Tambaya: Shin ya halatta acire zakka a saryar dashi zuwa ga gina Masallatai da kuma Asibitoci?
Amsa: baya halatta fitar da zakka da bada shi domin gina Masallatai ko kuma Asibitoci.
domin basu daga cikin wurare takwas da Allah yace a isar da zakkah zuwa garesu.
Wanda sune:
- Talakawa
- Miskinai
- Masu aiki kan Zakkan
- Wanda ake jan ransu zuwa ga Musulunci
- Fanso fursunoni
- Masu bashi
- Don ɗaukaka kalmar Allah
- Matafiyi
Wa’innan sune Shari’a ta yadda a basu zakka, ko kuma a kashe dukiyar zakka ta hanyarsu.
Faɗin Allah
وفي سبيل الله
Don Ɗaukaka kalmar Allah malamai sun tafi kan cewa fisabilillah yana tabbatuwa ne kan mayaƙa masu fita don jihadi don ɗaukaka kalmar Allah.
Alƙurɗubi ya fada cikin tafsirinsa: Wa fisabilillah: sune mayaƙa wa’inda suka fita domin ɗaukaka kalmar Allah.
Suma za’a basu daga cikin dukiyar zakkah.
Ibn Qudama ya faɗa acikin Al-mugni
Bashi halatta bada dukiyar zakkah zuwa ga wani wuri wanda bashi daga cikin wuraren da Allah ya ambata cikin wannan ayah. Kaman gina Masallatai, ko gine gine, ko kuma samar wa mutane ruwan sha, ko kuma gyaran hanya da sauransu na ayyukan alheri wanda Allah bai ambata ba cikin wannan ayah.
Abu dawud yace: Naji Ahmad an tambayeshi sin za’a suturce mamaci da dukiyar zakkah, sai yace A’a
Sheikh Mostapha Al-Adawy: Al-fatawa Muhimmah lil ummah page: 86-87
Leave a Reply