HARAMUN NE MUSULMI YA WUCE GONA DA IRI GAME DA ZATIN MANZON ALLAH MAI TSIRA DA AMINCIN ALLAH
Imamul Bukhaarii ya ruwaito hadithi na 3,445, da Imamu Muslim hadithi na 1,691 cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce:-
((لا تطروني كما أطرت النصارى ابن مريم انما انا عبد فقولوا: عبد الله ورسوله)). انتهى.
Ma’ana: ((kada ku wuce gona da iri cikin yabona, kamar yadda Kirista suka wuce gona da iri cikin yabon Dan Maryam, ni ba kowa ba ne face bawa, ku ce: bawan Allah kuma manzonSa)). Intaha.
‘Yan’uwa Musulmi! Ga shi dai kun ji da kunnuwanku cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya hana al’ummarsa wuce iyakar Sahari’ah cikin yabonsa, ma’ana su yi wata karya game da shi da nufin yabo, to amma kuma abin bakin ciki da mamaki sai ga shi an samu wasu nau’in ‘yan bidi’ah da suka bijire wa wannan hani nasa suka wuf suka fada cikin wannan musiba ta guluwwi !!
Misali: ya zo cikin babban littafin ‘Yan Darikar Tijjaniyyah mai suna Jawaahirul Ma’anii 1/147 kamar haka:-
((اول ما خلق الله تعالى روح محمد صلى الله عليه وسلم ثم نسل الله منها أرواح الكائنات ثم كون الله من جسد النبي صلى الله عليه وسلم أجساد الملائكة والأنبياء والأقطاب)). انتهى.
Ma’ana: ((Farkon abin da Allah Ya halitta shi ne ran Muhammad mai tsira da amincin Allah, sannan ya halitta sauran rayukan halittu daga shi (wannan ran) sannan kuma Allah Ya halicci jikkunan Mala’iku da Annabawa da Manyan waliyyai daga jikin Annabi Mai tsira da amincin Allah))!!! Intaha.
‘Yan’uwa Musulmi masu girmama Allah da Shari’ar da ya aiko ManzonSa da ita! Don Allah ku dubi abin da suka rubuta a nan na tabbatar da cewa: wai da Annabi Adamu da kuma Mala’iku da sauran halittu dukkansu zurriya ce daga Annabi Muhammad, duk kuwa da cewa ijama’in dukkan Musulmin kwarai ya kullu a kan cewa Annabi Muhammad yana daga cikin zurriyyar Annabi Adam ne ba wai shi Annabi Adam din ba ne yake daga cikin zurriyyar Annabi Muhammad mai tsira da amincin Allah ba, saboda Allah Madaukakin Sarki Ya ce cikin Suratul Hijri aya ta 28-29 :-
((وإذ قال ربك للملائكة اني خالق بشرا من صلصال من حما مسنون. فإذا سويته ونفخت فيه من روحي فقعوا له ساجدين)). انتهى.
Ma’ana: ((A lokacin da Ubangijinka Ya ce wa Mala’iku lalle ne ni Mai halittan wani dan adam ne daga wani irin laka busashshe, daga wani irin bakin tabo jirkitacce, to idan na daidaita shi, kuma na busa raiNa cikin shi, to sai ku fadi kuna masu yi masa sujjada)). Intaha.
Sannan kuma Ya ce cikin suratus Sajdah aya ta 7-8 :-
((الذي أحسن كل شيء خلقه وبدا خلق الانسان من طين. ثم جعل نسله من سلالة من ماء مهين)).
Ma’ana: ((Shi ne wannan da Ya kyautata dukkan kome da Ya halitta shi, sannan Ya fara halittar jinsin mutum ne da laka, daga nan Ya yi zurriyyarsa daga wani irin daskararren jini da kuma wani irin ruwa kaskantacce)). Intaha.
‘Yan’uwa Musulmi! Wannan shi ne abin da Allah Ya gaya mana a cikin Alkur’ani Mai girma, kuma jinsin mutum da ake nufi a cikin wadannan ayoyin shi ne Annabi Adam alaihis salam, ba wai Annabi Muhammad mai tsira da amincin Allah ba.
Muna fata masu bin Darikar Tijjaniyyah za su yi tunani mai zurfi, su gauggauta tuba zuwa ga Ubangijinsu, su kyautata Musuluncinsu, su yi watsi da irin wadannan akidu na ilhadi, su dawo su yi Musulunci irin wanda Annabi sa sahabbansa da kuma tabi’ansu suka yi.
Babu abin da muke nufi sai gyara iya iyawarmu, kuma Allah Shi ne madogararmu, muna kuma fata Ya taimake mu Ya nuna mana gaskiya gaskiya ce Ya ba mu ikon bin ta, Ya kuma nuna mana karya karya ce Ya ba mu ikon guje mata.
Leave a Reply