Tambaya: Shin ya halatta matafiyi yayi sallar Nafila akan abin hawa? Kaman Mota, ko jirgin Sama?
Amsa: ya halatta matafiyi yayi sallar nafila in yana cikin abin hawa, koda ko baya fuskantar Alqibla.
Dalili: Ibn Umar Allah ya kara masa yarda yace:
Annabi Sallallahu alaihi wasallama ya kasance yana sallatan sallolinsa na farilla duk ta yadda rakumarsa ta fuskanta
Bukhari: 1105
Muslim: 700
Wannan hadisi karara yana nuna cewa Annabi yana Sallar nafila kan abin hawansa, sannan duk yadda ta fuskanta yana yi ba dole sai tana fuskantar Alqibla ba.
Ta yaya za’ayi Ruku’i da Sujada?
Idan mutum zaiyi sallah akan abin hawa toh zai rinka yin Ima’i ne(Nuni) da gabobinsa, Zai karkata yayin ruku’i hakanan yayi sujada, amma ta sujada zata fi ta ruku’i.
Dalili: An rawaito daga ibn Umar Allah ya kara musu yarda yace:
Annabi Ya kasance yana sallah a yayin tafiya akan aban hawansa, duk yadda ta karkata dashi, ya kasance yana Ima’i(Nuni).
Bukhari: 1000
Muslim: 700
Allah shine mafi sani
Leave a Reply