Shimfida- “ Qasa zata amayo guntattakin abin cikinta na zinari da azurfa, manya manya kaman ginshikai – sai wanda yayi kisa yace a saboda wannan ne na yi kisa; sai wanda ya yanke zumunci shima ya ce a saboda wannan ne ya yanke zumunci; sai wanda yayi sata ya zo yace akan wannan ne aka yanke hannun shi. Sannan su bar wannan dukiyan duka ba mai ta6a komai a cikinta”.
Tambayoyi dake ciki:
- Ya hallata mutum ya ci danyen kifi?
- Nasiha ga wadda take son ta yi sallah amma bata iya yin sallar.
- Wai da gaske ne ba Nana ‘A’isha (RA) akai yi wa qazafin zina ba?
- Wanda ya taba laifi ya tuba, zai iya rantsuwa ma wanda su ke cigaba da żargin shi akan wannan laifin?
- Hukuncin wanda yayi bakance in Allah ya biya mishi wata buqatar shi zai gabatar da wani aikin alkhairi, bai aikata aikin alkhairin ba saboda buqatar bata samu ba!
- Sahihancin samu ko rashi – jarabawa ce daga Allah.
- Hukuncin wadda ta sha azumi saboda ciki da shayarwa, ta kasa ramawa saboda rashin lafiyar ulcer- za ta ciyar a kowanni lokaci ko sai watan axumin ya tsaya, ko ciyarwar ta fadi?
- Shin bismilla ko sallama mutum zai yi idan zai aika saqon wasiqa ko text?
- Yadda za a fitar da zakkar kudin da mutum ya samu ta sana’ar hannu da kudin da ya samu na balance din a daidaita sahu!
- Hukuncin kudin da aka ba ma ma’aikacin gwamnati saboda amfani da qwarewarsa a samu wata takarda ko amfani -kamar driver’s licence.
- Ya hallata amfani da mushafin al-qur’ani a shirin film?
- Hallacin sayayya a ranar black friday?
- Mutumin da ya je hajji bai yi aski ba yana da laifi?
- Gwargwadon abinda mace zata cire a gashinta ya zama tayi aski karbabbe ma hajjinta.
- Ya hallata mamu ya dauki al-qur’ani lokacin sallar tahajjud ko tarawih?
- Matsayin masu fadin “ Bala wa nahnu ala dhalika mina shahidin” a qarshen suratut Tin.
- Hukuncin wanda ya gina gidan kallon bal domin sana’a.
- Hukuncin “hire purchase”
- Hukuncin yin salati a sallar farilla?
- Shin miji zai iya zuwa ma kowacce matanshi ya ga dama duk lokacin da ya so, ba tare da la’akari da rabon kwana ba saboda fadin Allah (SWT) “ matayenku gonaki ne a gare ku, don haka ku je wa gonakinku ta inda kuka so…”
Download
Leave a Reply