ka zauna ka tattauna da kanka, ka tambayi kanka wannan Tambayoyi:
Gashi ina raye, wasu da dama sun mutu, wani yana begen da ace za’a dawo dashi wannan duniya domin ya samu daman tuba ko kuma aikata wani aikin alheri, koda ko sujada ɗaya ce wacce zaiyi wa Allah, ko istigfari ko tasbihi gashi ni ina raye, shin ina Amfani da wannan dama da Allah ya bani na rayuwa?
Sannan ga da yawa daga cikin Mutane wanda Allah ya ɓatar dasu daga kan tafarkin addinin Muslunci, Amma ni gashi Allah ya halicce ni Musulmi ba dun wani aiki da nayi ba.
Ga wasu daga cikin mutane wanda suka rasa hankulansu, suna yawo akan titina basu san me sukeyi ba sabida Allah ya ɗauke musu hankalin su, gashi ni Allah ya bani.
Ga wasu Allah ya jarabcesu da wani ciwo, wannan ciwon ya hanasu sakat. Wani ko motsi baya iya yi ballantana ya tashi. Amma gashi ni Allah ya bani lafiya.
Ga wani yana kulle a gidan yari, an rabashi da iyalansa da dukiyarsa, yana begen da za’a bashi dama ya kasance tare da iyalansa amma babu.
duka wa’innan abinda aka ambata ya ɗan’uwa ka sani falala ce Allah yayi maka kuma Allah zai tambayeka game dasu, yaya kayi amfani dasu!!
Kayi amfani da lokacin ka yadda ya dace?
Kayi amfani da hankalinka yadda ya dace?
Kayi amfani da dukiyarka yacce ta dace?
Kayi amfanida lafiyarka yadda ya dace?
Toh ka shirya wa ire-iren wa’innan tambayoyin amsa ranar da babu wadda ya isa ya tserar dakai sai Ayyukan ka da Rahamar Allah.
Leave a Reply