Huduba Jum'ah Daga Masallacin Abu Huraira (RA), Sokoto A Kan Alfarmar Jinin Musulmi 16 J. Akhir 1434H (26/4/2013M)(Dr. Mansur Sakkwato)

·

·

– musulunci addinin rahama ne ga
bayin Allah duka ba ‘yan adam
kawai ba.
– Manzon Allah (SAW) rahama ne
ga talikai
– Ibn Umar (RA) da yaron gidan
Yahya bin Sa’id mai wasa da kaza.
– Allah ya azabta wata mata a kan
mage Bukhari (3407) da Muslim
(5804).
– Allah ya gafarta ma wata karuwa
a kan ta tausaya ma kare. Sahihul
Bukhari (3251) da Sahihu Muslim
(5812).
– Tun daga samun ciki shari’a ta
sanya dokoki masu bada kariya ga
lafiya da rayuwar dan Adam da
uwar da za ta haife shi. (Shan
azumi, jinkirin haddi, hukuncin
zubar da ciki dss)
– musulunci ya ceci kananan ‘yan
mata a jahiliyyar larabawa.
– hudubar bankwana : “Ko kun san
wace rana ce muke yau?” … “Ya
Allah, ka sheda. Ku kuma duk
wanda ya zo ya fada ma wanda bai
zo ba. Kuma kada ku yarda ku
zama kafirai a bayana; kuna sarar
wuyan junanku”.
– Ibnu Abbas daga Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wa Alihi
Wasallam “Wannan daki akwai
daraja a gare ka da alfarma.
Amma babu shakka darajar
mummuni ta fi taka a wurin Allah”.
Albani ya kawo ta a cikin Silsila
Sahiha.
– A hadisin Tirmidhi (1393) wanda
Abdullahi dan Amru Radiyallahu
Anhuma ya ruwaito kuma Ibnu
Majah ya ruwaito shi (2689) daga
Bara’u dan Azib Radiyallahu Anhu,
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa
Alihi Wasallam cewa ya yi: “Wallahi
gara gushewar duniya a wurin
Allah bisa ga a kashe ran
mummuni ba da wani alhaki da ya
dauka ba. Kuma in da mutanen
sama da na kasa sun hadu a kan
kashe mutum daya duk sai Allah
ya jefa su wuta”. Sahihut Targib
Wat Tarhib (2438).
– Usama bin Zaid: “To, yanzu ya
zaka yi da La ilaha illallahu idan ta
zo ta yi ma sa hujja a ranar
alkiyama?!”
Saboda kai matuka ga hana yin
kisa addinin musulunci ya hana ko
nunin mutum ayi da makami:
(( ﻣﻦ ﺃﺷﺎﺭ ﺇﻟﻰ ﺃﺧﻴﻪ ﺑﺤﺪﻳﺪﺓ ﻓﺈﻥ ﺍﻟﻤﻼﺋﻜﺔ ﺗﻠﻌﻨﻪ
ﺣﺘﻰ ﻳﻨﺘﻬﻲ، ﻭﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﺃﺧﺎﻩ ﻷﻣﻪ ﻭﺃﺑﻴﻪ((، ﻭﻓﻲ
ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﺍﻵﺧﺮ)) : ﻣﻦ ﺃﺧﺎﻑ ﻣﺆﻣﻨﺎ ﻛﺎﻥ ﺣﻘﺎ ﻋﻠﻰ
ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻥ ﻻ ﻳﺆﻣﻨﻪ ﻣﻦ ﺃﻓﺰﺍﻉ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻘﻴﺎﻣﺔ)).
– Babu wani laifi da ke sa shamaki
tsakanin mutum da rahamar Allah
kamar zubar da jinin musulmi.
Bukhari ya ruwaito hadisi (6409)
daga Ibnu Umar ya ce, Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi
Wasallam ya ce: “Mumini ba zai
gushe ba yana da wata safa ta
samun sauki a addininsa matukar
dai bai zubar da jinin da aka
haramta ma sa ba”.
– A wani hadisin na Bukhari (6729)
Sallallahu Alaihi Wa Alihi
Wasallam ya sake cewa: “Mutane
uku ba wanda Allah ke kyama
kamar su:
1. Mai ilhadi a cikin harami
2. Mai shigo da dabi’un jahiliyyah a
cikin musulunci
3. Mai neman jinin wani mutum
don ya zubar da shi babu gaira
babu dalili”.
Don haka, kisan musulmi na daga
cikin abubuwa guda bakwai da
manzonmu Sallallahu Alaihi Wa
Alihi Wasallam ya fada mana
cewa, suna halaka mutum; su kai
shi su baro su hana shi samun
tsira. Wadannan abubuwa Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi
Wasallam ya jeranta su kamar
haka: 1. Shirka 2. Sihiri ko bokanci
3. Kisan ran da Allah ya haramta 4.
Cin kudin riba 5. Cin dukiyar
maraya 6. Gudu daga fagen jihadi
7. Yin kazafi ga mata musulmi
wadanda ba su san hawa ba ba su
san sauka ba. Wannan hadisi yana
a cikin Bukhari (2707). Shi ya sa a
kullum muke ganin Allah Ta’ala
yana hada kisan kai da shirka cikin
alkur’ani. Suratul Furkan: 68-71.
– Abud darda’i daga Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wa Alihi
Wasallam: “Ana sa ran samun
gafarar Allah ga kowane zunubi
banda in mutum ya mutu kafiri ko
ya kashe dan uwansa musulmi da
gangan”. Sunan Abi Dawud (4270)
, Silsila Sahiha (511).
Sayyidina Mu’awiyah Radiyallahu
Anhu ya kasance yana fadin
wannan hadisi a kan mimbari. As
Sunan Al Kubra na Nasa’i (3446).
wadannan laifukan guda biyu babu
wadanda shedan yake ba lambar
yabo kamar ma su yin su. «Kullum
aka wayi gari shaidan ya kan
rarraba rundunarsa don su taya shi
aiki. Ya kan ce ma su duk wanda
ya tozarta musulmi a yau zan sa
ma sa kanben girma. Sai wani ya
zo ya ce, na yi ta kokari sai da na
hada husuma tsakanin sa da
matarsa har ya sake ta. Sai
Shedan ya ce ma sa, to, ai gobe in
ya huce zai ce ya mayar da ita.
Wani kuma ya ce, to, ni na hada
shi fada da iyayensa. Sai Shedan
ya ce, to ai gobe za su shirya.
Wani kuma zai zo sai ya ce, ni kam
shirka na sa shi ya yi. Sai Iblisu ya
ce, Ahah! Ahah!!. Sai wani ya ce,
na sa ya kashe dan uwansa. Sai
ya ce, madallah! Ga wanda za mu
ba kanben girma. Al Imam Al
Mundhiri ya kawo shi cikin At
Targib Wat tarhib. Duba Sahihinsa
(2449). Mu saurari yadda Allah
Tabaraka Wa Ta’ala ya fadi
hukuncin kashe musulmi cikin
alkur’ani. Suratun Nisa’i: 92-93.
(( ﻭﻣﻦ ﻳﻘﺘﻞ ﻣﺆﻣﻨﺎ ((..
..)) ﺃﻧﻪ ﻣﻦ ﻗﺘﻞ ﻧﻔﺴﺎ ﺑﻐﻴﺮ ﺃﻭ ﻓﺴﺎﺩ ﻓﻲ ﺍﻷﺭﺽ ..))
Abinda muka sani ne cewa, kome
yawan ladar musulmi ranar
alkiyama, ba zai gushe ba in ya
zalunci wasu bayin Allah sai an
rinka dibar ladarsa ana ba su. To,
idan aka yi daidai da cewa ya
kashe musulmi babu gaira babu
dalili to, wannan kam karyarsa ta
kare gaba daya.
– Qabila da Habila. Suratul Ma’ida:
27-32.
(( ﻭﺍﺗﻞ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﻧﺒﺄ ﺍﺑﻨﻲ ﺁﺩﻡ ﺑﺎﻟﺤﻖ.. ﺇﻧﻲ ﺃﺭﻳﺪ ﺃﻥ
ﺗﺒﻮﻭﺃ ﺑﺈﺛﻤﻲ ﻭﺇﺛﻤﻚ..))
– Nasa’i (4008), Silsila Sahiha
(2698) daga Abdullahi dan Mas’ud
(RA): “Mutum zai zo rike da
hannun wani mutum a gaban
Allah, sai ya ce, ya ubangiji!
Wannan shi ya kashe ni. Sai Allah
ya ce ma sa, don me ka kashe shi?
Sai ya ce, don girma ya zama
naka. Sai Allah ya ce, lalle ko
girma yana gare ni. Wani kuma ya
zo ya tungumo wani, sai ya ce, ya
ubangiji! Wannan shi ne ya kashe
ni. Sai Allah ya ce ma sa, don me
ka kashe shi? Sai ya ce, don girma
ya zama na wane. Sai Allah ya ce,
to wane ba shi da girma. Sai ya
kwashe ma sa zunubbansa”.
– A ranar alqiyama jinainai ake fara
hukunci a kan su.
– A shari’a ba a rarraba laifin kisan
kai, sai dai duk a shigar da
wadanda suka yi tarayya a cikin sa
cikin wuta.
– A cikin Mu’ujam na Dabarani,
wani ya tafi wurin Ibnu Abbas yana
fatawa, ko wanda ya yi kisan kai
zai iya tuba? Sai Ibnu Abbas ya ce
ma sa – yana mai mamaki – me ka
ce ? ya rinka sa yana maimaita ma
sa tambayar har sau ukku, sannan
ya ce na ji annabinku Sallallahu
Alaihi Wa Alihi Wasallam yana
cewa : «wanda aka kashe zai zo
ranar alkiyama da hannunsa
rataye ga wuyansa, a daya
hannunsa kuma ya kamo wanda
ya kashe shi duk jijiyoyinsa suna
furzo da jini har ya zo gaban
al’arshi da shi. Sai ya ce, ya
ubangiji! Wannan fa shi ne ya
kashe ni. Sai Allah madaukakin
sarki ya ce ma wanda ya yi kisa: «
Ka halaka ». Sannan ya sa aje da
shi a wurga shi cikin wuta». Silsila
Sahiha (2697).
Ya ku Al’ummar musulmi!
Babu shakka abin da ya faru a
wannan sati a garin “Baga” na jihar
Borno abin takaici ne mai kona
zuciya.
A ko ina ka je a duniya gwamnati
tana kokarin kare jinin dan kasarta
ne. Jami’an tsaro a ko ina kokarin
suke yi su ga an hana zubar da
jinin dan kasa. Amma mu a nan
kamar ana jiran dama ta samu ne
a far ma wadanda ba su ji ba ba su
gani ba.
Kafafen yada labarai sun ruwaito
cewa an rusa gidajen musulmi
sama da 200. An kona babbar
kasuwar kifi da musulmi suke ji da
ita a yankin. Akalla an tabbatar da
an yi jana’izar mutane 185 a lokaci
guda. An nuno hotunan
gawawwakin wadanda aka yi ma
kisan rashin imani kuma aka
kokkona su abin babu dadin kallo.
Muna juyayin wannan lamari a
cikin jin haushi da rashin tabbas na
cewa, shin ina abin zai tsaya?!
Jihar Borno kadai ake nufi da
wannan lamari kuwa ko akwai
wata ajenda a boye ta wargaza
duk yankunan musulmi a wannan
kasa?!
– Rahotannin da muka samu sun
nuna wurare da yawa ana zaman
xar xar a jihar Borno kuma ana
kashe mutane da Allah kadai ya
san adadinsu a yankuna da dama.
Ba jihar Borno kawai ba. A
shekaranjiya an yi ta barin wuta ga
jama’a a Gashua ta jihar Yobe.
Jiya an yi makamancin haka a
garin Mayobelwa ta jihar
Adamawa.
MEND a kwanakin baya ta ce zata
fara kai hari ga masallatai da
makarantu da camps din alhazai.
Mene ne matsayin CAN a kan
wannan furuci na ta’addanci?Mene
ne matsayin ita kanta gwamnatin
tarayya a kan wannan ta’addanci?
Mu kwatanta martanin da
shugaban Amirka Obama ya maida
bayan harin Boston a satin da ya
wuce. Me zamu fahimta? A ko ina
duniya ta’addanci abin kyama ne,
amma mu a nan Nigeria in ya shafi
yan Arewa/Musulmi to maraba da
shi ake yi.
Wane irin tunani manyanmu suke
da shi game da makomarmu da ta
‘ya’yanmu a wannan kasa?
Muna jajanta ma al’ummar
musulmi da duk ‘yan Najeriya
masu kishin kasa, masu son
zaman lafiya bisa ga faruwar
wannan al’amari. Wadanda suka
mu riga mu gidan gaskiya a cikin
wannan fitina muna rokon Allah ya
yi mu su gafara. Wadanda suka
tagayyara Allah ya ba su lafiya.
Zuriyar da aka bari Allah ya jibince
su.
Ya Allah! Ka yi ma na maganin duk
bala’in da ba mu iya magance ma
kanmu. Madaukakin sarki ka isar
mana ga duk masu nufin mu da
sharri, masu son rikita mana kasa.
Ya Allah ka tona asirinsu, ka lalata
dibararsu, ka watse taronsu, ka
tarwatsa shirinsu.
‘Yan uwa musulmi, abin yana da
daure kai wallahi. Ya za a yi jinin
dan Adam ya koma kamar na
kiyashi?!
Ya ku shugabanni! Ku tuna cewa,
rayuwar talakawa amana ce a
wuyanku. Kuma Allah zai tambaye
ku. Wajibi ne a dauki dukkan
matakan tsaro da kariya ga
rayuwar jama’a. Kuma duk lokacin
da irin haka ta faru wajibi ne a
dauki dukkan matakai na bincike a
gano masu laifi a kuma hukunta su
tsakani da Allah.
Muna kira ga kungiyoyin kare
hakken ‘yan Adam masu zaman
kansu da su bibiyi wannan lamari
su ji daga bakin wadanda Allah ya
tserar da su kuma wadanda suka
shedi abin da ya faru da idanunsu.
Sannan a shigar da karar duk
wadanda aka tabbata suna da
hannu a ciki ga kotunan da suka
dace.
Ya Allah! Kada ka bi mu da
miyagun halayenmu da munanan
ayyukanmu. Ya Allah! Ka jibintar
da al’amarinmu ga masu tsoron ka.
Ka yaye mana bakkan ciki, ka
kuranye mana matsaloli, ka dora
mu a kan dibarar da zata amfane
mu. Allah ka taimaki duk masu
taimakon addininka ta ko wace
hanya. Duk wadanda ke shirya ma
musulmi makarkashiya Allah ka fi
su dabara. Allah ka wargaza
anniyarsu, ka xaixaita al’amarinsu,
ka sanya husuma a tsakanin su, ka
kare musulunci da musulmi daga
sharrinsu.
ﺃﻻ ﻓﺎﺗﻘﻮﺍ ﺍﻟﻠﻪ، ﻭﺍﺣﺬﺭﻭﺍ ﻣﻦ ﻏﻀﺒﻪ ﻭﺳﺨﻄﻪ، ﻭﻻ
ﻳﻨﺰﻏﻨﻜﻢ ﺍﻟﺸﻴﻄﺎﻥ ﻭﺍﻋﺼﻮﺍ ﺃﻣﺮﻩ، ﻭﺇﻣﺎ ﻳﻨﺰﻏﻨﻚ
ﻣﻦ ﺍﻟﺸﻴﻄﺎﻥ ﻧﺰﻍ ﻓﺎﺳﺘﻌﺬ ﺑﺎﻟﻠﻪ .
ﻫﺬﺍ ﻭﺻﻠﻮﺍ ﻭﺳﻠﻤﻮﺍ ﻋﻠﻰ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻣﺘﺜﺎﻻ ﻷﻣﺮ
ﺍﻟﻠﻪ، ﺣﻴﺚ ﺃﻣﺮﻛﻢ ﺑﺬﻟﻚ ﻓﻘﺎﻝ ﺟﻞ ﻣﻦ ﻗﺎﺋﻞ ﻋﻠﻴﻤﺎ :
ﺇﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻣﻼﺋﻜﺘﻪ ﻳﺼﻠﻮﻥ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﻳﺎ ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﺬﻳﻦ
ﺁﻣﻨﻮﺍ ﺻﻠﻮﺍ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻤﻮﺍ ﺗﺴﻠﻴﻤﺎ ]ﺍﻷﺣﺰﺍﺏ .[56:
ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺻﻞ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﺑﺎﺭﻙ ﻋﻠﻰ ﻧﺒﻴﻨﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﺻﺎﺣﺐ
ﺍﻟﺤﻮﺽ ﻭﺍﻟﺸﻔﺎﻋﺔ، ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ، ﻭﺍﺭﺽ
ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻋﻦ ﺧﻠﻔﺎﺋﻪ ﺃﺑﻲ ﺑﻜﺮ ﻭﻋﻤﺮ ﻭﻋﺜﻤﺎﻥ ﻭﻋﻠﻲ،
ﻭﻋﻨﺎ ﻣﻌﻬﻢ ﺑﻌﻔﻮﻙ ﻭﺟﻮﺩﻙ ﻳﺎ ﺃﻛﺮﻡ ﺍﻷﻛﺮﻣﻴﻦ .
ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺃﻋﺰ ﺍﻹﺳﻼﻡ ﻭﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ، ﻭﺍﻧﺼﺮ ﺇﺧﻮﺍﻧﻨﺎ
ﺍﻟﻤﻀﻄﻬﺪﻳﻦ ﻓﻲ ﻓﻠﺴﻄﻴﻦ ﻭﻓﻲ ﻛﻞ ﻣﻜﺎﻥ، ﻭﻛﻦ ﻟﻬﻢ
ﻧﺎﺻﺮﺍ ﻭﻣﻌﻴﻨﺎ، ﻭﺍﻧﺼﺮﻫﻢ ﻋﻠﻰ ﺃﻋﺪﺍﺋﻬﻢ ﺍﻟﻈﺎﻟﻤﻴﻦ
ﺍﻟﻴﻬﻮﺩ ﺍﻟﻤﻌﺘﺪﻳﻦ…
ﺭﺑﻨﺎ ﺗﻘﺒﻞ ﻣﻨﺎ .. ﺭﺑﻨﺎ ﺁﺗﻨﺎ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ..
ﻋﺒﺎﺩ ﺍﻟﻠﻪ، ﺇﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﺄﻣﺮ ﺑﺎﻟﻌﺪﻝ ﻭﺍﻹﺣﺴﺎﻥ..

One response to “Huduba Jum'ah Daga Masallacin Abu Huraira (RA), Sokoto A Kan Alfarmar Jinin Musulmi 16 J. Akhir 1434H (26/4/2013M)(Dr. Mansur Sakkwato)”
  1. nasirudden abdulhameed Avatar
    nasirudden abdulhameed

    ya ~Allah ka karama malam basira Amin

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: