Yana daga cikin abinda yake damun Al’ummar mu a wannan zamani Gulma, tsegumi, da kuma bibiyar laifukan juna, wanda kuma wannan ba ɗabi’ah bace mai kyau a duniyance da kuma addinance, ta yadda mutane suka koma basu bayyana aikin alkhairi da ƴan’uwansu sukeyi, amma da zarar sunga wani laifi da suka tafka sai suyi wuf su yaɗa shi kowa ya sani.
wannan abu bata tsaya akan gama garin mutane ba har kan shuwagabanni da kuma malumar Al’ummah. Wanda wa’innan sune garkuwar Al’ummah. Zaka ga mutane inda shugaba ko malami zaiyi aikin alheri dubu bazasu ce uffan ba, amma da zarar ya tafka kuskure ɗaya ka rinƙa gani suna yaɗa wa kenan a kafafe da dama, musamman wannan zamani namu da hanyoyin yaɗa labarai suka yawaita. Sai mutum yayi ta yaɗa wannan kuskure da shugaba yayi ko malami, sai kace ance masa lada zai samu ayin haka. Toh a haƙiƙah mumini baya tona asirin mumini, sannan kuma baya yaɗa sirrinsa, mumini nasiha yakeyi ya kuma rufa asiri, amma shi munafiƙi baya nasiha sai dai ya yaɗa laifukan mutane kowa ya sani. Domin shi mai wannan laifin ya tozarta.
Bukhari da Muslim sun rawaito hadisi acikin Littafinsu Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yana cewa:
المسلم أخو المسلم، لا يظلمه, ولا يسلمه, ومن كان في حاجة أخيه كان الله في حاجته، ومن فرج عن مسلم كربة فرج الله عنه بها كربة من كرب يوم القيامة، ومن ستر مسلماً، ستره الله يوم القيامة
Bukhari: 2442
Muslim: 2564
Musulmi ɗan’uwan Musulmi ne, baya zaluntar sa, baya kuma miƙa shi,(domin a cutar dashi ko a zalunce shi) wanda ya kasance wurin biyan buƙatar ɗan’uwansa(ma’ana ya rinƙa duba masu buƙata yana biya musu) toh shima Allah zai taimaka masa ya kuma biya masa buƙatunsa, wanda ya yaye wa wani musulmi wata damuwa ko baƙin ciki da take damunsa, toh shima Allah zai yaye masa damuwowi da baƙin ciki ranar tashin Alqiyaama, haka nan wanda ya rufa wa musulmi asiri toh shima Allah zai rufa masa ranar tashin Al-Qiyaama
dubi tarbiyyar da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya baiwa musulmi. Maganarmu ta shafi ƙarshen hadisin “wanda ya rufa wa Musulmi asiri Allah zai rufa masa asiri ranar tashin Al-Qiyaama”
Wannan yake nuni da cewa wanda ya tona wa musulmi asiri Allah shima zai tona masa asiri.
Ya kamata mu kula mu rinƙa yaɗa abubuwa masu alheri, mu guje yaɗa laifukan mutane domin muma muna da laifuka da in aka yaɗa su baza muji daɗi ba. Kuma yana da kyau mu rinƙa kyautata zato wa ƴan’uwanmu musulmi a koda yaushe. Duk lokacin da mukaji ance sun aikata wani abu mara kyau toh kada mu yarda har sai mun bincika, idan kuma muka bincika muka tabbatar toh ba yaɗa wa zamuyi ba, sai mu roka musu Allah gafara da shiriya.
yana daga cikin zargi da Allah yayi wa wa’inda suka amshi labarin ƙazafi da akayi wa Ummuna Aisha lokacin da akace tayi zina. Allah yake cewa:
لولا إذ سمعتموه ظن المؤمنون والمؤمنات بأنفسهم خيرا وقالوا هذا إفك مبين
Surat-Annur: Ayah 12
Allah yace: da lokacin da kukaji wannan labari na ƙarya da aka lanƙaya wa Sayyada Aisha( Radiyallahu Anha) Sai kuyi zaton alheri wa kawunanku ku muminai, kuce wannan ƙiran ƙarya ne a bayyane.
Haka ɗabi’ar mumini yake, a lokacin da yaji ance ɗan’uwansa ya aikata wani mummunan abu sai yaji a ransa cewa wannan ba gaskiya bane ko kuma in akwai wani uzuri da zai bashi sai yayi ƙoƙari ya bashi, ba kawai ya kama yaɗa labarin ba.
Ya kamata muji tsoron Allah mu rinƙa kiyaye bakunanmu, mu daina furta kalamai sai masu amfani. Domin zaka iya furta wata maganar ta zama sanadiyyar shiganka wuta, sannan kuma kana iya furta wata maganar ta zama sanadiyyar tsirarka. Kamar yadda aka rawaito daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Allah yasa mudace.
Leave a Reply