Lafiyayyen Hankali baya cin karo da ingantaccen Nassi

Danna nan domin shiga karatu Online

Allah madaukakin sarki shine ya halicci hankali sannan ya saukar da wahayi, saboda haka ba zasu taɓa cin karo ba tunda daga guri ɗaya suke.

Wahayi ya sauka ne don share ƙura akan abubuwan da hankali zai iya kuskure akan su, ko waɗanda bazai iya riskar su ba, shifa wahayi tare yake tafiya da hankali don sai sun haɗu ne Sannan za a fahimci komai a yadda yake.

Sannan wahayi ya ƙunshi abubuwan da hankali yake fahimtar manufar su(waɗanda sune suka fi yawa) da kuma waɗanda hankali bai san hikimar da take cikin su ba

Dukkanin wani Addini dole sai ya ƙunshi abubuwan da hankali bai san manufar su ba(ina fatan za a fahimci banbanci tsakanin rashin riskar abu da kuma cin karo dashi)
Saboda da irin waɗannan abubuwan ne za a rabe tsakanin waɗanda suka miƙa wuya ga Allah gaba ɗaya da kuma waɗanda basuyi hakan ba.

Sannan ta haka ne za a banbance tsakanin addini da kuma manhajin rayuwa wanda ɗan Adam zai iya ƙirƙira.
Misali duk wanda yake bin manhajin libraliyya(liberalism) ya kamata a hankalce ya fahimci duk abinda ta ƙunsa da kuma manufofin komai daya ke cikinta, ta yadda idan ya samu wani abu da bai gamsu dashi ba sai yayi watsi dashi. ( Duk da cewa dayawa daga cikin mutanen mu ba haka suke ba, don dayawa daga cikin su basu da lafiyayyen hankalin da zasu iya yin haka, kawai dai duk abinda yazo daga turai to dai-dai ne)
To da ace shima addini haka yake to kaga baza a banbance tsakanin addini da kuma abinda ba addini ba.

Idan ka fahimci wannan shimfiɗar to kasan cewa duk sanda kaga cin karo tsakanin nassi da hankali to ɗaya daga cikin abubuwa biyu ne ya faru

  1. Nassin bashi da inganci ko kuma kaine baka fahimci ma’anar sa ba, don haka mai makon ka zauna kayi ta surutu akan abinda baka fahimta ba, kamata yayi ka fara tuntuɓar waɗanda suka fahimci addini da kyau
  2. akwai matsala acikin yanayin hankalin ka da kuma hanyar da kake tunani, kenan kaga matsalar ba a Nassin bace a’a a wajen ka take

Tun sama da shekaru dubu malaman Musulunci kala kala sukayi rubuce rubuce akan wannan mas’alar kuma har yanzu ba a fasa ba, saboda haka abin mamaki ne matuƙa wani wanda bai karanta komai ba a addini ko a ilimin hankali yazo yana rubutu ba tare da yasan me yake rubutawa ba, sai dai abinda yafi ban mamaki shine mai yasa baya ganin wata matsala shi sai a wahayi kawai? Yanzu wannan itace matsalar da take damun Al’umma? Ko dai akwai wata a ƙasa ne?

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates