YA KAMATA A SAKE DUBA IRIN
AQIIDUN DA KE CIKIN DARIKUN
SUFAYE
11/4/1434 H 22/2/2013 M
{ﻭﻣﺎ ﺍﺭﻳﺪ ﺍﻥ ﺃﺧﺎﻟﻔﻜﻢ ﺍﻟﻰ ﻣﺎ ﺃﻧﻬﺎﻛﻢ ﻋﻨﻪ ﺍﻥ ﺍﺭﻳﺪ
ﺍﻻ ﺍﻻﺻﻼﺡ ﻣﺎ ﺍﺳﺘﻄﻌﺖ ﻭﻣﺎ ﺗﻮﻓﻴﻘﻲ ﺍﻻ ﺑﺎﻟﻠﻪ
ﻋﻠﻴﻪ ﺗﻮﻛﻠﺖ ﻭﺍﻟﻴﻪ ﺃﻧﻴﺐ.{ ﻫﻮﺩ: ٨٨ .
A kwanakin baya ne muka yi
rubutu a cikin Facebook muna
masu jinjina wa sheik Abduljabbar
a kan matakin da ya dauka na
inkarin munkarin da wasu muridan
Darikar Tijjaniyyah suka bayyana a
fili ta yadda kowa da kowa ma zai
iya fahimtar irin kafircin da yake
cikin abin da suka fada.
To amma a wancan lokacin ni na
ce hakan bai isa ba, saboda ya
kamata a ce shi Sheik Abduljabbar
ya kara matsawa gaba ta yadda
zai dubi dukkan aqiidun da aka
gina Darikun Sufaye baga dayansu
a kansu, sannan ya yi
muqaaranarsu da abin da Shari’ar
Musulunci mai haske ta zo da shi.
Lalle, na fadi hakan ne saboda irin
abin da ni na sani game da
wadannan darikun.
Misali: Dukkan ‘Yan Darikar
Tijjaniyyah sun yadda da cewa
Sheik Ibrahim Khaulaha Shi
Gauthu ne! Abin da kuwa suke nufi
da Gauthu shi ne: Mai yin abin da
yake so cikin duniyan nan, Wanda
kome ke fitowa daga gare shi!!
Yana rubuce cikin littattafansu
magana kamar haka:-
ﻓﺎﻟﻐﻮﺙ ﻫﻮ ﺍﻟﻔﺮﺩ ﺍﻟﻮﺣﻴﺪ ﺍﻟﺬﻱ ﻳﺘﺼﺮﻑ ﻓﻲ ﺍﻟﻌﺎﻟﻢ
ﻓﻼ ﻳﺤﺪﺙ ﻓﻲ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﻜﻮﻥ ﻣﻦ ﺍﻣﺮ ﺍﻻ ﺑﻌﺪ ﺍﺫﻧﻪ .
ﻭﺗﺤﺖ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﻐﻮﺙ ﺑﺪﺭﺟﺔ ﻭﺍﺣﺪﺓ ﺍﻷﻗﻄﺎﺏ ﺍﻻﺭﺑﻌﺔ
ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻳﻤﺴﻜﻮﻥ ﺟﻬﺎﺕ ﺍﻻﺭﺽ ﻭﺗﺤﺘﻬﻢ ﺍﻷﻭﺗﺎﺩ
ﺍﻟﺴﺒﻌﺔ ﻭﻫﻢ ﻳﻤﺴﻜﻮﻥ ﺑﺎﻷﻗﺎﻟﻴﻢ ﺍﻟﺴﺒﻌﺔ ﻭﺗﺤﺘﻬﻢ
ﺍﻷﺑﺪﺍﻝ ﺍﻷﺭﺑﻌﻮﻥ !!
Ma’ana: Gauthu shi ne makadaicin
nan guda daya wanda yake yin
abin da ya ga dama, babu wani
lamari da yake faruwa a cikin
wannan Duniya sai bayan
yardarsa. Sannan a karkashin
Gauthu da daraja guda akwai
Qudubannan guda hudu wadanda
suke rike da bangarorin Duniya.
Sannan su ma a karkashinsu
akwai Autaadannan guda bakwai
wadanda suke rike da
yankunannan guda bakwai na
Duniya. Sannan su ma a
karkashinsu akwai Abdaalannan
guda arba’in!!!
Ke nan daga wannan maganar ce
za mu fahimci cewa lazimin duk
wanda ya yadda da cewa Shehu
Ibrahami Khaulaha Gauthu ne, to
kuwa dole ne ya yadda da cewa
shi Shehu Ibrahim Khaulaha shi ne
mai yin abin da ya ga dama cikin
wannan Duniya tamu, shi ne mai
rayawa, shi ne mai kashewa, shi
ne Mai azurtawa, shi ne mai
tsiyatarwa, shi ne kome, shi ne, shi
ne….
Saboda haka masu wannan waka
ta Ibrahim Khaulaha babu wani
abu sabo da suka fada game da
abin da yake nade cikin aqiidar
Tijjaniyyah, domin da ma wannan
shi ne abin da yake rubuce kuma
shi ne imanin dukkan ‘yan
Tijjaniyyah!!
Muna fata maluman Tijjaniyyah a
duk inda suke za su kara tunani
sosai, sannan su sa tsoron Allah
cikin zuciyarsu, su yi watsi da
wannan aqiidah ta Tijjaniyyah, su
komo su rika yin Musuluncinsu
kamar yadda Annabi mai tsira da
amincin Allah tare da Sahabbansa
suka yi. Allah ya taimake mu.
Ameen.
Leave a Reply