Mas'alolin Azumi Na Daya

Danna nan domin shiga karatu Online

Tambaya: An tambayi Sheikh ibn uthaimeen: Hukuncin wanda yake bacci baki dayan Rana a watan Ramadan, Meye hukuncin azuminsa?
Amsa: Wannan mas’alar ta kunshi yanayi biyu:
1. Ya zamto cewa mutum yana baccin ne baki dayan rana kuma baya tashi sallah akan lokacinta, toh wannan mutumi mai laifi ne, ta yadda baya tashiwa yayi ibada akan lokacinta,
2. Ya zamto yana tashiwa yayi sallah akan lokacinta, toh wannan Bashi da Laifi, sai dai yana asarar alkhairi masu yawa, domin ya dace ace mai Azumi ya zamto ya shagaltar da lokacinsa baki daya wurin Sallah da zikiri da karatun Alkur’ani da sauran ayyukan Ibada.
Tambaya: An Tambayi Sheikh ibn uthaimeen: Meye hukuncin karya Azumin Ramadan ba tare da uzuri ba?
Amsa: karya Azumin Ramadan ba tare da uzuri ba babban laifi ne, kuma wanda yayi wannan aiki ya zama fasiqi, ya wajaba akansa ya tuba sannan kuma Ramako ya kamashi. Amma in yazamto cewa ana azumin Ramadana sai mutum yaki daukan Azumi da gangan, toh wannan babban laifi ne shima, kuma Mai wannan laifi fasiqi ne dole ya tuba zuwa ga Allah, amma Ramako baya kansa abisa zance mafi inganci, domin wannan ramako bazata amfanar dashi ba, domin baza’a amsa masa ba, domin Ka’ida shine: “Duk wata ibada da take da kayyadadden lokaci, idan aka jinkirta ta daga kan lokacinta, ba tare da wani uzuri ba to ba’a karbanta”. Domin Manzon Allah(Sallallahu Alaihi wasallam) Yace: “Duk wanda yayi aiki wanda babu umarninmu aciki to an mayar masa”
Kaga wanda yaki yin azumin Ramadana alokacinta yayi awani lokaci daban wanda babu umarnin Allah ko na Manzonsa na cewa ayi wannan azumi acikinta to yayi abinda ba’a umarceshi dashi ba.
Kamar yadda bazai yiwu mutum ya fara azumi ba kafin watan Ramadan, to haka nan bazai yiwu ya jinkirta ta ba tare da wani dalili ba.


Reference: A duba littafin
الصيام مجموعة أسئلة في أحكامها(للشيخ محمد بن صالح العثيمين).

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates