TAMBAYA:
Mene ne hukuncin auren mace fiye da hudu?
AMSA:
Auren mace fiye da hudu haramun ne, domin ya sabawa littafin Allah da sunnar Manzonsa usallallahu alaihi wa sallam, da fahimtar magabata na kwarai, kuma aure ne na jahiliyya, domin a wancan lokacin mutum kan auri mace fiye da hudu. Ubangiji subhanahu wa ta’ala ya fada cewa:
وَإِنْ خِفْتُمْ أَلَّا تُقْسِطُوا فِي الْيَتَامَى فَانْكِحُوا مَا طَابَ لَكُمْ مِنَ النِّسَاءِ مَثْنَى وَثُلَاثَ وَرُبَاعَ …
Ma’ana:
Idan kun ji tsoron ba za ku iya yin adalci a kan auren marayu (wajen ba su sadaki daidai da su) ba, to, ku auri (wasu matan daban) wadanda suka dadada a gare ku biyu ko uku ko hudu…
Salon wannan ayar ya yi daidai da fadin Ubangiji subhanahu wa ta’ala cewa:
جَاعِلِ الْمَلَائِكَةِ رُسُلًا أُولِي أَجْنِحَةٍ مَثْنَى وَثُلَاثَ وَرُبَاع
ma’ana:
… (Ubangiji) ya sanya Mala’iku manzanni masu fuka-fukai guda biyu ko uku ko hudu…
Yana nufin a cikin Mala’iku akwai masu fuka-fukai biyu akwai kuma masu uku da kuma masu hudu, ba yana nufin a hada biyu da uku da hudu ba.
Haka kuma Imamus Shaukani ya ce:
Wannan ayar ta nuna hada mata fiye da hudu haramun ne, domin abin da ayar take nufi Allah yana magana ne a kan al’ummar Manzon Allah صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ cewa kowanne daga cikinsu yana da damar zabin mata adadin da zai iya aura, ko dai ya auri biyu ko uku ko hudu, kamar yadda idan aka baiwa jama’a kudi dubu daya kuma a ce da su kowa ya dauki dari biyu-biyu ko dari uku-uku ko dari hudu-hudu, sannan ya ce; wadanda suka fahimci wannan aya akan ana iya hada mata tara ko fiye da haka, to, hakika sun jahilci harshen Larabci.
Abdullahi Ibn Abbas radhiyallahu anhu, da jumhurum malamai sun fada game da wannan ayar cewa;
لأن المقام مقام امتنان وإباحة، فلو كان يجوز الجمع بين أكثر من أربع لذكره.
Ma’ana:
Wannan ayar waje ne na ni’ima da gori da halacci, da a ce ya halatta a hada mata fiye da hudu da Allah ya fada.
Haka kuma Imamus Shafi’i ya ce;
وقد دَلَّت سنة رسول الله صلى الله عليه وسلم المبينة عن الله أنه لا يجوز لأحد غير رسول الله صلى الله عليه وسلم أن يجمع بين أكثر من أربع نسوة.
Ma’ana:
Hakika sunnar Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam wadda take bayyana zancen Allah ta nuna cewa bai halatta ga wani mutum ya auri sama da mata hudu ba, sai Manzon Allah صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ, (domin wannan khususiyyarsa ce kamar yadda malamai suka fada).
Sai Imam Ibn Kathir ya ce:
وهذا الذي قاله الشافعي، رحمه الله، مجمع عليه بين العلماء، إلا ما حُكي عن طائفة من الشيعة أنه يجوز الجمع بين أكثر من أربع إلى تسع.
Ma’ana:
Kuma wannan abin da Imamus Shafi’i ya fada (Allah ya yi masa rahama) a kan haka ne jumhurum malamai suka tafi, idan ban da wasu bangarori na `yan shi’a, wadanda suke ganin za a iya auren mata fiye da hudu har zuwa tara.
Haka kuma Imamul Bukhari ya ce; Ibn Abbas رضي الله عنه ya ce;
مَا زَادَ عَلَى أَرْبَعٍ فَهْوَ حَرَامٌ ، كَأُمِّهِ وَابْنَتِهِ وَأُخْتِهِ
Ma’ana:
Auren mace fiye da hudu haramun ne, kamar haramcin wanda ya auri mahaifiyarsa ko `yarsa ko `yar’uwarsa.
A wata ruwayar kuma Ibn Abbas رضي الله عنه ya ce;
والمحصنات من النساء إلا ما ملكت أيمانكم كتاب الله عليكم قال لا يحل لمسلم أن يتزوج فوق أربع فإن فعل فهي عليه مثل أمه وأخته
Ma’ana:
An haramta muku katangaggun mata (masu aure) daga cikin mataye face abin da kuka mallaka na kuyangi, hukuncin Allah ne a gare ku, sai (Ibn Abbas رضي الله عنه) ya ce; bai halatta ga musulmi ya auri sama da mace hudu ba, idan kuma ya aura, to, ta zama (haramun a gare shi) kamar yadda mahaifiyarsa da `yar’uwarsa suke haramun a gare shi.
Imamu Hasanul Basari ya fassara fadin Allah
كتاب الله عليكم
Ma’ana:
Kada ku auri mata fiye da hudu.
Ubaidatu da Ada’u da Suddi da Ibrahimun Nakha’i sun ce:
كتاب الله عليكم
Ma’ana:
Su ne abin da aka haramta muku na auren mata fiye da hudu.
Haka kuma Imamul Baihaki ya rawaito cewa;
أن أم سعيد أم ولد علي رضي الله عنه حدثتها قالت كنت أصب على علي رضي الله عنه الماء وهو يتوضأ فقال يا أم سعيد قد اشتقت أن أكون عروسا قالت فقلت ويحك ما يمنعك يا أمير المؤمنين قال أبعد أربع قالت فقلت تطلق واحدة منهن وتزوج أخرى قال إن الطلاق قبيح أكرهه.
Ma’ana:
Hakika Ummu Sa’id wato kuyangar Sayyadina Aliyu رضي الله عنه ta ce: na kasance ina zuba wa Sayyadina Aliyu رضي الله عنه ruwa yana alwala, sai ya ce; ya Ummu Sa’id ina kwadayin na zama ango, sai ta ce; to mai zai hana ka ya Amirul Muminina? Sai ya ce mata hudu ne (za su hana ni), sai ta ce; to ka saki daya ka auri wata mana? Sai ya ce; hakika saki mummunan abu ne ba na son sa.
Haka kuma hadisi ya tabbata daga Wahabul Asadi ya ce:
أَسْلَمْتُ وَعِنْدِى ثَمَانُ نِسْوَةٍ فَذَكَرْتُ ذَلِكَ لِلنَّبِىِّ. صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ النَّبِىُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ « اخْتَرْ مِنْهُنَّ أَرْبَعًا»
Ma’ana:
Na musulunta alhali ina da mata takwas, sai na fadawa Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam, sai ya ce; ka zabi hudu daga cikinsu.
Da kuma hadisin Abdullahi Ibn Umar رضي الله عنه ya ce:
أَنَّ غَيْلَانَ بْنَ سَلَمَةَ الثَّقَفِيَّ أَسْلَمَ وَلَهُ عَشْرُ نِسْوَةٍ فِي الْجَاهِلِيَّةِفَأَسْلَمْنَ مَعَهُ فَأَمَرَهُ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنْ يَتَخَيَّرَ أَرْبَعًا مِنْهُنَّ
Ma’ana:
Hakika Gailana Ibn Salamatas Sakafi رضي الله عنه ya musulunta, yana da mata goma a zamanin jahiliyya, sai su ma suka musulunta tare da shi, sai Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya umarce shi da ya zabi hudu daga cikinsu.
A nan ne muke jan hankalin `yan’uwa al’ummar Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam cewa ba a fahimtar hakikanin littafin Allah da sunnar Manzonsa sallallahu alaihi wa sallam ba tare da malami ba, domin muna jin wadansu suna babatun cewa mutum zai iya auren mace fiye da hudu, kuma har suna kafa hujja da maganganun wasu kungiyoyin shi’a wadanda maganganunsu ba hujja ba ne, kasancewar sun sabawa daidaitacciyar fahimta wadda magabata na kwarai suke a kanta musamman Sahabban Manzon Allah , domin ijma’in Sahabbai da wadanda suka biyo bayansu har zuwa yau, sun hadu akan babu wanda yake auren mace fiye da hudu sai kungiyoyin da suka saba wa dandazon musulmi.
Allah ka shiryar da mu hanya madaidaiciya, amin.
Leave a Reply