Mas'alolin aure Fitowa ta 8(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

Danna nan domin shiga karatu Online

TAMBAYA:
Wadanne nau’ikan aure ne ake yi a lokacin Jahiliyya, wanda Shari’ar Musulunci ta haramta?
AMSA:
Nau’ikan auren da shari’ar musulunci ta haramta sun hadar da:
1-Auren Shigari (wato auren musanye).
2-Auren Kisan Wuta.
3-Auren Mutu’a.
Da sauransu.
TAMBAYA:
Mene ne auren shigari (auren musanye) kuma mene ne hukuncinsa?
AMSA:
Abin da ake nufi da kalmar “Shigari” a harshen Larabci shine “daga kafa” don haka ne ake cewa:
شغر الكلب
Ma’ana:
Ana fadin haka yayin da kare ya daga kafarsa kamar zai yi fitsari, alama ce ta ya balaga. Haka kuma ana cewa:
شغرت المرءة شغرا
Ana nufin mace ta daga kafarta lokacin saduwa. Ma’ana suna so ne su ce: kada ka daga kafar `yata ko kanwata don yin jima’i, face ni ma na daga kafar `yarka ko kanwarka, don mu yi musanyen farji. Wannan al’adar mutanen Jahiliyya ce wadda Shari’ar Musulunci ta haramta.
Amma ma’anar Auren Shigari a Shari’ance kuwa shine; Mutum ya aurar da `yarsa ko `yar’uwarsa ga wani mutum da sharadin shima ya aura masa `yarsa ko `yar’uwarsa ba tare da sadaki a tsakaninsu ba, wato sun yi musanyen farji ne kawai.
Wannan fassarar Imam Malik ce Allah ya yi masa rahama da sauran malamai.
ASALIN AUREN SHIGARI:
Alkali Iyadh (Allah ya ji kansa) ya ce: Auren Shigari yana daga cikin auren Jahiliyya wanda ake yin sa kafin zuwan Musulunci..
HUKUNCIN AUREN SHIGARI:
Babban malamin nan na Malikiyya Ibn Abdulbar ya ce: malamai sun hadu akan cewa: yin auren shigari bai halatta ba ( haramun ne).
Auren Shigari Yana Da Siffa Biyu
Siffa ta farko ita ce:- Mutum ya aurawa wani `yarsa ko `yar’uwarsa a kan cewa shima ya aura masa `yarsa ko `yar’uwarsa, amma ba tare da an bayar da sadaki a tsakaninsu ba. Wannan siffar malamai sun yi ijma’i a kan cewa haramun ce. Dalilinsu kuwa shine: hadisi ya tabbata daga Abdullahi Ibn Umar radhiyallahu anhu ya ce:
أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم نَهَى عَنِ الشِّغَار…
Ma’ana:
Hakika Manzon Allah sallallahu alaihii wa sallama ya hana yin auren shigari…
Sai kuma Abdullahi Ibn Umar radhiyallahu anhu ya fassara auren shigari da cewa:
… أَنْ يُزَوِّجَ الرَّجُلُ ابْنَتَهُ عَلَى أَنْ يُزَوِّجَهُ ابْنَتَهُ وَلَيْسَ بَيْنَهُمَا صَدَاقٌ.
Ma’ana:
…Shi ne mutum ya aurawa wani ‘yarsa ko ‘yar uwarsa da sharadin shima ya aura masa ‘yarsa ko ‘yar uwarsa, amma babu wanda ya bayar da sadaki a tsakanin su..
Siffa ta biyu ita ce:- Mutum ya aurawa wani `yarsa ko `yar’uwarsa da sharadin shima ya aura masa `yarsa ko `yar’uwarsa, amma dukkansu kowa ya biya sadaki.
SABANIN MALAMAI A KAN SIFFA TA BiYU:
Malamai sun yi sabani akan siffa ta biyu kamar haka:
1-Imam Malik ya tafi a kan cewa: za a raba auren Shigari idan ya afku, ko da kuwa mijin ya tara da matar ko kuma bai tara da ita ba; auren rusasshe ne har abada, an ambaci sadaki a lokacin daura shi ko ba a ambaci sadaki ba.
2-Imamush Shafi’i kuma ya ce: Idan aka ambatawa daya daga cikin su ko kuma su duka biyun sadakinsu, to, auren ya halatta, matukar an ambatawa kowacce sadakinta daidai da ita, sannan kuma kowacce an yi dukhuli da ita.
Dalilin Imam Malik da sauran malaman da suka ce auren shigari haramun ne, shine hadisin da Abdullahi Ibn Umar radhiyallahu anhu ya rawaito cewa:
أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ نَهَى عَنِ الشِّغَار…
Ma’ana:
Hakika Manzon Allah sallallahu alaihii wa sallama ya hana yin auren shigari…
Kuma duk abin da Manzon Allah sallallahu alaihii wa sallama ya hana ya zama haramun ne domin fadin Ubangiji subhanahu wa ta’ala cewa:
…وَمَا آتَاكُمُ الرَّسُولُ فَخُذُوهُ وَمَا نَهَاكُمْ عَنْهُ فَانْتَهُوا… الحشر: 7
Ma’ana:
… Kuma abin da Manzon Allah sallallahu alaihii wa sallama ya zo muku da shi, to ku rike shi, abin da kuma ya hane ku, to, ku hanu…
Sannan Manzon Allah sallallahu alaihii wa sallama ya ce:
مَا نَهَيْتُكُمْ عَنْهُ فَاجْتَنِبُوهُ وَمَا أَمَرْتُكُمْ بِهِ فَافْعَلُوا مِنْهُ مَا اسْتَطَعْتُم
Ma’ana:
Abin da na hane ku da shi, to, ku nisance shi, abin da kuma na umarce ku da yin sa, to, ku aikata shi gwargwadon iko.
Haka kuma Manzon Allah sallallahu alaihii wa sallama ya ce:
« مَنْ عَمِلَ عَمَلاً لَيْسَ عَلَيْهِ أَمْرُنَا فَهُوَ رَدٌّ »
Ma’ana:
Duk wanda ya aikata wani aiki wanda ba umarninmu a kansa, abin mayarwa ne.
Kuma Hafiz Ibn Abdulbar ya ce: A cikin ka’ida ta Usulul Fikihi, idan aiki ya ci karo da hani, to, wannan aikin lalatacce ne. Wadannan su ne dalilan da suke nuna cewa auren shigari haramun ne, ko da kuwa an daura shi kuma an bayar da sadaki.
Wannan kuma itace maganar da ta fi rinjaye. Allah shine mafi sani.
DALILIN SABANIN MALAMAI AKAN WANNAN HANIN:
Wannan sabani ya samu ne sakamakon tunanin shin illar(dalilin) wannan hanin tana komawa ne ga rashin ambaton sadaki ko kuma tana komawa ne kan kulla auren a bisa sharadin bani na baka?
Amsa: Idan muka ce, illar tana komawa ne kan rashin ambaton sadaki, to, koyaushe aka ambaci sadaki auren ya tabbata kenan.
Idan kuma muka ce, illar hanin tana komawa ne kan kulla auren a bisa wancan sharadin, to, auren rusasshe ne, amma ba saki ba ne, ko ya tara da ita ko bai tara da ita ba.
Saidai magana mafi rinjaye anan ita ce; ta biyu, don kuwa Manzon Allah sallallahu alaihii wa sallama ya hana auren shigari ne zallarsa ba tare da wani sharadi ko wariya ba.
Kuma hadisi ya tabbata daga Abdullahi Ibn Umar radhiyallahu anhu ya ce: Manzon Allah sallallahu alaihii wa sallama ya ce:
لاَ شِغَارَ فِى الإِسْلاَم
Ma’ana:
Babu auren shigari a cikin Musulunci (domin aure ne na jahiliyya).
Haka kuma an rawaito daga Abdurrahman Ibn Hurmuz al-A’araj ya ce:
أَنَّ الْعَبَّاسَ بْنَ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ الْعَبَّاسِ أَنْكَحَ عَبْدَ الرَّحْمَنِ بْنَ الْحَكَمِ ابْنَتَهُ وَأَنْكَحَهُ عَبْدُ الرَّحْمَنِ ابْنَتَهُ وَكَانَا جَعَلاَ صَدَاقًا فَكَتَبَ مُعَاوِيَةُ إِلَى مَرْوَانَ يَأْمُرُهُ بِالتَّفْرِيقِ بَيْنَهُمَا وَقَالَ فِى كِتَابِهِ هَذَا الشِّغَارُ الَّذِى نَهَى عَنْهُ رَسُولُ الله صلى الله عليه وسلم.
Ma’ana:
Lallai Abbas Ibn Abdullah Ibn Abbas radhiyallahu anhuma ya aurawa Abdurrahman Ibnul Hakam `yarsa, shima kuma Abdurrahman ya aura masa `yarsa, kowa ya ba da sadaki a cikin su, sai Mu’awiya Ibn Abi Sufyan radhiyallahu anhuma (a lokacin yana Halifa) ya rubutawa Marwan (a lokacin yana gwamna a Madina), yana mai umartarsa da ya raba tsakanin ma’auratan, yana cewa; wannan shine “Auren Shigarin” da Manzon Allah sallallahu alaihii wa sallama yayi hani a kansa.
Allah shi ne mafi sani.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates