Lahadi 9/6/1444 – 1/1/2023
Tambayoyi da Amsoshi tare da Dr. Muhammad Sani Umar R/Lemo, OON
- Menene ingancin cewa ba a yin Sallar nafila bayan Sallar Ƙasaru?
- Hukuncin karɓar ‘overtime’ ba tare da yin aiki da ake biyar wannan ‘overtime saboda da ya yi aikin overtime a zamanin baya amma ba a yi shi ba!
- Iyaye za su taimaka wa ‘yar su a gidan aure ko da mijinta yana ƙin haka?
- Wanda ya yi Bakancen zai yi azumin kwana uku a kowanni wata in sun fado a ranar Litinin da Alhamis , in azumin kwana uku ba su fado a ranar Litinin ko Alhamis yaya zai yi?
- Wanda ya yi bakancen zai yi Azumin Annabi Dawuda (AS) zai iya hutu na wani lokaci? Ko kuma in ya yi tafiya?
- Akwai amfani mutum ya yi sammakon zuwa massalacin Jumu’a a in da ake huɗuba da yaren da ba ya fahimta?
- Wanda ya yi salla a gida zai iya samun ladan jam’i in zuwa massalaci yana wahalar da shi saboda nisa?
- Wanda ya tafi karatu zai iya ƙasaru har ya gama karatu?
- Hukuncin ba da kwangila ga matar shugaba!
- Ya hallata yin sujjada akan naɗin rawani ko ɓangare na hula a lokacin sanyi ko tsananin zafi!
- Yaya mutum zai tsayar da yatsa ya yin Tahiya?
- Hukuncin cin abincin da Kirista ya dafa!
- In mace ta ba wani dama ya aureta sai bai samu hali ba, shin ta na da laifi in ta aure wani da ya shirya?
- Mutum zai iya ƙin taimakawa Mahaifinsa da ba ya kyautata wa Mahaifiyarsa?
- Hukuncin wanda ya siyya wa abokinsa giya ba da sani ba!
- Ya inganta Allah yana biya wa wasu musulmi bashi ranar Alƙiyama?
- Ƙarin haske akan hadisin kowanne abin Haihuwa ana haifar sa ne akan fiɗira
- Shin wanda yake gadi a wata ma’aikata wasu suke zuwa suna rashin gaskiya zai iya karɓar kuɗi da ake ba shi in an zo ɗaukan kaya?
- Mutum zai iya zuwa Sallah Massalaci da ke nesa da in da yake saboda massalacin da ke kusa suna karanta Alƙunut duk sallar Asuba!
- Mutum zai iya Siyan Alƙur’ani ya bayar sadaƙa jariya ga mahaifiyar sa?
- Ya ya mutun zai cigaba da biyyaya ga Mahaifiyarsa da ta rasu alhali bai kyautata mata a lokacin da ta ke raye ba?
- Wadda mahaifiyar sa ta rasu ake zargin kashe ta aka yi, zai iya bincike ya gano gaskiyar abin da ya faru?
- Ya hallata mutum ya koyi Al-ƙur’ani ta hanyar sauraro kadai?
Download
Leave a Reply