Yana daga cikin lokuta masu falala lokaci wanda ke dab da fitowan alfijir. Wanda Allah maɗaukakin sarki ya yabi wa’inda suke neman gafarar sa a wannan lokaci.
Allah yace cikin Surat Dhariyat Aya ta 18
وبالأسحار هم يستغفرون
Allah maɗaukakin sarki bayan da ya ɗauko labarin Masu tsoron sa, acikin sifofinsu sai yace: Suna Neman gafararsa a lokacin dake kusa da fitowan alfijir shine As-sahar.
Acikin Surat Aal emran yace:
والمستغفرين بالأسحار
da kuma masu neman gafarar Allah lokaci Al-As-har. Wanda mukace shine lokaci da ke dab da fitowan alfijir.
Yana da kyau Musulmi ya lazimci wannan lokaci mai falala wurin yin Sallah da kuma neman gafarar ubangijinsa da kuma neman biyan buƙatunsa wurin Allah.
Lokaci ne dake cike da natsuwa, kuma lokaci ne da Allah ke karɓan addu’ar bayinsa.
Leave a Reply