِبُ ليُضحِكَ بِه القومَ 

، ويلٌ لَه ، ثُمَّ ويلٌ لَه

Abu dawood: 4990
Attirmidi: 2315

Annabi yace: Azaba ta tabbata ga wanda zaiyi magana yayi ƙarya domin ya sanya mutane dariya, Azaba ta tabbata gare shi, Azaba ta tabbata gareshi.

Sabida haka ƴan’uwa ya kamata mu kula da harcenmu mu rinƙa sanya masa linzami. Sannan mu kula da abubuwa da muke yaɗa wa a social media. Domin za’a tambaye mu a kansu. Allah yasa mudace.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates