Wannan tambayace da Musulmi yakan yi wa kansa a wasu lokuta sabida Mamaki da ganin yadda kafiran duniya da ƴan kanzaginsu Munafukai daga cikin Musulmai sukanyi Caa akan duk wani hukunci da shari’ar Muslunci yazo dashi.
Ya kamata Musulmi ya sani cewa wannan ƙiyayya ba ta yanzu bace, daɗaɗɗiya ce. Babu yadda za’a samu gaskiya da ƙarya su haɗu wuri ɗaya su zauna lafiya, sabida shi maɓarnaci baiƙi kowa a duniya ya zamto maɓarnaci irinsa ba, sabida bayaso ya halaka shi kaɗai.
Sannan wannan ƙiyayya tsaƙanin gaskiya da masu kira zuwa gareta, da ƙarya da masu ƙira zuwa gareta bazata gushe ba matuƙar muna doron ƙasa.
Wannan Sunnah ce ta Allah. Allah yace:
Hakanan ne muka sanya wa kowani Annabi Abokan gaba daga mujrimai
Al Furqan: 31
Yaushe ne Kafirai da munafukai zasu so mu, su daina yaƙarmu?
Bazasu taɓa daina wa ba har sai mun ridda daga Addinin mu, ko kuma mun kauce akan tafarkin da Annabi yazo dashi. Da zarar kaga kafirai da munafukai sun fara yaba addininka toh ka tabbata ka kauce wa hanya, ka faɗa wani tafarki ne wanda hakan ya sanya kuka zama daidai dasu. Kamar yadda Allah ya bada labari yace:
Ba zasu gushe ba suna yaƙar ku har sai sun sanya ku kunyi ridda daga addinin ku.
Suratul Baqara: 218
Wannan aya a bayyane take. Kada ka ɗauka domin wayewarka ne suke kusanto dakai suna buɗa maka suna sonka. Ka sani cewa inhar kana kan tafarkin Muslunci ɗari bisa ɗari toh bazasu taɓa sonka ba sai dai su faɗa maka kawai da baki, amma zuƙatarsu cike take da ƙiyayyarka.
toh in Musulmi ya fahimci wannan zai gane cewa wannan itace sababin wannan ƙiyayya da sukeyi wa Shari’a. Bawai dun bata dace bane, ko kuma tayi tsauri.
Kamar yadda akwai hukuncin kisa a addinin Musulunci akwai hukuncin kisa a hukunce hukuncen da ƴan adam suka shar’anta. Amma hakan tana bambanta ne daga ƙasa zuwa ƙasa.
Wasu ƙasashen suna sanya hukuncin kisa ga wanda aka kamashi da safarar muggan ƙwayoyin, wasu kuma sukan sanya hukuncin kisa ga mai fashi da makami, wasu ma sukan sanya hukuncin kisa ga duk wanda ya soki Gwamnatin kasar a bayyane.
Ashe dai hukuncin kisa akwai shi kuma ana amfani dashi acikin dokokin wasu ƙasashe. Sannan kuma ko wacce ƙasa tana da wani abinda take ga ya cancanci a sanya masa hukuncin kisa.
Toh indai haka ne meyasa in Musulmi suka ce ga nasu abubuwan da suka sanya masa hukuncin kisa wanda wannan hukunci ya samo asali ne daga Allah maɗaukakin sarki sai ayi ta cece kuce. Wannan wani irin rashin adalci ne?
Misali hukuncin kisa kan wanda ya zagi Annabi: sukan ce ai mutum yana da dama ya faɗi albarkacin bakinsa, daga cikinsa kuma har da zagin Annabi da koma waye. Toh anan sai muce shima haka nan mai safarar miyagun ƙwayoyi da duk wasu laifuka makamantar haka wanda wasu ƙasashe suka sanya masa hukuncin kisa akai yana da Ƴanci yayi abinda yaga dama meyasa za’a takura masa a kuma salwantar da rayuwar sa kan abinda shi yakeso ya aikata, hakan akwai nau’i na takurawa. Idan har haka kuke so to dole sai a share duk wata doka abar kowa ya zauna yadda yaga dama, ya kashe wadda yakeso, ya ɗebi dukiyar wanda yakeso yayi duk abinda yaga dama sabida ƴanci da yake dashi na yayi duk abinda yakeso. Toh anan kaga duniya ba zata ta zauna lafiya ba.
Ashe dai ƴanci yana da iyaka. Ko wata Al’umma kuma tana da irin iyakar da ta shata. Mu Musulmi muma muna da dama mu shata namu iyakar.
Bayan Nazari abinda zai Bayyana wa koma waye shine: tsabar ƙiyayya ga Addinin Allah ne kawai ta sanya wa’innan kafirai suke ƙin Shari’ar Muslunci.
Ƙarin Misali:
- A dokokin su a wasu ƙasashe haramun ne na miji ya auri mace da bata kai shekaru 18 ba. Amma kuma basu da wata doka da zai hana zina da irin wa’innan matan.
- A dokokin su haramun ne mutum yasha Wiwi da Cocaine amma kuma giya halal ne. Duk da cewa sananne ne cewa wiwi tafi giya ƙara lafiya a jikin dan Adam.
- A dokokin su a wasu ƙasashe haramun ne na miji ya auri fiye da mace ɗaya, Amma kuma babu laifi yayi zina da kowace mace da yaga dama a waje. Kunga anan sun hanashi ƴancinsa na auran mace fiye da ɗaya sabida son zuciya da kuma ƙiyayya ga shari’ar Muslunci.
Mai duba ga irin wa’innan misalan zai fahimci cewa Bakomi bane a zuƙatan mutanen nan face son zuciya da ƙin gaskiya. Idan har doka bata dace da son zuciyarsu ba toh suna ganinta a matsayin dokace wacce bata inganta ba, amma inta dace da son zuciyarsu toh komi tsaurinta babu ruwansu.
Kai Musulmi ya dace kasan matsayinka game da wa’innan mutane. Kansan meye buƙatunsu. Wanda shine rabaka da Addinin ka ta kowani hanya.
Leave a Reply