Husaini Ya Aika Jekada Zuwa Iraqi
Matakin da Husaini ya dauka shi
ne ya aiki kanensa Muslim bn Aqil
a matsayin jekada don ya bincika
masa gaskiyar mutanen Kufa. Da
tafiya ta yi tafiya sai Muslim ya aiko
a fada ma Husaini tafiyar fa tana
da wahala sosai, kuma akwai
karancin ruwa a hanya. Don haka
yana rokon sa da ya bar shi ya
koma Makka. Husaini ya aika
masa cewa, ya dai yi hakuri ya ci
gaba da tafiya.
A lokacin da Muslim ya isa Kufa
yan Shi’a sun kewaye shi suka
jaddada mubaya’arsu ga Husaini
ta hannunsa. Kimanin mutane
18,000 ne suka dau alkawari ga
Allah idan Husaini ya zo wurinsu
za su kare shi. Ganin haka sai
Muslim ya tayar da manzo na
musamman don ya sanar da shi
abinda ake ciki, alabashi shi kuma
ya kama hanya ya iso. Sai dai
kamar yadda zamu gani a nan
gaba duk wannan yaudara ce
kawai yan Shi’a suke yi ba zancen
arziki ne ba.
Leave a Reply