Fatawoyin Rahama By Dr. Sani Umar Rijiyar Lemo 6th August 2023

Danna nan domin shiga karatu Online

  1. Wanda yake Nigeria zai iya biyan wanda yake ƙasar Saudiya ya yi masa Úmara?
  2. Musulmi zai iya rufa asirin wani musulmi da yake cutar wani?
  3. Bayan Alƙali ya raba aure Mace sai ta sake wani auren, in wannan Auren Ya mutu za ta iya komawa ta auri mijinta na farko da Alƙali ya raba aure?
  4. Mace mai takaba za ta iya cigaba da kasuwancin ta?
  5. Yaya mutum zai magance matsalar damuwa da kuncin rayuwa!
  6. Menene ingancin Hadisin da yake cewa in mutum ya sauke Al-ƙur’ani Mala’iku dubu saba’in za su yi masa addua!
  7. Ya hallata mutum ya ce zai siyi Al-ƙur’ani (Mushaf) maimakon ya ce zai fansa?
  8. Idan mutum yayi cinikin fili bashi, zai iya siyarwa wani saboda wanda aka siyarwa da farko bai biya ba?
  9. Ya hallata mahaifiya ta cinye gadon ‘ya’yanta?
  10. Mace za ta iya rage gashin kanta ba tare da yin azumi ba?
  11. Menene matsayin karanta sunayen Ashabul Kahfi lokacin addu’a
  12. Ya tabbata Annabi ﷺ yana karanta ‘Subhanal Malikil Ƙuddus Rabbil Mala’ikati Wa Ruh’ bayan Sallar Wutri?
  13. Ya inganta in Annabi ﷺ ya gama Sallar Asuba da Magriba baya tashi daga wajen da yayi Sallah har sai ya karanta ‘ La’ilaha Illa lahu Wahdahu La sharika Lah, Lahul Mulku Wa Lahul Hamdu, Yuhyi Wa Yumitu Wa Huwa Àla Kulli Shai’n Qadir”
  14. Ya hallata mata da ruwan sama ya tare su a massalacin makaranta su haɗa Sallah?
  15. Mutum zai iya zagin shugaba da ya zalince shi saboda dogara da faɗin Allah لَّا يُحِبُّ ٱللَّهُ ٱلْجَهْرَ بِٱلسُّوٓءِ مِنَ ٱلْقَوْلِ إِلَّا مَن ظُلِمَ وَكَانَ ٱللَّهُ سَمِيعًا عَلِيمًا
  16. Ya hallata mutum ya siyi Kayan da ake gwanjon su a maka’itar da yake aiki (watau auction) a bisa tsarin sai ma’aikaci ya biya kuɗin ‘form’ kafin ya shiga jerin masu sayarwa!
  17. Ya hallata mutum ya ba da rance kuɗin Buhun Siminti goma da sharaɗin in an zo biya a biya shi da kuɗin buhun Siminti goma ko da kuɗin Siminti ya tashi lokacin biya.
  18. Hukuncin Rina Gemu da lalle!
  19. Hukuncin limanin da yake sallama kafin Mamu su kammala tahiya!
  20. Mai Ladan zai ce in yana kiran Sallah lokacin da ake ruwan sama!
  21. Mai sana’a zai iya karbar kayan ajiyar da yayi wa waɗanda ba su zo karɓar kayansu ba!
  22. Mutum zai iya ƙudurce ya yafe bashin da yake bin wani?
  23. Jidda Miƙati ce?
  24. Uban adashe zai iya karɓar kuɗin cajin da Banki ya ke dai masa!

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates