TAMBAYA
Wace irin mace Shari`a ta kwadaitar da namiji ya aura; kuma wane irin namiji Shari`a ta kwadaitar da a baiwa auren ‘ya mace?
AMSA:
1.Mace ta farko da ya kamata mutum ya zaba itace musulma ma`abociyar addini. Ubangiji subhanahu wa ta’ala ya ce:
…وَلَأَمَةٌ مُؤْمِنَةٌ خَيْرٌ مِنْ مُشْرِكَةٍ وَلَوْ أَعْجَبَتْكُمْ…البقرة: 221
Ma’ana:
…Hakika kuyanga mumina ta fi alkairi fiye da `ya kafira, ko da kuwa ta kayatar da ku (da kyawunta)…
Haka kuma hadisi ya tabbata daga Abu Huraira radhiyallahu anhu ya ce: Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya ce:
تُنْكَحُ الْمَرْأَةُ لِأَرْبَعٍ: لِمَالِهَا وَلِحَسَبِهَا، وَجَمَالِهَا، وَلِدِينِهَا، فَاظْفَرْ بِذَاتِ الدِّينِ تَرِبَتْ يَدَاكَ.
Ma’ana:
Ana auren mace domin siffofi guda hudu: Ko don dukiyarta, ko asalinta, ko kyawunta, ko addininta. Ka ribaci ma`abociyar addini, idan ba haka ba, sai hannunka ya wofanta.
A nan Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama yana fadin irin yadda mutane suke zabar matar da za su aura. Ko dai ka aure ta domin dukiya, wadda takan kare, ko kuma ta hana ka dukiyar tata. Ko ka aure ta domin asalinta, wanda ba zai amfane ka da komai ba, kuma a qarshe ma ta zo tana yi maka girman kai. Ko ka aure ta domin kyawunta, wanda shi ma ba ya dawwama, saboda lokaci zai zo, wanda kyawun zai gushe. Don haka Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya ce a zabi ma`abociyar addini, kuma ya yi bushara ga wanda yayi haka da cewa zai samu albarka da rabauta a cikin auren. A karshe kuwa inda Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya ce “hannunka ya wofanta”, ba addu`a ba ce, salon magana ne da kan zo a harshen Larabci. Amma yana nufin za a hadu da matsala a cikin auren.
A nan ne muke nasiha ga `yan’uwa da cewa, a ji tsoron Allah, wurin zabar abokiyar zama, a zabi ma`abociyar addini. Wannan shi ne zai dawwamar da auren. Idan kuwa aka sami ma`abociyar addini, kuma ga kyau, ga asali, ga dukiya, to, wannan madalla da ita.
2.Siffa ta biyu da ake so a duba ita ce mace mai rahama da tausayi ga `ya`yanta, mai kuma tausasawa da kiyaye hakkin mijinta. Dalilinmu kuwa hadisi ya tabbata daga Abu Huraira radhiyallahu anhu wanda Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama yake cewa:
خَيْرُ نِسَاءٍ رَكِبْنَ الْإِبِلَ صَالِحُو نِسَاءِ قُرَيْشٍ: أَحْنَاهُ عَلَى وَلَدٍ فِي صِغَرِهِ، وَأَرْعَاهُ عَلَى زَوْجٍ فِي ذَاتِ يَدَاهُ.
Ma’ana:
Mafifitan mata, masu hawa rakuma, sune managartan mata, matan Kuraishawa, sun fi tausayawa `ya`ya a yayin da suke kanana, kuma sun fi kiyaye dukiyar mazajensu.
A nan Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama yana yabon matan Kuraishawa saboda siffofin da suke da su na tausayi da rahama ga `ya`yansu da kuma kiyaye hakkin miji da dukiyarsa. Amma ya siffanta su da masu hawa rakuma ne saboda shi ne abin hawansu a wancan lokacin.
3. Siffa ta uku itace , ta zama amintacciyya kuma ma`abociyar biyayya ga mijinta. Saboda hadisi ya tabbata inda Abu Huraira radhiyallahu anhu yake cewa:
سُئِلَ أَيُّ النِّسَاءِ خَيْرٌ؟ قَالَ: الَّتِي تَسُرُّهُ إِذَا نَظَرَ، وَتُطِيعُهُ إِذَا أَمَرَ، وَلاَ تُخَالِفُهُ فِي نَفْسِهَا وَمَالِهِ بِمَا يَكْرَهُ.
Ma’ana:
An tambayi Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama game da mafificiyar mace? Sai ya ce: “Ita ce wacce take farantawa miji idan ya kalle ta, take yi masa biyayya, idan ya umarce ta, sannan ba ta saba masa a kan kanta da kuma dukiyarsa.
4.Siffa ta hudu itace, ta kasance mai haihuwa. Wannan kuwa ana gane haka ne daga danginta, idan sun kasance masu yawan haihuwa ne. Sai dai Ubangiji I yana iya yin ikonsa duk yadda ya so. Domin Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya kwadaitar da mu cewa, mu auri wacce muke kauna kuma mai haihuwa, kamar yadda hadisi ya tabbata a cikin Sunan Abī Dāwūd daga Ma`aqil Ibn Yasar radhiyallahu anhu ya ce:
جَاءَ رَجُلٌ إِلَى النَّبِيِّ. فَقَالَ: إِنِّي أَصَبْتُ امْرَأَةً تَ حَسَبٍ وَجَمَالٍ، وَإِنَّهَا لاَ تَلِدُ، أَفَأَتَزَوَّجُهَا؟ قَالَ: لاَ، ثُمَّ أَتَاهُ الثَّانِيَةَ فَنَهَاهُ، ثُمَّ أَتَاهُ الثَّالِثَةَ. فَقَالَ: تَزَوَّجُوا الْوَدُودَ الْوَلُودَ، فَإِنِّي مُكَاثِرٌ بِكُمُ الْأُمَمَ.
Ma’ana:
Wani mutum ya zo wurin Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama sai ya ce: Na sami wata mace ma`abociyar asali da kyawu amma ba ta haihuwa, shin na aure ta? Sai Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya ce: “A`a!”. Sai ya sake dawowa a karo na biyu (a kan zancen auren), sai Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya hana shi. Sannan ya sake dawowa a karo na uku, sai Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya ce: “Ku auri ma`abociyar soyayya kuma mai yawan haihuwa, domin hakika zan yi alfahari da yawanku a ranar alkiyama.
Amma idan mutum yana da `ya`ya tare da wadansu matan ko kuma yana da mata masu haihuwa, to, babu laifi don ya auri wadda ba ta haihuwa.
Wadannan siffofin da ake dubawa kafin a auri mace su ne kuma ya kamata itama mace ta duba lokacin da take zabawa kanta miji. Su ne kuma ya kamata waliyyan mace su duba kafin su baiwa wani auren `yar su. Kada mace ta zabi miji, ko kuma waliyyan mace su aurawa wani `yarsu don kawai yana da kudi, ko domin matsayinsa, ko don shi kyakkyawa ne. Kamata ya yi a zabi mai addini, mai haihuwa, mai riqe aure (ba mai yawan aure-aure, ya auri wannan ya saki waccan ba), mai zama lafiya da mata.
Ya kamata kuma a fahimci cewa idan aka ce mace mai addini ko namiji mai addini, ana nufin mai halaye da dabi`u na imani da tsoron Allah, da gaskiya da amana da adalci da jin kai da tausayi da sanin ya kamata da basira da tsaida salla da kiyaye dokokin Shari`a.
Wadannan siffofin na hali da hankali da mutuntaka su ne abin da addini yake ginawa a zuciyar mutum, kuma idan aka ce mutum mai addini ana nufin wanda ya siffanta da su. Sanya hijabi ko tsaida gemu ko dage wando, alamu ne na addini, amma ba alamu ne na tabbatarsa ba. Don haka sai a bincika, domin sau da yawa” kama da wane ba wane ba ne”.
Leave a Reply