Shekara kafin Hijira: 13
Shekarar Miladiyya: 610
Farkon Abinda ya fara gani na Alamun Annabta shine Mafarki na gaskiya, ya kasance duk abinda ya gani yayin bacci yana aukuwa idonsa biyu, sannan Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya kasance a lokacin yana keɓance kansa a ƙogon Hirá yana Bautar Allah, ya kasance yana wannan bautan ne akan Addinin Annabi Ibrahim Alaihissalam.
Yana cikin wannan harkar bautan sai wata rana Mala’ika Jibrilu Alaihissalam yazo masa da faɗin Allah:
“Kayi Karatu”
Suratul Alaq Ayah 1- 6
ya dawo gida ya baiwa Matarsa Sayyada Khadija Labarin Abinda ya faru, ita kuma taje ta baiwa dan’uwanta Waraqah Bin naufal labari, ya gaskata Wannan labari da ta bashi, yace ai wannan Mala’ika Jibrilu ne wanda yaje wa Annabi Musa.
daga nan sai wahayi ya yanke zuwa wani lokaci, sai Jibrilu Alaihissalam ya sake dawo wa Annabi Sallallahu alaihi Wasallama sai Annabi yaji tsoronsa, ya dawo zuwa ga iyalansa yace “Ku lulluɓeni, Ku lulluɓeni” sai Allah Maɗaukakin sarki ya sauƙar da faɗin sa:
Ya wanda ya Lulluɓa da mayafi
Suratul Mudaththir: Ayah 1-5
Wannan shine farkon Ayah da Allah ya umarci Annabi Sallallahu alaihi Wasallama da yaje ya kira Mutane.
Leave a Reply