Bismillahirrahmanirraheem.
BAMBANCIN AQEEDAN SUNNAH DA SAURAN AQEEDU
Alhamdulillah!!! Allah ka Tabbatar damu akan sunnar annabi(sallallahu alaihi wasallam)
Haryanzu a duniyar Aqeedu koma wata irice, babu wata aqeeda da take fita tayi bayaanin aqeedunta dalla dalla, sannan ta yadasu a kasuwanni kowa ya karanta irin aqeedar sunnah, duniya ta shaidi ahlussunnah da haka, amma inka dubi sauran addinai da aqeedu zaka samu kodai su rinka boye aqeedunsu, ko kuma su rubutashi amma sai suce ba kowane ke iya ganeshi ba, dubi addinin shi’ah da yahudu, zaiyi wuya ka sami litattafan wa’innan addinai biyu ako’ina sai kaje tushensu, sannan baza’a yarda ka mallaka ba sai ansan kaima gogaggene acikin aqeedar, sai dai inkayi musu taqiyyah, Hakanan inka dubi littafan da ya shafi mabiya addinin kiristanci da kuma mabiya aqeedar sufanci, suma haka ba’a samun littafansu ako’ina, haka nan inka sameshi sai suce maka bazaka iya fahimta ba saboda ba kowa ke fahimta ba, Haka kiristoci suke fada akan bible, hakanan sufaye suke fadi game da littafansu… To wannan wace irin aqeedah ce baza’a fita ayiwa al’ummah bayaani su gamsu ba? Sai ayita nuku nuku? Shin akwai gaskiya cikin wannan lamari kuwa? mu aqeedah tamu ta ahlussunnah wal jama’ah, ta ginu ne kan Qur’ani da hadisi… Haka nan duk wata hukunce hukunce ta addini da zamuyi amfani da’ita, itama ta ginu ne kan Qur’ani da hadisi, da ijma’I da kiyaaas.. Duk abinda kaga mun fada toh muna da hujjar fadansa….. Shi yasa zakaga malaman ahlussunnah akoda yaushe suke bude majlisi na karantar da aqeedah.. Toh sauran aqeedu suma suyi haka mana dun Allah. Yau muga an bude majlisin karantar da aqeedar shi’anci da sufanci. Wallahi da wannan abu zaiyi kyau sosai. Allah ka tabbatar damu akan sunnar fiyayyen halittanka, Allah ka nuna mana Gaskiya Ka bamu daman binta Ka nuna mana karya ka bamu daman guje mata sannan ka rugujeta…
Leave a Reply