Tambaya: Shin ya halatta mata suyi sallah wa gawa?
Amsa: Babu laifi mata suyi sallah wa gawa, ko dai suyi masa acikin gida kafin a fitar dashi waje domin yi masa Sallah, ko kuma In akwai sarari da zasu iya yin Sallar tare da maza to sai suyi, sahun su zai zama a ƙarshe kamar yadda yake a Sallar farilla.
Imamu Muslim ya ruwaito hadisi.
Aisha Allah ya ƙara mata yarda lokacin da Sa’ad ɗan Abi waqasa ya rasu matayen Annabi Sallallahu alaihi Wasallama sun umarci a kawo musu gawan shi suyi masa Sallah. Aka kawo musu shi sukayi masa.
Muslim:973
Imamun-Nawawi yace: Amma mata idan zasuyi Sallar gawa tare da maza ne, to zasuyi koyi ne da limamin maza.
Sharhul Muhazzab: 5/172
An tambayi Sheikh Bin Uthaymeen
Shin ya halatta ga mace ta tara mutanen gida mata sai suyi sallah wa mamacinsu?
sai ya amsa yace: ƙwarai babu laifi ga mace tayi sallar gawa, daidai ne tayi sallar a masallaci tare da mutane, ko kuma tayi sallar acikin gidan mamacin domin mata ba’a hanasu sallar gawa ba.
Wannan yana nuna cewa mata suna Sallah wa gawa, kodai suyi a gida kafin a fitar da gawar, ko kuma suyi tare da maza a waje, amma sahunsu ya zama yana baya. Allah yasa mudace.
Leave a Reply