Mas'alolin aure Fitowa ta 22(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

TAMBAYA:
Mene ne hukuncin abincin da ake
yi da zarar an gama daurin aure?
AMSA:
Yin wannan abincin daga gidan
iyayen ango ko amarya babu laifi,
matukar an yi shi ne don a ciyar da
dangi da abokan arziki wadanda
suka zo daga nesa don taya
murna; Shari`ar Musulunci tana
son a karrama bako. Amma idan
an yi shi ne don koyi da Turawa ko
kuma domin gasa ko nuna isa, to,
wannan ya sabawa Sunnar
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama, kuma barin sa shine mafi
dacewa. Idan kuwa angwaye sun
yi shi ne a matsayin walima ta
sunna, to, ya fi kyau su bari sai
bayan an tare.
TAMBAYA:
Mece ce walima a Sunnance?
AMSA:
Walima ita ce shirya abinci don
nuna farin ciki da ni’imar da Allah
ya yi wa mutum. Babban abin da
aka fi sani shi ne ana yin ta ne
lokacin biki. Domin Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama ya yi
walima, kuma ya yi umarni da a yi
ta. Hadisi ya tabbata daga Anas
Ibn Malik radhiyallahu anhu ya ce:
ﺃﻗﺎﻡ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺑﻴﻦ ﺧﻴﺒﺮ ﻭﺍﻟﻤﺪﻳﻨﺔ
ﺛﻼﺛﺎ ﻳﺒﻨﻰ ﻋﻠﻴﻪ ﺑﺼﻔﻴﺔ ﺑﻨﺖ ﺣﻴﻲ ﻓﺪﻋﻮﺕ
ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ ﺇﻟﻰ ﻭﻟﻴﻤﺘﻪ ﻓﻤﺎ ﻛﺎﻥ ﻓﻴﻬﺎ ﻣﻦ ﺧﺒﺰ ﻭﻻ
ﻟﺤﻢ ﺃﻣﺮ ﺑﺎﻷﻧﻄﺎﻉ ﻓﺄﻟﻘﻲ ﻓﻴﻬﺎ ﻣﻦ ﺍﻟﺘﻤﺮ ﻭﺍﻷﻗﻂ
ﻭﺍﻟﺴﻤﻦ …
Ma’ana:
Yayin da Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama yake dawo wa
daga Khaibar zuwa Madina, ya
tsaya kwana uku domin tarewa da
Nana Safiyya ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ, sai ya ce
da ni in gayyato jama`ar Musulmi
don walimar aurensa. Babu nama
ko kuma gurasa a cikin ta, sai ya yi
umarni da a shimfida fata da aka
jeme, sannan aka zuba dabino da
cikwi da mai (Al-Hissa), (sai
Musulmi suka ci)…
Kuma wani hadisin ya tabbata
daga Anas Ibn Malik radhiyallahu
anhu ya ce:
ﺃﻥ ﺍﻟﻨﺒﻰ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺭﺃﻯ ﻋﻠﻰ ﻋﺒﺪ
ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺑﻦ ﻋﻮﻑ ﺃﺛﺮ ﺻﻔﺮﺓ ﻓﻘﺎﻝ » ﻣﺎ ﻫﺬﺍ «
ﻗﺎﻝ ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺇﻧﻰ ﺗﺰﻭﺟﺖ ﺍﻣﺮﺃﺓ ﻋﻠﻰ ﻭﺯﻥ
ﻧﻮﺍﺓ ﻣﻦ ﺫﻫﺐ. ﻗﺎﻝ» ﻓﺒﺎﺭﻙ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﻚ ﺃﻭﻟﻢ ﻭﻟﻮ ﺑﺸﺎﺓ
».
Ma’ana:
Hakika Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama ya ga shaidar
turare(mai nuna alamar angwanci)
a jikin Abdurrahman Ibn Auf
radhiyallahu anhu, sai ya ce da shi:
mene ne wannan? Sai ya ce: ya
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama na auri wata mata ne a
kan sadakin zinare gwargwadon
kwayar dabino. Sai Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama ya ce
da shi: Allah ya sa albarka a cikin
aurenka kuma ka yi walima ko da
da akuya ne.
Saboda haka ana yin walima ne
gwargwadon iko, ba a ce mutum
ya kallafawa kansa abin da ba zai
iya ba. Kuma an fi so duk mutumin
da aka gayyace shi walima, ya
amsa wannan gayyatar, matukar
babu batsa da abubuwan haramci
a wurin. Domin hadisi ya tabbata
daga Abdullahi Ibn Umar
radhiyallahu anhu ya ce: Manzon
Allah sallallahu alaihi wa sallama
ya ce:
ﺇﺫﺍ ﺩﻋﻰ ﺃﺣﺪﻛﻢ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﻮﻟﻴﻤﺔ ﻓﻠﻴﺄﺗﻬﺎ
Ma’ana:
Idan aka gayyaci daya daga
cikinku zuwa walima, to, ya amsa
wannan gayyatar.
Kuma an fi son abincin walima ya
zama bai daya ga babba da yaro,
masu arziki da talakawa, ba tare
da kebanta ko fifita wani bangare
akan wani ba. Sabanin idan bako
mutun yayi, wanda hidimar da yake
yiwa wani, idan wani ya zo zai yi
masa tafi ta wancan; kowa yana da
matsayin sa. Saboda hadisi ya
tabbata daga Abu Hurairata
radhiyallahu anhu ya ce: Manzon
Allah sallallahu alaihi wa sallama
ya ce:
ﺷﺮ ﺍﻟﻄﻌﺎﻡ ﻃﻌﺎﻡ ﺍﻟﻮﻟﻴﻤﺔ ﻳﻤﻨﻌﻬﺎ ﻣﻦ ﻳﺄﺗﻴﻬﺎ ﻭﻳﺪﻋﻰ
ﺇﻟﻴﻬﺎ ﻣﻦ ﻳﺄﺑﺎﻫﺎ ﻭﻣﻦ ﻟﻢ ﻳﺠﺐ ﺍﻟﺪﻋﻮﺓ ﻓﻘﺪ ﻋﺼﻰ
ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ
Ma’ana:
Mafi sharrin abinci, shi ne abincin
walimar da za a hana wanda zai zo
(wato mabukaci) kuma a gayyaci
wadanda suke kin zuwa (masu
kudi/mawadata). Kuma duk Wanda
bai amsa kiran walima ba, hakika
ya sabawa Allah da Manzonsa
sallallahu alaihi wa sallama.
Wannan ya nuna wajabcin amsa
gaiyatar da aka yi wa mutun saidai
idan akwai uzuri. Allah ya sa mu
gyara.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

One response to “Mas'alolin aure Fitowa ta 22(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)”
  1. maman Hafsa Avatar
    maman Hafsa

    Allah ya saka da alheri

Leave a Reply to maman HafsaCancel reply

Latest updates
Categories