Mas'alolin aure Fitowa ta 13(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

Danna nan domin shiga karatu Online

Bayani ya gabata akan auren mutu’a da haramcin sa.
TAMBAYA
Mene ne hukuncin auren mutu’a idan ya riga ya auku?
AMSA:
Tunda auren mutu’a, ba tabbataccen aure ne a shari’a ba, to, idan ya auku sai a rushe shi, kafin tarewa ko bayan tarewa. Kamar yadda babban malamin nan na Malikiyya Ibnul Qasim ya fada.
TAMBAYA
Shin ana riskar da dan mutu’a zuwa ga ubansa?
AMSA:
Imam Malik da sauran almajiransa da kuma Hanabila sun ce a riskar da dan mutu’a zuwa ga ubansa duk da cewa wannan auren haramtacce ne. Sun yi kiyasi ne a kan dan da aka same shi ta hanyar auren shubuha, Allah shi ne mafi sani.
TAMBAYA
Shin akwai haddi ga wanda ya yi auren mutu’a?
AMSA:
Imam Malik da Imamu Ahmad sun ce za a yi masu (macen da namijin) ukuba ne ta hanyar ta’aziri gwargwadon abin da shugaba ya ga ya cancanta, domin tsoratarwa, amma ba za a yi masu haddin zina ba, domin wanda ya yi wannan auren ya yi shi ne bisa shubuha. Allah shi ne mafi sani.
Monday at 9:04pm · Like · ReportAbdullahi Bala Zango and 51 others like this.
View previous comments
Gambo Sabo Said
Allah ya karawa mallam yawan kwana
Like · Tuesday at 10:45am
Haruna Usman Aliyu
Ya kuke gudun Gaskiya.Harma wani nacewa na kawo hujja mana,ai danaso ne shi sheikh dinku yazo nayi magana dashi,amma tunda naga kuna ta cika baki,toh ku saurari hujjoji na akan mut,ah,kuma dan Allah a amsa da hujja ba surutu ba.
Like · Tuesday at 11:31am
Haruna Usman Aliyu
(1)Bismillahi Rahmanir Rahim….zan fara da yin shinfida.A cikin Suratul Nisa,i,aya ta 24,Allah Ta,alah yace:-“…Fastamta,atum bihi min hunna fa,atuuhunna ujuurahunna
“….
FASSARA:-“…Abin kuka ji dadi dasu daga gare su,to,ku basu ijarorinsu bisa farilla”…,suratun Nisa,i.
-Anan,Ibn Jarir Dabari,imamul mussasirun na ahlussunna,ya kawo a cikin Tafsirin sa( JAMI,UL BAYAN-ANIL TA,AWILIL QUR,AN) a karkakashin wannan ayar cewa wannan maganar tana magana ne akan Auren Mut,ah,inda daga cikin ruwayoyi da ya kawo,ya kawo riwayar Saddee da Ibn Abbass inda sukace kasance suna karanta ta da “Ila ajalim musamma”,,”zuwakaidaddun lokaci”,suna nufin Mut,atin Nisa,i kenan.
(2)Sannan, a cikin (SAHIHUL BUKHARI),karkashin Kitabun Nikaa,hi,Hadisina 1844,hadisin Jabir bn Abdullah da salamata bn Ak,wa,sun ruwaito daga manzon Allah(s),a yayin da suke cikin runduna na yaki,inda Ma,aikin Allah(s) ya tawo garesu yace dasu :-“Innahu qad uzzina lakum an tastami,uu,fastamti,uu”,-yace”Lallai shi Allah yayi muku izini da kuyi auren Mut,ah,to kuyi ta.
-Anan Allah da manzon sa sun yiwa sahabbai izni da suyi auren Mut,ah bisa cika sharuddan ta. kuma dayawa daga cikin sahabbai mabukata sunyi ta.Wannan babu tamtama akai.
-kuma wannan cewa Auren Mut,ah,Umurni ne daga Allah da Annabin sa Muhammad(S),sahabbai kuma sunyi ta.Kuma babu wata aya a Qur,ani inda Allah Ta,alah ya haramta ta,haka kuma babu Hadisi sahihi wanda ya nuna cewa manzon Allah(s)ya hana yinta,sai dai hadisi nakikkira,idan kuma akwai sahihin hadisi,to,a kawo mugani,domin a cikin littafin hadisi na Imam Tabarani(MU,UJAMUL AUSAT),juz,i na 4,hadisi na 5741,daga Ummul mumineen Aisha,Manzon Allah(s) yace:-“Laatum sikuu ala shai,in,fa,innilaa uhillu illa maa uhillallah fi kitabahu,wala ahrama illa maa haramallahu fi kitabahu”,-manzon Allah(s) yace:-“kada kuyi riko da komai(abun da ba daga gare ni ba)domin ni bana halatta sai dai abunda Allah ya halatta a littafinsa,kumabana haramta sai dai abunda Allah ya haramta daga littafinsa”.
-To,tambaya anan shine, idan Allah bai haramta ba kuma Manzon Allah bai haramta ba,WAYE YA HARAMTA?….Umar bn Khattab ne ya haramta.Imam Hafiz Jalaluddeen Syuti a cikin littafinsa(TARIKHUL KHULAFAA,U)a babin faslu fi,auliyaati Umar bn Khattab radiyallahu anhu,yace: “Awwalu man harrama mut,ata,Umar bn Khattab”-watau”Farkon wanda ya fara haramta Mut,ah,shine Umar bn Khattab”

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates