HUKUNCE-HUKUNCEN AIKIN HAJJI DA UMRA Darasi na 6(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

Danna nan domin shiga karatu Online

HUKUNCE-HUKUNCEN AIKIN
HAJJI DA UMRA
Darasi na 6
SIFFAR YADDA AKE YIN UMRA
DA KUMA SUNNONIN IHIRAMI:
A baya an ji cewa aikin hajji nau‘i
uku ne:
Hajji a hade da umra (kirani).
Hajji da umra a rabe (tamattu‘i).
Hajji ita kadai (ifradi).
A yanzu za muyi darasi akan aikin
umra kafin mu shiga yadda ake
hade ta da hajji ko a raba su.
SIFFAR AIKIN UMRA A TAKAICE
. Mutun yayi harama a mikati.
. Sannan ya tafi yana talbiya har ya
isa Ka‘aba, sai yayi dawafi sau
bakwai.
. Sai yayi sallah raka‘a biyu a
Makama Ibarahim.
. Sai yayi sa‘ayi 7 a tsakanin safa
da marwa.
. Sai yayi saisaye, idan kuma mace
ce sai ta yanke gwargwadon gabar
dan yatsa a karshen gashin ta.
Idan mutun ya yi haka ya kammala
umra.
Akwai karin bayani akan kowace
gaba, kuma akwai abubuwa da
aka haramta, don haka za mu
gabatar da bayani akansu daya
bayan daya.
HARAMA;
Shine yin harama da kulla niyyar
fara umra ko hajji.
Sunnoni da abubuwan da ake so a
ihirami sune:
1-Ana so mutun ya yanke farce, ya
aske gashin gaba da na hammata
kafin ihirami don kar ya bukaci
hakan bayan ihirami.
2- Ana so mutun yayi wanka kafin
ya dau harama.
3- Ana so mutun ya shafe jikin sa
da turare kafin ihirami domin bai
halatta ya shafa turare ba bayan
ihirami. Kuma bai halatta ya shafa
a jikin ihiraminsa ba.
4- Ana so ihirami ya zama bayan
sallar farilla ko nafila. Amma idan
mutun ya zo mikati a lokacin da ba
a sallar nafila ba sai ya jira lokacin
yin nafila ko farilla ba. Sai yayi
haramarsa a haka.
5- Tun da dai umara muke
magana, sai mai umra yace:
ﻟﺒﻴﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻋﻤﺮﺓ
idan kuma hajji ce kirani sai ya ce:
ﻟﺒﻴﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻋﻤﺮﺓ ﻭﺣﺠﺎ.
6- Sai mutun ya tafi yana talbiya
har yaje yayi dawafi.
In sha Allahu za mu dora daga
abubuwan da aka haramtawa
wanda yayi harama, sannan mu
dora bayani da Dawafi.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates