BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM MU KARANTA TARIHI TARIHIN RIKICIN TATTAR (MAJLISI NA 2)(Dr. Mansur Sakkwato)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
MU KARANTA TARIHI
TARIHIN RIKICIN TATTAR
(MAJLISI NA 2)
Asalin Tattar:
Asalin Tattar (kuma ana ce masu
Mugul) kabilu ne na kasar Sin
(China). Suna da jinin turkawa, kai
a Turkiyyah ma babu kabilar da ta
kai yawan ta su a wancan lokaci.
Ba a taba samun labarin su ba sai
da suka bayyana kwatsam a
karshen karni na shida; shekarar
599H karkashin jagorancin
sarkinsu Jinkizkhan (Sarkin
duniya). Amma an samu labarin
cewa kafin haka, sun yi ta fadace-
fadace tsakanin junan su, bayan
galabar Jinkizkhan ne suka bullo
ma al’ummar musulmi. Tattar
mutane ne masu bautar rana,
kuma sun yi imani cewa, tun da
Allan da yake sama guda daya ne
to dole ne a duniyar kasa a samu
sarki guda. don haka suke yaki a
kan tabbatar da wannan manufa. A
addininsu babu haramun; kome
ana iya yi. Don haka suna cin kare,
suna cin alade, kuma ba su aure;
kowa na iya zo ma macce, ba
wanda ya san dan wani. Suna da
kishin kasa wanda ya zarce iyaka.
A cikin su akwai masu da’awar
musulunci, suna kalmar shahada,
suna kuma ganin girman musulmi
amma basu yakar kowa sai a kan
‘yan kasancin nan nasu.
A majlisi na uku zamu je kai tsaye
ga shigowarsu kasar musulunci in
Allah ya so.
Darasi da zai zoma kullum sau
daya ko sau biyu gwargwadon
yadda Allah ya bada iko. Ku biyo
mu.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

One response to “BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM MU KARANTA TARIHI TARIHIN RIKICIN TATTAR (MAJLISI NA 2)(Dr. Mansur Sakkwato)”
  1. Rahim Daya Avatar

    its realy a great site there is so many thing of religious for learn …..

Leave a Reply to Rahim DayaCancel reply

Latest updates
Categories