Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai.
Haƙiƙa yanar gizo ta zo mana da cigaba, sai dai kuma kamar yadda muka sani ne mafi yawancin abubuwa zaka samu suna da fuskoki guda biyu, fuska mai kyawu da mara kyau. A matsayin mu na musulmai sai mu duba fuska mai kyau ɗin muyi amfani da ita yadda ta dace. Idan mukayi haka to Haƙiƙa zamu tsira a duniya da lahira.
A wannan rubutu yau zan yi bayani ne yadda mutum zai hana wayar sa shiga duk wani shafi da ke ɗauki da hoto ko Bidio na batsa. Domin wani lokaci mutum yakan shiga irin wa’innan shafukan ba da son ransa ba ƙwatsam sai ya samu kansa a ciki.
To insha Allah idan aka bi hanyoyin da zamuyi bayani anan to mutum zai tsare kansa daga buɗe shafi da zai kai shi ga halaka.
Allah yasa mudace.
Da farko: Na iOS (iphone)
1. Ka buɗe “settings“:
2 ka shiga “Screen Time“
3. Ka shiga “Content restrictions”
4. Ka shiga “web content”
5. Sai ka zaɓi “limit adult content”
In kabi wannan hanyoyi to duk lokacin da zaka buɗe wani shafi wanda ke ɗauke da hotunan batsa aciki to bazai buɗu ba har sai da izinin ka. Sai dai idan ka buɗe shi ne ta Application, kamar twitter to wannan yana buƙatar ka rufe duk wani abu da ke alaƙa da batsa acikin settings na shi kanshi manhajan twitter ɗin. Amma idan har a browser zaka buɗe bazai buɗe ba har sai ka amince.
Ga yadda Tsarin yake cikin hoto
1.
Bayan ka kammala bin wannan tsari idan ka buɗe shafi da ke ɗauke da hoto na batsa ga abinda zaka gani
Ma Biyu: Yadda ake ƙulle shafukan batsa a Android.
Zamu canza DNS na wayar, wannan yana buƙatar wayar ta zamto tana amfani da Android Version 9 ko sama. Sannan Settings yana bambanta daga waya zuwa waya. Amma zaka iya searching “DNS” acikin settings zai kawo maka.
1. Ka shiga “Settings”
2. Ka Shiga “Network“
3. Ka shiha “Private DNS”
4. Sai ka canza shi daga “Automatic” zuwa “Private dns provider hostname” sai ka rubuta family.cloudflare-dns.com. sai ka dannna ok.
Shikenan.
Allah ya tsaremu bakk ɗaya.
Leave a Reply