DARASI NA GOMA SHA HUDU (14)SHUBUHOHIN SHI’A A KAN FADIN MANZON ALLAH (SAW) GA SAYYADINA ALI (RA) “KAI NE NI, NI NE KAI” DA BAIWA SAYYADINA ALI TUTA RANAR YAKIN KHAIBARA(Mal.Aminu Ibrahim Daurawa)

Danna nan domin shiga karatu Online

SHUBUHOHIN SHI’A A KAN
FADIN MANZON ALLAH (SAW)
GA SAYYADINA ALI (RA) “KAI NE
NI, NI NE KAI” DA BAIWA
SAYYADINA ALI TUTA RANAR
YAKIN KHAIBARA.
Shubuha ta goma sha daya da
`Yan Shi’a suke yadawa ita ce: –
fadin Manzon Allah (S.A.W) ga
Sayyadina Ali: (R.A)- “Kai ne ni, ni
ne kai” da kuma fadinsa ga
Sayyadina Ali (R.A) ranar yakin
Khaibara. “Lallai zan bayar da tuta
gobe – ga wani mutum da yake
son Allah da Manzonsa, kuma shi
ma Allah da Manzonsa suke
sonsa, Allah zai bude Khaibara a
hannunsa”
‘Yan Shi’a sukan kafa hujja da
wadannan Hadisai, don su yada
munanan akidunsu.
Jawabi a kan wannan shi ne ta
fuskoki kamar haka: –
1) Wadannan Hadisai duk da cewa
ingantattu ne, amma ba su da
alaka da akidun Shi’a.
2) A riwayoyin Shi’a na Hadisin
Khaibara suna kara wasu abubuwa
kamar haka: –
Na daya: – Manzon Allah (S.A.W)
ya fara bawa Sayyadina Abubakar
(R.A) da Sayyadina Umar (R.A)
tuta a ranar yakin Khaibara suka
kasa komai, suka gudu. Sannan
daga baya ya bawa Sayyadina Ali
(R.A) aka sami nasara.
Na biyu: – Fadin Manzon Allah
(S.A.W) ga Sayyadina Ali (R.A)
“Kai ne ni, ni ne kai” ya faru ne
lokacin da Manzon Allah (S.A.W)
ya hada kawance tsakanin
mutanen Madina da masu Hijira a
ranar yin Mubahala da Kiristocin
Najran.
Na uku: – Manzon Allah (S.A.W.) ya
hada kawance tsakaninsa da
Sayyadina Ali (R.A) bayan ya
gama hada kawance tsakanin
Sahabbai.
Dukkan wadannan kare-kare basu
inganta ba, kamar yadda malamai
suka tabbatar.
Daga dalilan da malamai suke
ambata a kan haka akwai: –
Na daya: – Ayar mubahala ta sauka
ne shekara ta tara da hijira,
Manzon Allah (S.A.W.) kuwa ya
hada kawance ne tun farkon
shigowarsa Madina.
Na biyu: – Manzon Allah (S.A.W)
bai hada kawance a tsakanin masu
hijira ba. Yana hada kawance ne
tsakanin masu hijira da mutanen
Madina, bisa zance mafi inganci.
Shi yasa Imamul Bukhari ya kulla
babi kai tsaye mai taken “Babin
hada kawance tsakanin masu hijira
da mutanen Madina”
Na uku: -Manzon Allah bai hada
kansa kawance da kowa ba, domin
shi shugaba ne na dukkan
al’umma.
Saboda haka maganar cewa
Manzon Allah (S.A.W) ya kama
hannun Sayyadina Ali (R.A) ya ce:
– “Ni wannan ne dan uwa na” ba ta
da asali.
Malamai suka ce Ibn Ishak ya
kawo wannan magana ne ba tare
da sanadi ba.
Na hudu: – Abin da ya tabbata shi
ne Manzon Allah ya hada kawance
ne tsakanin Sayyadina Ali (R.A) da
Sahal dan Hunaif (R.A.).
3) Fadin Manzon Allah (S.A.W) ga
Sayyadina Ali (R.A) yana son Allah
da ManzonSa suma kuma suna
sonsa
Wani yabo ne ga Sayyadina Ali
(R.A) dake nuna tabbacin
imaninsa. Amma ba yabo ne da
Sayyadina Ali (R.A) yakebanta da
shi ba.
Saboda Allah (S.W.T) ya fada a
gurare da dama a cikin Al-Kur’ani
cewa: – Yana son wasu mutane,
daga ciki akwai masu jihadi,
wadanda basa jin tsoron zargin
mai zargi.
Idan `Yan Shi’a, suka ce
Sayyadina Ali (R.A) ma ya shiga
cikin wadannan mutanen.
Sai mu ce, gaskiya ne Sayyadina
Ali (R.A) yana cikinsu.
Amma ba shi kadai ya kebantu da
soyayyar Allah da manzonSa ba, a
haduwar malamai.
Banda wannan ma, Manzon Allah
(S.A.W) ya fada cewa: – “Da zan
riki wani badadi ba Allah ba, to da
na riki Sayyadina Abubakar (R.A).”
Malamai kuwa sun tabbatar da
cewa badadi gaba yake da masoyi.
Kuma an tambayi Manzon Allah
(S.A.W) wa yafi so a duniya cikin
mazaje sai ya ce: “Sayyadina
Abubakar (R.A).” Da aka sake
tambayarsa, a cikin mata fa? sai ya
ce: “Nana Aisha (R.A).”
Idan wani ya ce: yaya za’a ce
Manzon Allah (S.A.W) ya fi son
Nana Aisha (R.A) bayan ga shi a
cikin Bukhari akwai Hadisin da ya
nuna cewa Manzon Allah (S.A.W)
ya fi son Nana Khadija.
Sai mu ce: – akwai maganganu
guda uku a kan wa ya fi wani,
tsakanin Nana Khadija da Nana
Aisha.
Amma masu ganin cewa, Nana
Khadija tana gaba da Nana Aisha,
suna bayar da amsa a kan Hadisin
da ya gabata da cewa, hukuncinsa
ya shafi matan da suke raye ne
kawai.
Kari a kan haka fadin cewa
Sayyadina Ali (R.A) zai shiga
karkashin masu jahadin da basa
jin zargin mai zargi, zai tabbatu ne
kawai a mahangar Ahlu Al-Sunna
da suke siffanta Sayyadina Ali
(R.A) da jarumta da rashin tsoron
kowa in ba Allah ba.
Amma a fahimtar `Yan Shi’a,
Sayyadina Ali (R.A) ba zai iya
shiga cikin fadin ma’anar ayar ba.
Domin su `Yan Shi’a suna siffanta
Sayyadina Ali (R.A) da cewa ya
rayu ne cikin tsoro, ta inda ya kasa
fadar gaskiyar abin da ya shafi
addini, ya kasa bayyana akidar
Shi’a, ya yi ta yin biyayya ga
Sayyadina Abubakar, Umar da
Usman (R.A), saboda tsoro da
ragwanci da gudun zargi da sunan
wani abu wai shi “Takiyya” wato
boye gaskiyar lamari da bayyanar
da karya.
Ita kuwa ayar cewa ta yi “Ya ku
wadanda ku ka bayar da gaskiya
hakika wanda duk ya bar addini
daga cikinku, da sannu Allah
(S.W.T) zai zo da wasu mutane,
yana son su, suma kuma suna son
sa, masu saukin hali tare da ‘yan
uwansu muminai, masu izza a kan
kafirai, za su dinga yin jihadi don
daukaka kalmar Allah, ba tare da
jin tsoron zargin-mai zargi ba”
3) Soyayyar Allah da ManzonSa ba
ta mayar da mutum ma’asumi, ko
halifan Manzon Allah (SAW).
Da kuwa haka lamarin yake, to da
duk wadanda Allah (S.W.T) ko
ManzonSa suke so, sun zama
Ma’asumai.
5) Maganar cewa Manzon Allah
(S.A.W.) ya bayar da tuta ga
Sayyadina Ali (R.A) ranar yakin
Khaibara da maganar cewa Allah
(S.W.T) ya bayar da nasara a
wannan yakin. Hakika wani abu ne
dake nuni da tsarkin zuciyar
Sayyadina Ali (R.A) da falalarsa da
jarumtarsa.
Amma hakan ba ya goyan bayan
akidun Shi’a, kuma ba ya mayar da
mutum ma’asumi.
Abin dake tabbatar da haka shi ne
Manzon Allah (S.A.W) ya bayar da
tutar yaki ga mutane daban daban,
kuma Allah (S.W.T) ya ba su
nasara.
Kamar yadda yake sanannen abu
ne cewa, Allah ya bude garuruwa
masu tarin yawa a lokacin
halifancin Sayyadina Abubakar,
Umar da Usman (R.A) karkashin
jagorancin manyan kwamandoji
irinsu Khalid Bn Walid, wadanda
ba su kai darajar Sayyadina Ali
(R.A) ba, a haduwar malamai.
Amma duk da wannan cikin
malaman Sunna, babu wanda ya yi
da’awar cewa wadannan manyan
Sahabbai Ma’asumai ne. Ko ya ce:
su kadai ne za su halifanci Manzon
Allah (S.A.W).
7) Fadin Manzon Allah (S.A.W) ga
Sayyadina Ali (R.A): “Kai ne ni, ni
ne kai” baya nuni da cewa
Sayyadina Ali (R.A) ma’asumi ne,
kuma shi kadai zai halifan ci
Manzon Allah (S.A.W), kamar
yadda ‘Yan Shi’a suke da’awa.
Saboda ya tabbata a cikin Hadisi
cewa, Manzon Allah (S.A.W) ya ga
wani Sahabi da ake kira da
Julaibib (R.A), a kwance bayan ya
yi shahada, a tsakanin gawarwakin
kafirai guda bakwai.
Sai Manzon Allah (S.A.W.) ya ce:
“Ya kashe mutane bakwai daga
baya aka kashe shi, kai ne ni, ni ne
kai” har sau uku. Kwatankwacin
abin da ya fada ga Sayyadina Ali
(RA).
Kamar yadda ya fadi irin wannan
maganar ga Abu Musa Al-Ash’ari
da mutanensa, lokacin da labarin
yadda suke taimakawa juna ya zo
masa.
Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce:
“Su ne ni, ni ne su”
8) A cikin kissar da `Yan Shi’a suke
ha kaitowa na yadda Manzon Allah
(S.A.W) ya hada kansa kawance
da Sayyadina Ali (R.A), an yi
amfani da lafazin alkunya wato –
Baban Hasan.
Sai wannan yake dada tabbatar da
abin da muka gabatar tun da farko
cewa, Manzon Allah (S.A.W) bai
hada kansa kawance da
Sayyadina Ali (R.A) ba. Abin dake
nuna haka shi ne a lokacin da
Manzon Allah (S.A.W) ya hada
kawance a Madina, Sayyadina Ali
(R.A) bai auri Nana Fadima (R.A)
ba.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

4 responses to “DARASI NA GOMA SHA HUDU (14)SHUBUHOHIN SHI’A A KAN FADIN MANZON ALLAH (SAW) GA SAYYADINA ALI (RA) “KAI NE NI, NI NE KAI” DA BAIWA SAYYADINA ALI TUTA RANAR YAKIN KHAIBARA(Mal.Aminu Ibrahim Daurawa)”
  1. Abubakar Usman Avatar
    Abubakar Usman

    Allah saka Mallam

  2. Muhd sadi ibrahim Avatar
    Muhd sadi ibrahim

    Masha Allah

  3. ZILKIFIL DANGAWO JEGA Avatar
    ZILKIFIL DANGAWO JEGA

    Limatukuluna malatabbf aluu

Leave a Reply

Categories
Latest updates