TAMBAYA
Mene ne hakkin mace a kan
mijinta?
AMSA:
Lallai mata suna da hakkoki masu
yawa a kan mazajensu kamar
yadda su ma maza suke da
hakkoki a kan matansu. Domin
gudun tsawaitawa za mu rarraba
hakkokin mata a darasi 3, sannan
mu shiga hakkokin maza.
Yana daga cikin hakkokin mata a
kan mazansu:-
1- Kyautatawa tare da tausasawa
da tausayawa, da sakin fuska a
gare su. Dalili kuwa fadin Allah
subhanahu wa ta’ala cewa:
… ﻭﻋﺎﺷﺮﻭﻫﻦ ﺑﺎﻟﻤﻌﺮﻭﻑ… ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ19 :
Ma’ana:
Kuma ku zauna da su (zama) na
kyautatawa …
Haka kuma hadisi ya tabbata daga
Nana A’isha ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ yayin da
ta baiwa Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama labarin Ummu
Zar’in da irin kaunar da take yi wa
tsohon mijinta Abu Zar’in saboda
kyautatawarsa gare ta, sai Annabi
sallallahu alaihi wa sallama ya ce
da ita:
ﻛﻨﺖ ﻟﻚ ﻛﺄﺑﻲ ﺯﺭﻉ ﻷﻡ ﺯﺭﻉ
Ma’ana:
Ni na kasance a gare ki kamar Abu
Zar’in ga Ummu Zar’in.
Ita kuma Nana A’isha ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ
sai ta ce masa:
ﺑﺄﺑﻲ ﺃﻧﺖ ﻭﺃﻣﻲ ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻞ ﺃﻧﺖ ﺧﻴﺮ ﺇﻟﻲ ﻣﻦ
ﺃﺑﻲ ﺯﺭﻉ
Ma’ana:
Fansar ka da mahaifina da
mahaifiyata ya Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama,
Wallahi matsayinka a wurina ya fi
matsayin Abu Zar’in ga Ummu
Zar’in.
2- Ciyar da su da tufatar da su da
kuma samar musu muhallin zama
na halal gwargwadon iko. Saboda
fadin Ubangiji subhanahu wa ta’ala
cewa:
ﻟﻴﻨﻔﻖ ﺫﻭ ﺳﻌﺔ ﻣﻦ ﺳﻌﺘﻪ ﻭﻣﻦ ﻗﺪﺭ ﻋﻠﻴﻪ ﺭﺯﻗﻪ
ﻓﻠﻴﻨﻔﻖ ﻣﻤﺎ ﺁﺗﺎﻩ ﺍﻟﻠﻪ… ﺍﻟﻄﻼﻕ 7 :
Ma’ana:
Mawadaci ya ciyar daga
wadatarsa, wanda kuma aka
kuntata arzikinsa (talaka), to, ya
ciyar daga abin da Allah Ya ba
shi…
A wata ayar kuma Ubangiji
subhanahu wa ta’ala ya ce:
ﺃﺳﻜﻨﻮﻫﻦ ﻣﻦ ﺣﻴﺚ ﺳﻜﻨﺘﻢ ﻣﻦ ﻭﺟﺪﻛﻢ ﻭﻟﺎ
ﺗﻀﺎﺭﻭﻫﻦ ﻟﺘﻀﻴﻘﻮﺍ ﻋﻠﻴﻬﻦ… ﺍﻟﻄﻼﻕ 6 :
Ma’ana:
Ku zaunar da su a wurin da kuke
zaune, gwargwadon samunku,
kuma kada ku cutar da su domin
ku kuntata musu…
Hadisi ya tabbata daga Abu
Huraira radhiyallahu anhu ya ce:
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama ya ce:
ﺩﻳﻨﺎﺭ ﺃﻧﻔﻘﺘﻪ ﻓﻰ ﺳﺒﻴﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺩﻳﻨﺎﺭ ﺃﻧﻔﻘﺘﻪ ﻓﻰ ﺭﻗﺒﺔ
ﻭﺩﻳﻨﺎﺭ ﺗﺼﺪﻗﺖ ﺑﻪ ﻋﻠﻰ ﻣﺴﻜﻴﻦ ﻭﺩﻳﻨﺎﺭ ﺃﻧﻔﻘﺘﻪ ﻋﻠﻰ
ﺃﻫﻠﻚ ﺃﻋﻈﻤﻬﺎ ﺃﺟﺮﺍ ﺍﻟﺬﻯ ﺃﻧﻔﻘﺘﻪ ﻋﻠﻰ ﺃﻫﻠﻚ
Ma’ana:
Dinaran da ka ciyar da shi
fisabilillah, da kuma dinaran da ka
`yanta bawa da shi, da dinaran da
ka ciyar da miskini da shi, da kuma
dinaran da ka ciyar da iyalinka, sai
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama ya ce: To, mafi girman
lada a cikin wadannan shi ne
dinaran da ka ciyar da iyalinka da
shi.
Haka kuma Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama ya ce:
ﻛﻔﻰ ﺑﺎﻟﻤﺮﺀ ﺇﺛﻤﺎ ﺃﻥ ﻳﺤﺒﺲ ﻋﻤﻦ ﻳﻤﻠﻚ ﻗﻮﺗﻪ
Ma’ana:
Ya ishi mutum laifi ya tozartar da
wanda yake ciyarwa.
Manyan malamai kamar Imam Abu
Hanifa da Imam Shafi’i da Imam
Ahmad Ibn Hanbal (Allah ya jikan
su), suna ganin yana daga cikin
kyautatawa ta zamantakewa
mutum ya raba wurin zama
tsakanin iyayensa ko danginsa da
matansa, domin zama da iyayen
miji zai iya cutar da ita matar, ya
kuma hana ta sakewa. Amma idan
ita ta zabi hakan, to, babu laifi
domin hakkinta ne. Imam Malik
(Allah ya jikansa) ya ce:
Idan matar madaukakiya ce a
wurin dukiya ko mulki, to, bai
kamata a hada su da iyaye ko
dangin miji ba, amma idan ‘yar
talaka ce, to, babu laifi, sai dai idan
za ta cutu.
Idan kuma mutum yana da mace
sama da daya, to, babu laifi ya
hada su a gida daya, kowacce da
dakinta kamar yadda Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama ya
zauna da matansa a gida daya,
kowacce kuma ya ware mata
dakinta daban. Amma idan mutum
ya ware wa kowacce gidanta bisa
zabin kansa, ko domin gudun fitina,
to, wannan babu laifi.
A nan muke yi wa ‘yan uwa
musulmi nasiha musamman
wadanda Allah ya ba su wadata,
ya kamata su raba wurin zaman
matansu da na iyayensu ko kuma
danginsu, saboda gudun fitina da
rashin kyakkyawar fahimtar da take
faruwa tsakaninsu musamman a
irin zamantakewarmu ta kasar
Hausa. Domin mafi yawan
matsaloli da mace–macen aure
sukan samo asali ne daga irin
zaman da ake yi tsakanin uwar miji
ko danginsa.
Sannan idan mutum ya raba
iyalinsa da iyayensa, wajibi ne ya
kula da hakkin mahaifansa wurin
ciyarwa da tufatarwa da
makamantansu. Domin bai kamata
a sami bambancin abinci ko na
sutura tsakanin matarsa da
mahaifansa ba, ko kuma ya fi mika
wuya ga matarsa don wulakanta
mahaifansa.
Su kuma iyaye mata su ji tsoron
Allah, su daina sa ido a kan abin
da dansu yake yi wa matansa,
domin su ma lokacin da suka yi
nasu auren, babu wanda ya sa
masu ido ko ya tsangwame su.
Haka nan ita matar, in dai ta gari
ce, bai kamata a same ta tana
wulakanta uwar mijinta ko zagin ta
ba, domin uwar mijinta, tamkar
uwa ce a wurinta.
Haka kuma hadisi ya tabbata daga
Mu’awiyyatul Kushairi radhiyallahu
ya ce:
ﻗﻠﺖ ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﺎ ﺣﻖ ﺯﻭﺟﺔ ﺃﺣﺪﻧﺎ ﻋﻠﻴﻪ ﻗﺎﻝ »
ﺃﻥ ﺗﻄﻌﻤﻬﺎ ﺇﺫﺍ ﻃﻌﻤﺖ ﻭﺗﻜﺴﻮﻫﺎ ﺇﺫﺍ ﺍﻛﺘﺴﻴﺖ – ﺃﻭ
ﺍﻛﺘﺴﺒﺖ – ﻭﻻ ﺗﻀﺮﺏ ﺍﻟﻮﺟﻪ ﻭﻻ ﺗﻘﺒﺢ ﻭﻻ ﺗﻬﺠﺮ
ﺇﻻ ﻓﻰ ﺍﻟﺒﻴﺖ ».
Ma’ana:
Na ce ya Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama, mene ne hakkin
matar daya daga cikinmu a kansa?
Sai Manzon Allah sallallahu alaihi
wa sallama ya ce: ka ciyar da ita,
idan ka ci, kuma ka tufatar da ita,
idan ka tufata, kuma kada ka doke
ta a fuska, kuma kada ka munana
mata, kuma kada ka kaurace mata
sai a cikin dakinta.
3- Kula da lafiyarta da daukar
nauyin jinyarta da maganinta.
Manyan malaman mazhabobin nan
guda hudu sun hadu akan cewa
miji shi zai dauki nauyin jinya da
maganin matarsa, dalilinsu kuwa
shi ne hadisin Jabir Ibn Abdullah
radhiyallahu anhu ya ce: Manzon
Allah sallallahu alaihi wa sallama
ya ce:
… ﻭﻟﻬﻦ ﻋﻠﻴﻜﻢ ﺭﺯﻗﻬﻦ ﻭﻛﺴﻮﺗﻬﻦ ﺑﺎﻟﻤﻌﺮﻭﻑ…
Ma’ana:
… Yana daga cikin hakkin da ya
wajaba a kanku, ku ciyar da su,
kuma ku tufatar da su bisa
kyautatawa …
Abin fahimta a nan shi ne kalmar
‘ciyarwa’ wadda ta hada da kula da
lafiya da daukar nauyin magani.
Sai dai babu laifi ga matar da take
da wadata, ta taimakawa mijinta
wurin sayen maganin da take
bukata, domin yin haka zai karfafa
soyayyarsu da zamantakewarsu.
A nan muke jan hankalin `yan’uwa,
domin sau da yawa za ka ga
mutum yana zaune da matarsa
idan tana cikin koshin lafiya kuma
tana biya masa bukatunsa, amma
da zarar rashin lafiya ya kamata
sai ya tura ta wajen iyayenta
kamar ba ta da wani nauyi a
kansa. Ina soyayya da kauna da
tausayi da rahamar da suke
tsakaninsu? kuma ina kyaututtukan
da ake bayarwa lokacin zuwa
zance domin neman samun shiga?
Don haka a ji tsoron Allah, kuma a
yi riko da karantarwar Manzon
Allah sallallahu alaihi wa sallama
bisa fahimtar magabata na kwarai
wajen kyautatawa da kulawa da
iyali a lokacin da suke halin koshin
lafiya ko kuma lokacin da ba su da
lafiya, Allah ka sa mu dace.
4- Yana daga cikin hakkin mace a
kan mijinta, ya koyar da ita addini.
Idan ta kama ma ya sanya ta a
makarantar da ake koyar da
Alkur’ani da hadisi da fikhu da
sauransu domin ta fahimci
hakikanin tauhidi da kadaita Allah,
da nisantar shirka da zuwa wurin
bokaye da masu duba da camfe-
camfe, sannan kuma ta koyi yadda
hakikanin sallah take. Idan kuma
tana da dukiya, ya nuna mata
yadda za ta fitar da hakkin Allah na
zakka, domin tsarkake dukiyarta.
Kuma ya nuna mata dokokin azumi
da abin da yake bata shi da
falalarsa. Shi ma aikin hajji, idan ta
samu dukiya, ya nuna mata yadda
ake yin sa, domin mata ba su da
jihadin da ya wuce shi. Sannan
kuma idan za ta tafi aikin hajjin ya
yi kokari ya hada ta da
muharraminta, wanda zai iya
kiyaye mutuncinta ya kuma dauki
nauyin dawainiyarta. Har ila yau,
wajibi ne miji ya koya wa matarsa
kyawawan halaye da dabi’u domin
ta kyautata mu’amalarta da
kishiyoyinta, da makwabtanta da
sauran abokan mu’amalarta.
Sannan ya nuna mata abubuwan
da Allah ba ya so, kamar kallon
fina-finai na batsa da sauraron
kade-kade da wake-wake da
sauran abubuwan da shari’a ta
hana.
5- Ya kamata miji ya tsare
mutuncin matarsa, ya kuma kare ta
daga dukkan abubuwan da za su
zubar da mutuncinta.
Leave a Reply