Godiya Sun Tabbata ga Allah maɗaukakin sarki, Alhah yayi daɗin tsira wa Shugaban mu Annabi Muhammad Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi.
An rawaito hadisi ingatacce daga Uwar Muminai Aisha Allah ya ƙara Mata yara tace:
Nace: Ya Manzon Allah shin kana gani idan nasan wani dare ne daren Lailatul Qadri meye zan faɗa aciki? Sai yace kice: “Allahumma Innaka Afuwwun Tuhibbul Afwa fa’afu anni”
اللهم إنك عفو تحب العفو فاغف عني
Attirmidhi: 3513. Ibnu Maja: 3850
Lailatul Qadri shine dare mafi girma acikin darare domin ibada acikin sa yafi alheri fiye da ibada acikin watanni dubu kamar yadda Allah ya bada labari acikin Suratul Qadr Ayah ta 3
Kuma ana samun wannan dare ne acikin wata Ramadana, a goman ƙarshe, a wutiri.
Anaso Mutum idan ya tashi yin ibada acikin wa’innan darare na goman ƙarshe na Ramadan ya yawaita yin wannan Addu’ar domin ya fito ne daga bakin Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi. Kuma ya ƙunshi duk wani abinda mutum yake buƙata, domin idan Allah yayi wa mutum rangwame to haƙiƙa ya tsira.
Allah ya sada mu da daren Qadr. Ameen
Leave a Reply