Author: Dr. Ibrahim Jalo Jalingo
Babban Malami kuma Mujaddidin Musulunci
 Sheikh Uthman Dan Fodiyo ya ce: Maulidi bidi’a
 ce abar kyama. Shehu ya rubuta cikin littafınsa
 mai suna: Ihyaa’us Sunnah Wa Iqmaadul Bid’ah
 shafi na 104 kamar haka:
ربيع الأول
 فان قلت ما حكم ما يفعل الناس في )فيشهر
 يوم المولد او اليوم السابع من المولد من اجتماع الناس للذكر
 والطعام الذي يعملونه لذلك؟ قلت: انه بدعة مكروهة أن خلا
 عن كل معصية. وقيل: أن الصواب آن عمل المولد الشريف
 النبوي من البدع الحسنة المندوبة اذا خلا عن معصية. وأما ما
 يعتاده الناس في هذا الزمان في ذلك من اختلاط الرجال
 فمعاذ ال له
 والنساء( (.أن يقول احد بجوازه
 Ma’ana: ((Idan ka ce: Mene ne hukuncin abin da
 mutane suke yi a cikin watan Rabii’ul Awwal a
 ranar maulidi, ko kuwa a ranar bakwai ga
 maulidi na taruwar jama’a saboda yin zikiri, da
 cin abincin da aka yi tanadinsa saboda hakan?
 Sai in ce: Wannan bidi’ah ce makruuhiyah in yin
 maulidin ya kubuta daga dukkan sabon Allah.
 (A wani kaulin kuma) an ce: Abin da yake daidai
 shi ne: shirya maulidin Annabi yana daga cikin
 bidi’o’i masu kyau da a ake so matukar dai ya
 kubuta daga ko wane sabon Allah. To amma
 abin da mutane suka Saba yin shi a maulidi a
 wannan zamani na cakuda tsakanin maza da
 mata A’uuzu Billaahi wani ya yadda da
 halaccinsa)
 A cikin wannan magana ta Shehu Uthman Dan
 Fodiyo za mu fahimci abubuwa muhimmai
 kamar haka:
- Fatawar Sheikh Uthman Dan Fodiyo ita ce
 Bukin Maulidi bidi’ah ce makruhiya, watau
 bidi’ah abar kyama
- Akwai wata magana da ke cewa: Bukin
 Maulidi bidi’ah ce da ake so, to amma shi
 Sheikh Uthman Dan Fodiyo yana ganin wannan
 magana mai rauni ce; wannan shi ne ma ya sa
 ya hikaito maganar da sigar tamriidhi
 Allah muke roko da ya tausaya wa al’ummarmu
 Ya cusa musu kyamatar bidi’ah duk yadda
 Shaidan zai yi kokarin kawata ta cikin
 zukatansu. Ameen.







Leave a Reply